NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Tunda suka Isa school takejin hankalinta ba’a kwance ba fargaba da tsoron abinda zai iya faruwa takeji idan har Imran yayiwa MALEEK maganar neman aurenta Wanda takega idan hakan tafaru ta take doka me qarfi tareda tsaurin ido da kawo reni.

Dafe kanta tayi tanajin kanta kaman ze buga ta fiddo wayar daga cikin jaka bayan ta fito daga first class dinta ta saka Kiran Imran din.

Cikin kulawa ya dauka da sanyayyar muryarsa me Dadi yace”

Hello baby how are you doing?

Kasa maganar tayi sbd batasan me zatace Masa ba Kai tsaye sbd Babu ta yanda zata iya fada Masa ita negestati ce ta waya.

Hello sweetie are you there??

Dawowa tayi hankalinta daga Nisan datayi a tunani ta gyara murya cikin sanyi tace”

Dama inason ganinkane we need to talk akan maganan jiya.

Gyara zama yayi daga inda yake Yana cewa”

Akwai matsala ne?

No Inason muyi maganar ne dakyau kafin akaita gaba.

Shiru yayi na tsawon mintuna kafin yace”

Ok karki damu koma menene Ina Nan zanyi handling komai yatafi smoothly
Idan kingama ki kirani I will come and pick you up.

Gyada Kai tayi kaman Yana ganinta tareda kashe wayar ta maida jaka ta miqe daga coffee shop din datake zaune takoma.

Sai yamma sosai suka fito kusan lokaci daya da Afia Dan haka Dole tare zasu tafi gidan Dan haka suka bi motar Imran sukace driver yakoma kawai.

Ganin afia na taredasu yasa tafasa Masa magana sai kawai suketa fira su dukansu musamman akan karatunsu da yanzu suka fara nisa sai ‘yar soyayyarsu dasuke jefi jefi ta hanyar kallon juna da kalmomin kulawa Wanda duk yake qara burge afia take ganin ba qaramin dacewa sukai da junaba.

Koda suka iso gida dukkaninsu tare suka fito afia na gaba suna bayanta Imran na Mata magana ahankali Yana kallonta kaman ze hadiyeta da so da kulawa.
Ita Kuma dayake duk a Sanyaye take sai yake ganin kaman yangace take Masa duk yasake sukurkurcewa Wanda ba hakan bane agurinta.

Suna shigowa palon farko itace agaba sbd afia tuni ta shige shikuma Yana gefenta cikin dibbin mamakinta da tsoronta MALEEK suka gani zaune a palon abinda bayayi hannunsa riqeda waya yanayi cikin turanci da yarensa na Amharic Wanda yasa su duka fahimtar da gida yake waya dama mahaifiyarsa sbd Jin yafada sunanta cikin yare.

Dukkaninsu sunsan ko zasu rube agurin bazai dago ya kallesuba musamman ma ita da tana shigowa fararen idanuwansa masu girma acikin nata suka fara sauka tayi saurin sauke Kai zuciyarta na harbawa
Bata tsaya wata wataba ta wuce ciki sum sum tabar Imran a gurin Wanda shikuma ya gyara zaman jiran MALEEK sbd gabatarda kansa amatsayin me neman auren NURU da neman izinin turowa a nema Masa aurenta.

Zaman jiran MALEEK ya dasa tsawon lokaci me tsayi Wanda harya fara sarewa sbd ganin kaman lokacin basa ne MALEEK din bayada Amma bazai sareba haka yayita jira har maleek din yagama.

Barka da dare MALEEK.

Kallo daya MALEEK yayi Masa ya maida kansa kan wayarsa dake sake daukan ringing ya gyada Masa Kai alamar amsawa.

Gyara zama da gyaran murya duk yayi lokaci daya Imran din Yana saka nutsuwa a muryarsa yace”

MALEEK Ina neman izini ne na shigowa neman auren NURU idan an…

Dakatawa yayi daga zancen Yana gyara zamansa sbd ganin kaman MALEEK din baiji abinda yafara fada ba.
Sake bude Baki yayi zaiyi magana MALEEK ya dago ya kallesa da kyau a karon farko da yayi Masa kallon tsaf
Ya bude bakinsa cikin dakakkiyar muryarsa me izza da kamewa yace”

Nayi waya da santiano albeiriteo gobe zasu sauka France jibi zamuyi board meeting na signing contract dinsu
Get yourself ready Kaine zaka kula da contract din har gamawansa.

Yana fadar hakan ya miqe yabar palon Imran yabisa da kallo da idanuwansa dasukai kaman zasu ciko da hawaye,
Shin MALEEK be jisa bane kokuwa zancen ne bai fahimta ba?
Shafa Dan zufan tashin hankalin da fargaban daya tsatsafo Masa yayi duk sanyin AC daya gama gauraya babban Palon Yana girgiza Kai cikin cire negative thoughts yace”

Baiji Mena fadaba gobe zanzo after breakfast nayi Masa bayani daidai.

Miqewa yayi ya fice Yana maida hankalinsa Kuma gurin contract din santiano albeiriteo da MALEEK din ya basa shugabancin handling Wanda bazai taba samun lokacin kansaba tsawon lokaci sbd contact din nada tarin ayyukanda bazasu barka ko lokacin samun nutsuwan bacci me Dadi kayi.,
Tabbas zaizo gobe yakai qarshen maganarsa da NURU agurin maleek kafin aikin yasa yarasa lokaci duk da hakan zai Kira dad dinsa akan maganar.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR????????????

Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899
[9/22, 8:52 PM]: Mamuhgee 17

Turare by awwaba
*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kinaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* tazomaku *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what’s app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram *@turare_by_awwaba mungode*


Washe gari tunda safe yasake dawowa gidan Dan ganawa da maleek Amma sbd rashin sa’a Koda yazo maleek din yafita haka ya juya jiki amace yakoma gida da niyar ya dawo anjima Dan Dole Dole tsakanin yau zuwa gobene damarsa ta qarshe ta ganawa da maleek sbd jibi Ana fara aikin Santiago Babu ranarda zai samu kansa harya samu damar magana dashi.

Ta bangaren NURU itama gabaki daya ta rasa sukuni da walwalarta akan zancen Dan ko abincin kirki tadaina ci kullum saidai tea sbd fargaba da tsoron abinda zai iya kaiwa ya komo
Duk yanda Afia tayi tayi da ita akan abinda yake faruwa takasa Mata bayani dataga kaman ran afian ya baci ne saita fada Mata da Imran nason turowane ita Kuma tana tsoron karatuntane kawai da haka afia ta zaunar da ita tabata wani qwarin gwiwan barin Imran din yayi zancen tahakane zataji idan abin me yiyuwa ne.
Hakan yasa tadan rage damuwar abin cikin ranta tafara jiran tsammani.

IMRAN kuwa Kai yayi mugun daukan zafi sbd duk wata hanyar dazai gana da maleek ta toshe har abin yafara bashi tsoro sai kawai ya yanke shawaran fadawa mahaifinsa Dan shi dakansa ya nema MALEEK din.

Zaune suke a dining suna dinner Kiran FORMER M.AMB JALALUDDEEN yashigo wayarsa yayiwa wayar kallo daya yaci gaba dacin abincinsa a natse harsaida yagama zuwa lokacin yayi Masa Kira kusan hudu sai Ana biyar din ya daga cikin kamewa da ikon sarauta dake yawo cikin jikinsa ya amsa sallamar M JALALUDDEEN suka gaisa a mutunce gaisuwa irinta dattijai manyan mutane kafin M JALALUDDEEN yafara da cewa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button