NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

MALEEK nayi kirane akan maganar aure da Imran yakeson yarinyar gurinka wadda yace sunriga sunfahimci juna sosai da ita to…..
Wata nutsatsiyar gyaran murya MALEEK yayi a natse wadda duk wanda yasan mulki da sarauta yasan dakatarwane ga zancen da ake Dan haka M JALALUDDEEN ya dakatar da abinda yake fada
Kai tsaye MALEEK cikin kamewar muryarsa me nuna isarsa yace”

Wannan maganar ba’ayin irinsa a waya.

Hakane tabbas Bata waya bace MALEEK to kabada lokacinda zamuzo sai ayi maganar akai qarshe Inshallah.

Kallon agogo yayi alamar zancen na shiga lokacinsa Dan haka Kai tsaye yace inada tafiya gizah agabana banida lokacin bayarwa idan nasamu time zangani Inshallah.

Daga haka sukai sallama Yana aje wayar AFIA dataji ya ambaci tafiya gizah hankalinta yayi mummunan tashi ta kallesa cikin son tabbatarwa tace”

Dad zakaje delah gizah??

Yana miqewa yace”

Eh Anneti tasamu attack na zuciya yau da safe.

Yana fadar hakan ya wuce gabaki daya.

Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na bugawa tana nanata zancen tafiyar.

Kasa yadda da tafiyar dad dinta zuciyarta tayi dari bisa dari sbd zuwansa zai iya kawo komai na lalacewan faranta da adduar datai shekaru tanayi na ganin dawowar iyayenta tare,
Shin Tata dad zaije delah gizah yanzu bayan zuwansa batareda matarsaba zai bayyanawa duniya cewan sun rabu Wanda hakan daidai yakeda rasa qimarsa da darajarsa hakama Kuma hakan zai jawo kokuma bada damar shigowar wata cikin rayuwar mahaifinsu ko Mata ko negestati.

Dafe kanta dake neman tarwatsewa sbd tsananin tarin damuwa data sawa kanta akan wani irin zazzafan kishi datake jiwa mahaifiyarta Dan haka bazata iya Bari dad yayi tafiyar Nan gizah ba sbd sanin tsananin qarfin iko da dokoki tareda al’adun mulkin irin na delah gizah.

NURU dake cikin Tata damuwar me nauyi tana zaune gefen AFIA din taji yanda takeda sauke ajiyar zuciya alaman Bata cikin kwanciyar hankali ko daya ta bude Baki ahankali cikin kulawa tace”

AFIA kinada damuwan wani abune?kimata sauke ajiyan zuciya.

Kasa waiwayowa tayi takalli NURUn sbd idanuwanta dasukai zuru zuru sbd masifar data sakawa ranta ta kishin mahaifinta ga wata mace
Batareda ta juyoba tace”

Bakomai kawai kaina na ciwo ne shima inaga sbd rashin bacci ne da bansamu nayiba jiyan.

Kafin NURU tayi magana ta miqe ta nufi toilet tashige ta rufo qofa.
Hawaye takeson Yi Amma ta daure tana kallon fuskarta cikin mirror ta rintse ido tana Jin shin mum dinta ta cancanci wannan fadan datake tare Mata kuwa?
Shin idan ta dage ta Hana dad dinta rayuwa da wata mace akan Taya mum dinta kishi tayi adalci a tsakaninsu kuwa bayan mum din itace ta lalata komai tayi watsi dasu ta tafi neman duniya wadda idan ba Allah yasoba har abada bazata samu duniya irinta dad dinsu ba.

Share hawayenta tayi tareda wanke fuskarta ta dauro alwalar azahar datai ta fito tana qoqarin sakewa Dan kawarda tambayoyin NURU akanta.

NURU dake binta da ido ganin babu damuwar komai a kan fuskan AFIA din sai tabar tamabayarta tana sauke numfashi Dan harta fara shiga tunanin kodai maganartane da Imran tazama matsala tunda tasanma kila zuwa yanzu yagama fadawa MALEEK komai.

Farhat ce tashigo daukeda littafi a hannunta tayo gurin NURU ta zauna kan cinyarta tana cewa”

Lewa nakasa gama wannan dubamin kigani.

Sallah Afia ta tayar tana dauke tunaninta daga kansu sbd Sam Babu Wanda zai gane abinda takeji.

Tana idar da sallar tadawo cikinsu suka cigaba da abinda sukeyi da ita Dan tasamu ta fitarda tunani da damuwardake azalzalar ranta.

Har dare tana sintirin yawo tsakanin Palo da ‘dakinsu akai akai sbd tanason ganin dad dinta akan ko tafiyarsa delah gizah na Nan.

Har suka kwanta Bata samu ganin dad dinba sbd bai dawoba koya dawo ya wuce sama ya shige Bata saniba gashi tana Kiran Mr Omar Amma wayan Bata shiga haka ta hakura ta kwanta badan taso ba.

Washe gari da safe daga NURU har Farhat sun wuce makaranta ita kadaice Bata tafiba sbd ta sakawa ranta zata zauna harsai tasamu yin magana da dad dinta.

Guraren 11 na safe kuwa saigashi ya sauko qamshinsa na gauraya palon ahankali ahankali sai kyakkyawar fuskarsa dake kame kamar koyaushe
Tai Masa kallon qaunarsa amatsayinsa na mahaifinta datake tsananin kauna da alfahari dashi ta miqe tsaye tana aje laptop din dake kan cinyarta tana amfani da ita ta saki wani siririn murmushi tana qarasawa gurinsa tace”

Good morning dad,barka da fitowa.

Kallon kyakkyawar fuskarta dake yanayi da tasa yayi Yana alfahari da ita sbd juriyarta da iliminta tareda hakurinta ya bude Baki da muryarsa me amon iko yace”

Morning li’iliti(princess)

Murmushi tasake saki tana kallon dining din dayake qoqarin zama tace”

Dad can I join you?

Batareda ya dagoba yace”

Sure princess.

Janyo kujeran dining din tayi ta zauna tana cewa” thank you abal.

Tsit gurin ya dauka suna cin abinci Babu me mgnar sai ita dake cin abincin ahankali sbd son fara kawo zancen tagaji da wasi wasin yin zancen ko kartayi kawai saita kasa dannewan ta aje spoon din hannunta a natse ta kallesa da taushin murya tace”

Dad Yaya jikin Anneti(sarauniyar mahaifiya/mahaifiyarsa)
Zaka tafi tafi gizah kenan dad?

Dan kallonta yayi tareda sassauta fuskarsa ya gyada Mata Kai.

Sake gyara zama tayi cikin tausasa harshenta da bayyanarda damuwar data Dade da dannewa cikin ranta da biyayyarta ga dad din nata tace”

Dad maganarku da mum zai fito fili idan kaje….shiru ta Dan Yi tana kallon kamewar fuskarsa ta daure taci gaba da cewa”
Idan zancen ya bayyana cewan mum ta tafiyarta tabar…… kallo daya yayi Mata da fararen idanuwansa takasa qarasa sauran zancen ta marairaice fuska tace”

Dad please ko zaka duba kagani kodan sunan mum da naka dazai iya baci.

Tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda Miqewa tsaye ya kalleta yace”

Take care princess”ya wuce.

Kasa motsawa tayi kanta na toshewa sbd hakan na nufi zancenta be karbu ba agurin dad dinta sbd hakan da yayi shine rashin amintarsa ga zance idan ankawo Masa.
Miqewa itama tayi tabar gurin Takoma daki ta zauna ta jawo waya ta Nemo numbern mum dinta tafara tunanin takira ko karta Kira,
Fasa Kira tayi tai wurgi da wayar tareda Miqewa tsaye ta sauya Kaya ta fito tashiga mota ta fice daga gidan Dan zuwa dauko NURU datasan yanzu ta Isa gamawa tunda ita yau Bata samu zuwaba.

Tunda suka dawo taketa qoqarin cire damuwarta sbd kada NURU tagane saidai NURUn tana lure da ita saidai batason takura Mata da tambaya sbd batasaniba ko matsalar ta sirrice.

Kwana sukayi ahaka suka Kuma yini ahakan har akai kwana biyu
cikin kwana biyun duk ta Hana kanta sukuni da tunanin al’amarin Wanda take ganin rushewa familynta zaiyi idan wata tashigo cikinsu amatsayin matar dad dinsu ko negestati
Itadaima tafi son iyayenta su shirya koma menene hakan yafi shigowar wata cikinsu.

Ganin dai dagaske AFIA na cikin damuwa me qarfi boye kawai take yasa NURU kallonta bayan sun kwanta tace”

Afia koma menene abindake damunki please ki rage idan bazaki iya ciresaba ko hakura dashiba sbd wannan damuwan naki bamajin dadin ganinki ahaka ko farhat dake qaraman yarinya tafara cewa menene akaiwa AFIA.
Please AFIA kicire koma menene kibarwa Allah a rayuwa dama akwai hakan duk da nasan ke koma menene damuwan ba wani babba bane sbd Babu wani abu najin dadin duniya da Kika rasa Dan Allah ki cire damuwan please baby.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button