NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Murmushin takaici na manya Anneti ta sake tana kallon zallar kuruciyar afia da yarintarta tace”

Idan har hakane kuna buqatar uwar dazata kula daku da mahaifinku sbd….

Cikin tsananin tashin hankali da firgici afia ta miqe tsaye jikinta har ‘yar rawa yakeyi ta zube gaban Anneti cikin rawar murya da Bata girmanta na uwar MALEEK tace”

Anneti Ina roqanki da kadaki kawo Mana kowa bama buqatar wata uwa sbd munada me kula damu wadda take tamkar uwa.

Kallon tsaf Anneti ta Mata saidai tasan zallar kuruciya kecin afia Amma tace”

Wacece ita?

NURU tafada Kai tsaye.

NURU ba mata bace Matar uba ake magana wadda zata zauna daku har abada.

Rintse ido tayi sbd fadar abinda zata cutatar da NURU saidai Dole zatai hakan Dan kawai abar zancen su samu su taciyarsu batareda wani maganar aure aure ba wa dad dinsu.

Bude idanuwanta dasukai jajir tayi ta sauke Kai muryarta na rawa tace”

NURU da dad zasuyi aure idan munkoma…….

Wani razanannan kallo Anneti tai Mata cikin tsananin mamakin mahaikaciyar kuruciya irin tata,
Wace irin zuciyane da afia dazata yiwa mahaifinta qarya Dan Kare mahaifiyarta?.
Ji tayi zuciyarta ta sosu da abinda afian tayi saidai ta danne bacin ranta sbd gudun shedan yashigo cikin lamarin sbd afia ta dauko wata mummunar sabia me qarfi qararda zance irin wanan akan MALEEK guda idan har Bata dauka matsayinsa na mahaifi agaretaba.
Tabbas yau zata nunawa afia yaro man kaza ne,
Ta dauko magana me girma Dan Kare darajar wadda batasan daraja ba Dan haka yau zatasan ba’a Wasa da magana irin wannan.

Kitashi kije zancenki ya karbu.

Ajiyar zuciya boyayya afia ta sauke duk ganin takashe maganar qara auren mahaifinta duk da zuciyarta bata daina bugawaba kamar zata faso ta miqe ta fice tana istigfarin na neman yafiyar ubangiji.

Bayan fitarta waya Anneti ta daga ta Danna Kiran jekadi Kai tsaye cikeda bada umarnin me qarfi tace”

A isarwa kaleeb saqo daga Anneti cewan muna roqon alfarmar auren NURU daga negestati zuwa Mata ga MALEEK na Delah gizah UBAYD MALEEK.

Da qarfi jekadi ta zube qasa tana yiwa Anneti wani irin kirarin tsananin farin ciki da girmamawa.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR????????????

Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE

DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

08085405215

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

0903 234 5899
[9/22, 8:52 PM] +234 703 598 9527: Mamuhgee 20

Assalamu alaikum, ina masu son su iya baking da decoration na birthday cake wanda idan aka kalla sai an kara kalla????

toh ga dama ta samu er uwa kiyi maza kiyi rigista, sannan zaki koyi ydda ake hada whip cream din da yke daukar awanni ba tare da ya narke ba????????

zaki koyi ydda akeyin vanilla cup cake mai dadin gaske???? er uwa ba’a iya nan muka tsaya ba zamu koya miki ydda akeyin chocolate bar cookie domin farantawa mai gida da baki????

kuma duk akan kudi naira 3500 kacal????????
Online class neh full vedios kamar a gabanku akeyi, tare da note da voice note ydda zaku fahimci komai cikin sauki????

kada kubari wannan dama ta wuceku????
Domin neman karin bayani ki kira: 07089621678
I.G handle: Umsad cakes nd more????


Tana aje wayar miqewa tayi Takoma dakinta tareda dafe kanta da tuni yadauki wani irin ciwo sbd tarin mamakinda afia ta Bata Wanda take sake Dora hakan akan rashin uwane tareda ita tarbiyarta tafara yin qaranci tana sauyawa Dan kuwa ita din Bata saniba Amma abinda tayi laifine me girma da Muni yiwa mahaifinta qarya irin wannan da zata iya zubda mutuncinsa da awani gurin ta fada hakan Dan hakanma ta yanke shawaran Babu Wanda zaisan abinda afia din tayi zata bar zancen akan MALEEK aure kawai zai qara basai kowa yasanda rabuwarsa da matarsaba bare qaryar da afian ta shata Dan Kare mahaifiyarta.

Afia kuwa tana Isa sashensu a palo ta tadda NURU da farhat na zaune Kamar ko yaushe farhat na jikin NURUn suna kallon cartoon din SpongeBob ta tsaya cak tana kallonsu hawaye nason ciko idanuwanta Amma ta danne sbd tanajin zuciyarta na karyewa na abinda tayi din sbd ta Kara NURU Dan biyan buqatarta Wanda idan daga baya bayan sun koma akaji auren NURU da Imran za’a iya daukan hakan amatsayin cin amanar MALEEK datayi tunda yanzu Anneti taji cewar MALEEK zata aura..

Cikin yanayi na sanyi NURU ta dago Jin mutum a tsaye akansu ta kalleta da idanuwanta dasukai laushi sbd ciwon Kai datake ji kadan kadan ta bude baki ahankali tace da sanyin murya tace”

Afia lafiyanki k…..Bata qarasa maganar taba afian ta qaraso hawayen cikin idanuwanta na gangaro ta rungume NURUn tana rintse ido batareda tace komaiba.

Shiru NURUn tayi itama dukkanin jikinta na sake yin sanyi Jin saukan hawayen afia akan bayanta dake bayyane ta cikin doguwar riga Mara hannu.

Sun Jima ahaka kafin NURUn ta dago afia tana kallon idanuwanta dasukai jajir ta saki wani sanyayyan numfashi tace”

Menene yafaru??

Kasa kallonta afia tayi ta juyar da Kai gefe tana hawayen cikin idon suka sake gangarowa kafin ta dago ta zubawa NURU idanuwanta cikin sanyin murya da nadama tace”

NURU idan Baki saniba ayau inason kisani ke din wata babbar bangarene na rayuwata nida farhat,
Ina Jin araina tamkar yanda nakejin farhat sbd na dade da Baki matsayi na ‘yar uwar uwa daya uba daya,
NURU wlh kisani duk duniya banajin zanyi Abu Dan kawo cutatarwa gareki Dan haka nake roqonki dakimun uzuri karki zargeni da komai idan har kikaji wata magana ta bullo Miki daga Anneti duk da nasan sirrine da bazata futarba ita kanta saidai koma yayane Ina roqon alfarmarki da kadakice komai duk tsanani kada kifada komai duk abinda akace kice eh sbd hakan shine zai bani lokacin kawo gyara tsakanin dad da mum Dina Wanda kinfi kowa sanin wannan shine burina a duniya and you promise to support me akan hakan right??

Tsit NURU tayi tana kallon afia din kaman wata sokuwa sbd ita anan Bata gane komaiba sbd zancen duk a baibai yake bayan hakan ita menene nata wane matsayi take dashi da afia zatace tashigo cikin zancen komai akace tace eh,to menene zata cewa eh din??

NURU Zaki taimakemu mu dawo da mahaifiyarmu nida farhat??

Cikin tsoro da mamakin shiga huruminda ba nataba ta kalli afian da idanuwanta sukai jajir ta gyada Kai ahankali batareda ta iya bude Baki tayi maganaba sbd Jin abin take yayi Mata nauyi kaman bazata iyaba sbd Jin kamar ba zancenda zata shiga bane.

Zamewa tayi gefen NURUn data shiga tunani haka kawai ta kwanta tareda Dora kanta kan jikin farhat dake jikin NURUn itakuma da hakan duk su duka biyun suka shiga tunani.


Tsaf kaleeb yaga sauraron saqo me girma da jekadi tazo dashi idanuwansa nakan makekiyar TVn data kusa cike Rabin bangon palonsa zaka dauka baya sauraronta Amma tsaf yagama Jin komai ya jinjina Kai Yana sake juya zancen cikin ransa da tunaninsa.

Jekadi menene halaye munana da kyawawa na NURULHUDA??
Ya qarfin nutsuwarta da biyayyarta?
Ya qarfi da girman son duniyarta take?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button