UBAYD MALEEK COMPLETE
Kuna lafiya?
Gyada Kai tayi tana cewa”
Yes Inshallah.
Ahankali NURU ta tako ta qaraso ciki ta tsaya ta gefen NURU cikin sanyin murya batareda ta kallesa ba kanta na ‘dan qasa tace”
Barka da fitowa.
Tsit gurin yayi kafin ya dago ahankali itama ya kalleta Wanda yayi daidai da fitowar Anneti tasaki murmushin ganinsu ta nufi hanyar dining room tana cewa”
Farhat zo ahau table cin abinci Afia zokiyi serving Dina.
Dan kallon NURU afia tayi ta sauke idanuwanta akan budaddiyar gaban rigarta daya bude sosai Dan idan har ba shedan ne yake Mata gixoba tana hango saman nonuwar NURUn kadan ta juya ta wuce tana Dan waiwayowa harta shige dama farhat ita tuni tashige.
Dauke idonsa yayi daga kanta tareda Miqewa baice komaiba ya wuce ciki.
Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd idan har akwai abinda yafi takura da firgici tashiga sbd taji idanuwa akanta saidai Babu tabbacin nasane Kona afia.
Kokarin zama takeyi taji Anneti takira sunanta tafasa ta nufi hanyar dining room din a sukwane tana Dan sauke Kai tana shiga Anneti ta nuna Mata kusada ita ta qaraso ta zauna kirjinta na bugawa sosai sbd duk wannan abin wani iri takejinsa Yana Mata nauyi sbd zuwan komai lokaci daya.
Afia ce tayi serving kowa Nan suka hau cin abincin Babu me mgn musamman itadai gabaki daya bataci abinda ya wuce Loma hudu ba sbd amatuqar takure take.
Maleek ne yafara tashi ya fice kafin Anneti saisu daga baya suna fitowa tuni aka fitarda komai na tafiyarsu suka dunguma zuwa ainihin fadar NEGES inda yayiwa NURU kallon tsaf kafin ya kalli MALEEK Dan kuwa yatabbatarda NURU bazatayima sa’ar afia ba Amma maleek ya aureta.
Yanaga Dole akwai dalilin dayasa MALEEK auren wannan yarinyar wadda akace asalinta ma ‘yar bawan kaleeb ne,
Idan har da akwai dalili saiya bincika yaji Dan kuwa wannan karon bazai dagawa MALEEK qafaba Dan Bai shirya sauka mulkiba ya bawa MALEEK kujerarsa Dan haka zai binciki asalin ita yarinyar da zuriarta dole baza’a rasa abinda zaiyi amfani dashiba daga ciki ya rusa maleek gaba daya saiya mallaki kejeran da hujja.
Kyauta me girma yayiwa NURU tareda su afia kafin aka fito da NURU sai alokacin kowa yaganta ‘yan jaridu kuwa sukaita dauka wasuma a sace suke daukar hotunan hadda maleek batareda sun saniba.
Kayan aure da aka bawa NURU Dole saidai aka barsu anan a hannun jekadi data riga yanxu tadawo gizah sbd sassan NURU daza’a fitar a tsara itace zata zauna Dan duk lokacinda NURU zataxo tananan Dan haka kayan acan sassan NURUn za’a ajesu.
Har airport jekadi ta rakasu tana sake jaddadawa NURUn wasu bayanan na cewa wannan aure ba saki ba warwarewa,aurene daya qullu har abada Dan haka ta nutsu ta rungumi abinda Allah yabata ta riqe da kyau tareda kiyayewa Banda Kuma yarda da kowa sbd za’a iya biyowa ta gurinki a cutatar da maleek.
Itadai saurare take kawai Dan batamasan wane turn rayuwarta zata daukaba daga yanzu Kuma.
Harsuka shiga jirgi suka miqa tana cikin tunanin yanda zatai rayuwa agidan amatsayin matar dadynsu afia gashi haryanxu bataga wani Alama daya nuna afia bataji dadin abinba ta bangare daya ga Imran datasan yanacan Yana jiran dawowarsu batasan me zatace masaba ya fahimta.
Sai dare sosai suka sauka motocin daukarsu suna airport jiransu Mr Omar sai wani rawar jiki yakeyiwa NURU Wanda yasa MALEEK yimasa kallo daya ya nutsu ya daina aka barta cikinsu afia kamardai yanda suka Saba tun ada.
Suna isowa gida su mum Sarah suka tarbesu suna zubewa yiwa MALEEK barka da dawowa Kai tsaye ya wuce samansa bayan ya amsa musu da hannuwa.
NURU suka jiyo sunawa barka da dawowa taredasu afia wadda tayi gaba sbd sai yanxu taji tasamu nutsuwa harwani ajiyar zuciyar nutsuwa take sakewa farhat mum Sarah takama hannunta suka nufi dakinta Dan wanka da hutawa.
Koda NURU tashigo daki afia harta shiga wanka Dan haka itama a qage ta cire kayan jikinta ta dauko towel ta daura tana warware gashinta afia ta fito tana gama warwarewa ta nufi toilet din tashige ta sakarwa kanta ruwan zafi tana rufe ido itamadai kusan dawowa gidan yabata nustuwa.
Tana fitowa ta Sanya kayan bacci ta saka jallabiya akai tayi sallolinta tana gamawa ko ruwa Bata nemaba ta cire jallabiyar ta haye gado ta shige bargo sai bacci Wanda afia tuni tayi nata baccin.
Washe gari sai guraren 11 dukkaninsu suka fito kowanne a shirye Banda farhat da har ankaita school sukuma sai zuwa gobe zasu fara zuwa.
Kai tsaye dining suka nufa suka zauna breakfast afia na fadawa nuru suna buqatan zuwa shopping sbd kusan turarukansu da mayukansu dasu shower creams dinsu duk sunyi qasa gashi ita tana buqatan wasu books na karatunta data siya tun last month sun iso ankirata tazo ta karba.
Ruwa NURU Tasha ta aje cup din tana cewa”
I also need some books zanbincika idan munje.
Miqewa tayi ta nufi daki tana shiga wayarta na ringing ta qarasa ta dauka cikeda mamaki da tsoro ganin Imran ne me Kiran ta ajiye wayar tareda kifewa hankalinta na neman tashi,
Me Imran keyine dazai kirani bayan nasan yariga yasan abinda yafaru.
A musulunce a al’adance duk laifine me girma Amma duk da hakan zatai magana dashi tafada Masa Dole hakuri zasu dauka haka Allah yaso Babu aure atsakainsu.
Tana daukan wayar tana tsinkewa sai kawai ta ajiye tareda kashe wayar gaba daya ta nufi closet dinsu ta janyo dogon pencil jeans da riga doguwa har qasa saidai daga qasan a tsage take har cinyoyi Wanda yasa ake Dan ganin jeans din idan tana tafiya ta janyo veil ta daura harta dauki wayarta sai ta fasa ta ajiye ta juya ta wuce.
Afia Dama a shirye take suka fito afia da kanta zataja motar yau suna sako qafafuwansu waje NURU ta tsaya cak wani tunani Yana fado Mata na sanin yanzu fa ita Matar aurece batada ikon fita kona kanta.
Waiwayowa afia tayi ta kalleta tana cewa” lafiya Kika tsaya?
Numfashi NURU ta sauke tana basarwa kada afia tagano dalilinta saita riqe gefen cikinta tana Dan yamutsa fuska kadan tace”
Marata tana ciwo inaga period Dina zaizo kije Bari nakoma na kimtsa najira zuwansa Dan kowane lokaci zaizo.
Da wani irin kallon mamaki afia tace”
Amma ai ba lokacin period dinki bane.
Sake yamutsa fuska tayi tace”
Eh ba lokacinsa bane Amma inaga abubuwan da akaita banine a gizah dama tun can sunata sani ciwon ciki.
Kallon mamaki da tsoro afia Tai Mata takasa cewa komai sai kawai ta juya tana cewa”
Shikenan ki koma Ni zanje nadawo.
Juyawa tayi Takoma ciki tana shiga Palo tana ta sauke ajiyar zuciya ta nufi daki ta cire rigar ta sauyo da qarama Mara kauri tabar wandon ta nufi kicin direct Dan aikin abincin Rana Kota samu abinyi dazai hanata zaman tunani.
Tanayi su Fana da mum Sarah na tayata harta gama tafito ta jera a dining tana baro dining din saiga farhat andaukota daga school tun daga Palo tana shigowa tace”
Aunt NURU yau akwai drwing dazamuyi babba na Eiffel tower competition ne inason nazama 1st.
Yes yes sweetie Inshallah zamuyi shi babba me kyau Wanda zaisa ki cinye afterall who’s gonna help you drw????
Da qarfi tana tsalle tace”
Our beautiful Aunt NURU.
Hmmn that sounds like a bribe sbd bantaba Jin kince our NURU ba saidai kice your NURU to yau kenan kinyadda keda afia.
Suna qarasawa kofar shiga palon kurya farhat na cewa”
No not afia,Ina nufin me and my dad since you are his wife now.