UBAYD MALEEK COMPLETE

Tsit NURU tayi sakamakon hada ido datayi da maleek dayake saukowa tayi saurin dauke kanta tana riqo hannun farhat wadda ta kwace tayi gurinsa tana cewa”
Daddy barka da fitowa.
Kama hannunta yayi Yana nufar hanyar dining Yana cewa”
Hw is daddy’s little princess?
alhmdlh dad but today I have…….kallonta yayi cikin nustuwa yace”
Go and freshen up first kafin kizo naji menene.
Da gudu tayi ciki tabarsu tsaye sai alokacin NURU tadan gyara tsayuwa tana rage murya qasa qasa tace”
Barka da fitowa.
Kai kawai ya gyada Mata ya nufi dining Wanda yasata Dole binsa Dan serving tunda dai Babu kowa agurin.
Zama yayi taqaraso cikin Jin nauyin kayan dake jikinta musamman dayake kujeransa tana seti da inda take tahowa tamafi Jin kunyar rigar dake jikinta din sbd Ana ganin yanayin kalar bra dinta fara ta ciki sbd transparent ce Amma ba sosaiba Dan Bata tana tunanin har lokacin Yana gidaba.
Tana qarasowa tafara serving dinsa cikin nutsuwar Dolen data tattarowa kanta.
Tana gama zuzzuba Masa ta nufi kicin ta hado drink dinda tasan yanasha tareda ruwa masu sanyi Amma ba sosaiba takawo ta aje tareda zuba Masa drink din a cup ta Dan dago kadan ta kallesa zatai magana ta rude ta kasa sbd kallon dayayi Mata yasata neman rudewa hartana neman fada Masa Bata saniba Saida ya tareta da hannunsa daya Wanda ya ba tsammani ya sauka daidai kan shafaffen cikinta daga ita harshi da saida suka kalli juna ya dauke Kai Yana kamewa tareda janye hannunsa tayi saurin juyawa tabar gurin jikinta na neman sakewa sbd duk duniya Babu Wanda yataba taba mararta sai yau gashi abin kamar na tsautsayi batasan yaushe rigarta tadan dagaba Dan kuwa direct taji saukan dumin hannunsa akan skin dinta da gudu taqarasa daki ta nufi toilet da gudu sbd har wani fitsari fitsari takeji na shiga rudu.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR????????????
Alkiblah–SAFIYYAH HUGUMA
Makauniyar qaddara–BILLYN ABDULL
Dalaal–MISS XOXO
Mabudin zuciya–HAFSAT RANO
Ubayd Maleek–MAMUH GEE
DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
[9/22, 8:52 PM] +234 703 598 9527: Mamuhgee 23
Abdul-rahman (sudais) is a young boy who’s so passionate about putting the Holy Qur’an into memory. Please help this little boy grow his YouTube channel ABDUL-RAHMAAN you got nothing to lose in sha Allah thank you and Jazakumullah khair????????
Do subscribe please
Kodata fito kasa zuwa dakin farhat tayi sbd gabaki daya kafafunta sunyi sanyi toilet dinma tana fitowa ta zube kan gado a kife tana sauke ajiyar zuciya a jejjere Dan Kamar har lokacin tanajin dumi da softness na hannunsa akan mararta.
Bude kofar da akaine yasata Dan juyowa ahankali taga afia ce ta tashi zaune da sauri tana cewa”
Princess tadawo.
Dariya afia tayi tana qarasowa ta aje shopping bags din dake hannunta tace”
Harkinji sauki kenan?
Waskewa NURU tayi da cewa”
Eh” tajawo kayan tana budewa Dan mantar da kanta tunanin abinda yafaru din.
Duk abinda take buqata afian tasiyo Mata ta tashi ta tattara kayan tasa musu su a inda suke aje kowanne tayi sallah tazo ta zauna suna duba wani sabon Francie’s program na likitoci da lawyers tareda engineers a laptop.
Sai la’asar lis tayi wanka ta sauya cikin White three quarter da farar top me laushi ta fita tayi dakin farhat afia tabi bayanta da kallo sbd kusan kome NURU tasaka kyau yake Mata inama ace Imran dinta tafara aura dashine zata more rayuwa sbd yanda yake Sonta Amma dad dinta bazata taba samun so agaresaba har abada sbd mum ce kawai a zuciyarsa.
NURU na shiga dakin farhat ta taddata itama sanye da fararen qananun Kaya tana jiranta har ta fidda kayan drwing din Nan suka baje suka fara.
Sai bayan magriba suka gama
Farhat ta dauka da gudu taje nunawa dadynta ya duba Masu idan sunyi daidai Amma bayanan kusan so uku tana komawa bayanan ta karba wayar NURU ta saka numbernsa dake cikin kanta ta Kira Bai dagaba tukuna ta hakura anan dakin sukai sallarsu suka kunna cartoon suka baje abinsu adakin suna kallo Saida lokacin cin abincinsu na dare yayi suka fito zuwa dining suka zazzauna sukaci suka koshi suka shige anan dakin farhat NURU tayi barci Bata koma nasu ba Dan dama hakan takeyi wani lokacin.
Qarfe goma Sha biyu da mintuna ya nufo dakin farhat din wadda kusan kullum idan haryana gida saiyazo ya dubata da daddare sbd qarancin shekarunta musamman yau dayasan saitayi nemansa sbd zanenta yaduba Mata Dan haka ya nufa dakin Kai tsaye ya bude yashigo tareda rufe kofar har zai kunna wuta gudun kada ya tadata yasa Bai kunna dinbaya qaraso bakin gadonta tareda zaunawa bakin gadon ya Kai hannu yakunna bedside lamp kadan haske ya ‘dan bayyana yana waiwayowa yaganta itace kwance abakin gadon farhat na quryar gadon ya sauke sahirtaccen numfashi Yana kallon kayan baccin jikinsu itadai farhat komai iri daya riga da guntun wando royal blue bacci suke duk su duka hankali kwance.
Dan qara rage hasken wutar yayi sbd kaman hasken zai damesu yajanyo musu bargo ya lullubesu ko Gama janye hannunsa baiyiba NURU tasa kada ta yaye lullubin Dan dama Bata cikason rufaba cikin bacci.
Fuskarta yayiwa kallon minti biyu ya dauke Kai tareda Miqewa ya nufi hanyar ficewa harya taba kofa zai fita saiya tsaya tareda Dan rufe ido ya bude tunanin Dole wani daga cikin masu aiki zasu tadasu da asuba yasashi dawowa yasake Jan bargon ya rufa Mata saidai Yana dauke hannu takai hannu cikin baccin zata yaye yakai hannu zai danne hannuwansu suka sauka atareda nashi akan nata Wanda Kai tsaye yasata bude manyan idanuwanta dake cikeda bacci ta dagosu.
Kasa yadda tayi da abinda tagani tasan mafarkine kawai take Dan haka saita juya hannunta tasanya tafin hannunta tana sake tattaba hannunsa Dan Jin tsananin taushinsu ta lumshe ido baccinta na fizgarta har lokacin tafin hannuwansu na hade.
Dan sarquwa yayi da yawu kadan yasaki Dan qaramin tari Mara dogon sauti Wanda yasata bude idanuwanta duka da qarfi tareda zaburowa daidai motsawar farhat sai yayi saurin dafeta Takoma kwance sbd kada ta tada farhat ga farhat din da surutu zata iya jeho wani zance akan hakan.
Kallonsa takeyi face to face akaro na farko a rayuwarta zuciyarta na harbawa a tsorace yayi Mata kallo daya da idanuwansa da yau suka shiga daidai cikin nata take taji jikinta ya sake gabaki daya sai kawai ta sake a jikinsa ya hadiye wani mugun yawu a maqogaransa Wanda yasata kallon moqoshinsa sbd yanda Adams apple dinsa yayi sama yayi qasa ta maqoshin nasa.
Miqewa yayi tsaye yaraba jikinsu sbd asthma dinsa dayakejin kaman zata tashi ya juya ya fice adakin yabarta kwance Bata iya ko daga hannunta sbd mutuwar jiki saidai ido databisa dashi cikin wani irin yanayi na kunyane ko na menene ta Bata saniba illa dai Abu daya data tabbatar ayau shine kyawun da Allah yabasa Wanda ko rabinsa ‘yayansa Basu daukoba cikin yama manyanta kenan…daganan baccinta ya watse har kusan asuba Bata samu baccinba gashi gobe tanada zuwa makaranta Dole ta rintse idanuwanta Dan tayi baccin Kona Dole ne.