UBAYD MALEEK COMPLETE

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
[9/22, 8:52 PM] +234 703 598 9527: Mamuhgee 24
Saida safe dukkaninsu sukasan farhat batada lafiya Koda suka Isa dakinta tana zaune jikin dad dinsu Yana zaune bakin gadonta sanye da black jallabiya ta maza me tsananin taushi sai kyallin maiqo takeyi alamar ta masu abun duniya ce.
Itace agaba ashigowa kafin Afia Amma tana ganinsa tayi slow afia ta wuceta tana qarasa dayan gefen ta farhat din ta zauna tana cewa”
Gud morning dad,
Farhat bakida lafiya bamusaniba mum Sarah ke fada Mana yanzu da safen Nan.
Dago fuskarsa yayi dake fayau dinta sai wani daukan ido take ya kalleta da idanuwansa Wanda itama daidai shi ta sata kallo suka hada ido tayi saurin sauke idonta muryarta da wani irin salon sanyi dabata saniba tace”
Barka da safiya.
Har lokacin kallonta yakeyi
Tasake dagowa ta saci kallonsa suka sake hada ido sai kawai tunanin ganin dayayi Mata jiya da daddare kusan Babu komai a jikinta take wata matsananciyar kunya ta mamayeta batasan lokacinda ta rufe idoba ta fita da gudu Kamar karamar yarinya.
Da mamaki afia ta dago ta kalli kofar kafin ta juyo ta saci kallon dad dinta da bataga alamar ma yasan da NURU tashigo bare tace kofar yake kallo ta maida kallonta kan farhat tana cewa”
Sorry baby aunt NURU taje Sanyo kayane sbd batasan dad na Nanba ta taho da sleeping dress ajikinta shine Takoma ta sauyo nasan kin matsu tazo gurinki ko baby?
Gyada Kai farhat din tayi tana kwantawa jikin afia din tace”
Afia I saw mum yesterday a school dinmu she was there before I fainted……
Da sauri AFIA ta dago ta kalli farhat din tareda kallon dad dinsu da sauri shima saidai ko Gama juyowa batayiba ya miqe ya fice kamarma baiji me farhat taceba afia tabi bayansa da kallo kafin tadawo da kallonta kan farhat cikin mamaki tace”
Baby dagaske Kinga mum?
Gyada Kai tayi tana kallon afia din tace”
Eh naganta tazo kafin ta iso gurina I fainted daganan shikenan saidai Naga dad kawai.
Wani yawu afia ta hadiye kafin ta ta danne mamakinta da farin cikinta tana miqewa tace”
Ok baby Bari naje naturo Miki NURU tazo tayi Miki wanka da brush saita Baki abinci akwai abinda zanyi yanzu na gaggawa ok baby.
Wucewa tayi ta fice da sauri ta nufi dakinsu ta janyo doguwar riga tasanya akan kayan baccin jikinta ta dauki wayarta da sauri ta fice ta nufa library dinsu Dan Yin waya.
Doguwar kimono NURU ta doro akan kayan jikinta na bacci kafin ta wuce ta nufa kicin ta hadawa farhat Dan guntun breakfast sharp sharp ta dauko a qaramin faranti ta nufa dakin tana adduar Allah yasa ya fice.
Ganin baya dakin yasata qarasowa da wuri ta ajiye tray din tana cewa”
Sweetie kiyi hkr bamu San bakida lfy ba,jiya ma anan nayi wanka Amma banluraba sbd hankalina yatafi wani gurin dabam na……kasa qarasawa tayi tana sake tunano abinda yafarun sai kawai ta sauya zancen da sakin qaramin murmushi tana cewa”
Ok sweetie muje ayi brush kizo ga breakfast sai asha magani.
Tayar da ita tayi suka nufi toilet din suka shige.
Harsuka gama komai har wanka da Shirin farhat din kafin suka fito zuwa nasu dakin itama NURU tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga suka fito Palo ta kunna Mata cartoon takoma ciki tayi Shirin makaranta tazo ta fice har lokacin afia Bata shigowaba tanacan.
Tsaye take cikin libry din idanuwanta sunyi jajir sbd tsananin baqin cikin dake mamaye da zuciyarta ayanxun datake waya da mum dinta cikin tsananin sanyin murya da sarewa tace”
Haryanxu Babu ‘yayanki acikin ranki kenan?sbd wani burinki na duniya mum kike fadar haka? Tayaya kike tunanin dad zai iya rayuwa ahaka for how long kikeso yayita jiranki?mum please ki……
Cikin iko da muryarta me taushi ta katse afia da cewa”
Zandawo wa MALEEK Amma ba yanxuba haryanxu akwai abubuwan dake gabana,afia kinada naci akan zance daya koyaushe bayan nace Miki zandawo Amma ba yanzu ba idan akwai abinda yafi cancanta yanzu dakiyi shine ki raba maleek da yarinyar daya aura Kuma tabar gidan gabaki daya sbd matuqar tananan koya saketa bazan iya dawowaba infact inason sauyin gida tunda harta zauna a wannan gidan koba komai idan haryanzu kunason aikinta zaku iya zama da ita acan Amma dai Ni Kam a sauyamin gida musamman farhat da lalurorinta sunyi yawa yau ciwo gobe lafiya….
Cikin mamaki,takaici da baqin ciki daya Gama kashe afia tabude Baki tace”
Mum shin akan abindake gabanki kika watsar da ‘yayanki musamman Yar qanqanuwa Kamar farhat harkina cewa lalurarta yayi yawa?
Ciwone fa atareda ita Wanda Allah ne ya Dora Mata ba ita tadorawa kantaba, badan NURU ba da yanzu dukkanin mu munshiga wani hali and now kina cewa akoreta?a koreta kokuma mubita can mu zauna kenan kin yafemu?
Mum inasonku keda dad duka saidai I’m sorry to say this to you yau nafi son dad ayanzu fiyedake da duk wani tunaninki Dan kuwa koba komai shi yasan haqqinmu ‘yayansa akanshi Yana bamu Dan haka mum tunda haryanxu Bakida mijinki da yayanki aranki inaga zaifi idan na karbi hakan na runguma nakuma amince Dan kuwa na tabbatarda dana amince da hakan tuntuni da bazan cutatu hakaba,
Na lalata rayuwar mutum uku sbd hope din Zaki dawo saidai Ashe mafarkinane kawai….hawayen baqin ciki me tsanani ne suka gangaro Mata ta kashe wayar da qarfi tareda wurgi da ita sbd Jin mum din na cewa”
Afia ke yarinyace haryanxu bazaki ganeba Dan haka please don’t call again idan Baki shirya daukan abubuwan dazan fada mikiba.
Kuka me qarfi ta sake tareda daukar wayar taqara kwadawa da qasa tana qoqarin sulalewa qasa cikin kuka taji hannuwan dad dinta duka biyu ya riqota Yana kallon kyakkyawar fuskarta ya girgiza Mata Kai ahankali ya bude Baki cikin muryarsa me nutsuwa da dadin sauti yace”
AFIA MALEEK karki manta ke ‘yar maleek ce jikar kaleeb our beautiful and brave lioness and you know wat thats means right princess??
Da jajayen idanuwanta ta dago ta kallesa zatayi mgn yace”
Ya Isa haka banason Jin komai all I want from you shine ki maida hankali akan karatunki ki Gina career dinki da kanki.
Sakinta yayi tareda juyawa zai fice saikuma ya dakata batareda ya juyoba ya bude Baki wannan karon cikin cikakken iko da bada umarni cikin sautinsa me daidaita nutsuwarta yace”
Wannan shine Karo na karshe daza’a Kuma maganarta acikin gidan Nan.
Karo na karshe.
Gyada Kai tayi tana sawa ranta batada uwa araye daga yau itama sbd dukkanin inda take tunanin mum dinta yau ta kai limit Dan Bata taba daukar uwa zata iya yafe har yayanta ba datake ikirarin Bata buqatar farhat sbd tacika ciwo, wannan kalmar ta rusa duk wata sauran hope datake dashi akan mahaifiyarsu.
Fitowa tayi tana shigowa Palo ta tararda farhat zaune apalon tana kallon cartoon cikin walwala abinta tana ganin afia din tasake murmushin farin cikin ganinta tana cewa”
Afia bakije makaranta ba kina inane tun dazu?
Aunt NURU ta tafi ta dauka kintafine.
Kasa magana afia tayi tausayin qanwarta me tsanani na shigarta har batasan sanda hawaye suka ciko Mata idoba suna gangarowa ta qaraso ta zauna gefen farhat din tareda rungumeta jikinta tanajin tsananin so da kaunar yarinyar tareda tausayinta,tayaya uwa zatace Bata buqatar ‘danta sbd wani ciwo na harbawa da Allah ya sako Masa,
Ta Yaya mum dinsu zatace Bata buqatar farhat?
Kamar farhat din tasani saita lafe jikin afian batace komaiba hawayen afian Bata sauka kan jikinta sun Jima ahaka kafin Afia ta zame tareda Miqewa yayi daki ta rufe kanta tana wani irin kuka me ciwo da baqin cikin rayuwa,
Babu abinda Allah be basuba najin dadin duniya sai rashin uwa tagari da soyayyar uwa da Basu samuba kwata kwata,
Suna cikin ni’imar dukiya me yawa,
Mulki na sarauta me girma,uba nagari da soyayyarsa,ilimi na Boko Dana addini,kyawun jiki Dana fuska taredana zuciya daidai gwargwado Amma uwa Basu samu komai daga garetaba bayan dawainiyar daukan ciki da haihuwa duk cikinsu Babu Wanda yayi shekara yanashan nononta take zaresu tabarwa masu aikisu sune komai nasu tayaya zasu qarar da soyayyar uwa.