UBAYD MALEEK COMPLETE

Hannuwanta har rawa sukeyi tafara ragewa jekadi kayan jikinta tabarta daga ita sai shimi
Ta karbi towel din da mum Sarah ke miqo Mata yadau sanyi sosai sbd ruwan kankarane aka saka Masa ta ya6a Mata ajiki take sanyin yafara shigarta tafara jero ajiyar zuciya a wahalce.
Ganin hakan yasa NURU ta miqe da sauri kafafunta har rawa sukeyi ta nufi dakinsu kota kan afia dake kwance a qasa batabi ba ta zari wayarta ta fito sauri ta nufi dakin mum Sarah tana Nemo numbern Mr Omar dayake shima acikin mansion din yake Yana ganin kiranta ya tashi zaune sbd koyaushe a shirye yake kullum dare Baya wani dogon bacci sbd tsaro.
Cikin girmamawa ya dauka da cewa”
Barka da…..a yamutse ta katsesa da cewa”
Mr Omar maleek da jekadi sunci ko guba kokuma wani Abu daban kaga kawai kazo yanzu yanzu matsalan babbane, maleek… maleek..jikinsa duka yayi wani…
Ko rufe Baki batayiba taji buga kofarsa
Ta dago a tsorace ta kalli kofar palon zuciyarta na bugawa da qarfi sbd tsananin tsoro
Ta cikin wayar dake kunnenta har lokacin taji yace”
Nine abude kofar da sauri.
Da gudu ta qarasa kofar ta bude Masa dukkanin jikinta rawa yakeyi Bai dago ya kalletaba yace”
Zanduba jekadi ta jikinta zamu gano ko menene.
Da sauri tayi gaba tana cewa’
Zo zo zo kaduba suna cikin tsananin azaba,
Maleek ya….shiru tayi tana kaucewa ya qarasa gurin jekadi da sauri
Kallo daya yayi Mata yasan menene
Da sauri ya daga hannunsa daya yakai bakinta saikuma ya kasa tabbatarwa ta hakan ya dakata cikin tsananin tashin hankali yace”
Idan na tabbatar garin asirin Kona jinine Wanda zai…..
Cikin tsawar dabatasan Tai Masa ba tace”
Mekake jira ka tabbatar Mana maleek na can cikin irin halin kayi sauri kafada mana abinda za’ayi kokuma Akira Dr Damien kaduba kaga halinda suke ciki…
Sake sauke Kai yayi cikin Dan Jin nauyin zancen yace”
Bakinsu za’a laso aji idan da daci sosai.
Wani irin kallo Tai Masa itama cikin tsananin Jin zancen wani iri daga sama.
Ganin kallonda mum Sarah Tai Mata ta sauke Kai haka shima Mr Omar din yasata Shan jinin jikinta sbd hakan na nufin itace Dole zataje ta dandano musu na maleek tunda dai Babu me iya Shan na jekadi hakama maleek Dole sai ita Dan dama irin wannan masifar idan ta samu mutum Miji ko Mata ke lasa bakin idan Kuma yarone iyayensu idan tsofine yayansu.
Juyawa tayi da sauri ta fita ta nufi hanyar sama zuciyarta na bugawa a qarfafe sbd tsoro haka ta qarasa dakin har lokacin Yana kwance lullube idanuwansa arufe ganin hakan yasa ta qarasa da sauri ta haye gadon Bata tsaya wata wataba takai fuskarta dap da tasa zuciyarta na harbawa tasa hannuwanta biyu ta tallafo fuskarsa ta rufe idanuwanta ta Dora qaramin bakinta kan nashi ta zura harshenta cikin bakinsa ahankali ta laso sai alokacin ta bude fararen idanuwanta ta kallesa ga mamakinta saitaga idanuwansa a bude hancinta yake kallo.
Da sauri ta zabura tareda zare bakinta tana saukowa gadon dukkanin jikinta na rawa tayi kasa da kanta zatai mgn can qasan maqoshinsa ya bude Baki a wahalce yace”
Idan jekadi ce ko mr Omar kice abinda suke zargine Mr Omar yasan password na inda maganinsa yake
Daga haka ya maida idanuwansa ya rufe sbd azabar abinda yakeji cikin jikinsa
Da sauri ta juya daga dakin ta fice zuwa qasan har tana hada bene uku uku gurin saukowa ta iso dakin da sauri ta kalli Mr Omar muryarta na rawa tace”
Yace shine duk abinda kuke zargi din kayi sauri ka dauko antidote din yace kasan komai please please please hurry Mr Omar…
Cikin sauri sauri shima yace”
Ok ok Amma Dole saimun tabbatarda bakin nasa akwai “daci sbd ta hakan zansan idan yagamabin jininsa..
Rikicewa tayi tana rawar murya tace”
Eh”kawai sbd ita Bata wani gane daci acikin bakinsaba gabaki daya ta rude da wani irin dumi da qamshin Vedshakti lemon mouth freshner data debo abakin nasa Dan haka bazata iya tantance komaiba.
Tashi Mr Omar yayi ya fice daga dakin da sauri haryana tuntube tabarsu cirko cirko a tsaye kowa kayan cikinsa na juyawa sbd fargaba.
Jin shiru shiru yasa NURU fitowa takalli agogo lokacin har qarfe uku da arbain tayi tafito Palo yafiso goma tana komawa dakin mum Sarah Jin take Kamar tayi Ari hauka ta dauko wayarta zata Danna Masa Kira sai gashi yashigo da gudu gudu ya miqa Mata Yana cewa”
Hada da ruwan zafi kikai Masa yasha inshallah zafin zai sauka gabaki daya bayan asuba saina Kira Dr Damien.,
Idan yasha zaiyi amai sosai karki basa komai bayan wannan sai bayan 2 hours.
Karba tayi tayi kicin mum Sarah na bayanta jikinta na wata irin rawa take dafa maganin harsaida mum Sarah ta matso cikin tausayi da damuwa itama tace”
Ki nutsu Inshallah maleek da jekadi Babu abinda zaisamesu.
Gyada Kai tayi kawai tana dauko cup cikin cups din MALEEK dake gurinsu daban ta zuba Masa ko a tray Bata tsaya dorawaba ta dauka ta fice da sauri tana cewa”
Mum Sarah ki zuba kiyi gaggawar bawa jekadi.
Tana Isa dakin ta ajiye cup din saidata qara sanyin AC kafin ta qaraso gadon ta aje cup din kan bedside ta kallesa tanajin nauyin yanda zata bashi sbd tagama fahimtar Dan idanuwansa na rufe bashine ke nufin Yana bacci ba.
Kafin tayi wani yunquri taga ya motsa tareda bude idanuwansa Yana tashi zaune batareda ya kalletaba ya miqa hannu daqyar
Dasauri ta dauko cup din ta matso ta miqa Masa tareda tsayawa akansa Kamar zata fasa kuka sbd Jin yanayin take har cikin ranta.
Kurbi daya yayi ya dakata sbd abinda yakeji ta matsosa sosai cikin kulawa da damuwa tace”
Yace duka za’a shanye.
Ko kallonta Bata samu damar yayiba yasake daga cup din yasha Yana rufe ido tareda shanyewa ya miqa Mata cup din da sauri Yana saukowa gadon ya nufi toilet yafara kelaya wani irin aman azaba Wanda yasata kasa hkr tabisa ciki idanuwanta na cikowa da ruwa musamman ganin Aman hadda jini sosai aciki ta rude tana dafa bayansa da har lokacin yake bayyane ba Kaya ajikinsa Dan abin kamar daurin Rai da dai towel dinsa har lokacin be kunce ba koya kunce akwai qaramin gajeran wando ajikinsa.
Saidayayi mugun amai sosai kafin taji take zafin jikinsa ya sauka gabaki daya ta zuba Masa ruwa ya wanke fuskarsa da bakinsa ta fito tabarsa aciki ta sake gyara Masa gadon da duk suka cukuikuye sbd rudewa ta dauki cup din ta fice daga dakin tun kafin yafito sbd ta lura tun cikin toilet din yadawo MALEEK dinsa.
Gurinsu jekadi ta Isa da sauri itama cikin sa’a ta tararda ta amaye komai gabaki daya ta shigo suka kamata tareda goggge Mata jiki suka kwantar da ita take baccin wuya ya dauketa sai alokacin dukkaninsu suka saki ajiyar zuciya me qarfi abinda takeji tokare a zuciyarta ya fada Mata ta dafe goshinta tana sake sakin jerin ajiyar zuciya kafin ta dago dmta kalli mum Sarah tace”
Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?
Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace”
Bansaniba
Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin
Abu daya tace shine na jininta na quna.
Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace”
Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu
Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.
Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al’amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?
Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.