NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

AIRTEL
9MOBILE/ETISALAT
MTN
GLO

DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!

DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA

Ranonet.com.ng
GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN.

KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215

KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET.

RANO NET..!!!!


Ruwa farhat ta dauka a cup takai bakin NURUn cikin kulawa tana cewa”

Sorry Aunt.

Karban ruwan tayi takai bakinta Tasha bada yawaba ta ajiye cup din tana daukan Tissue ta goge Baki.

Kasa hakuri afia tayi sbd girman mamakinta ta kalli NURUn cikin son tabbatarwa da alamar tambayarta afili tace”

NURU menene matsalar?
Ina fatan dai ba maganata bane?

Kallonta NURU tayi tana ajiye Tissue din hannunta ta miqe tsaye idanuwanta kan afian cikin nutsuwarta tace”

Matsalar shine sarqewa nayi inacin abinci kila yawucin ba daidaiba.
Maganarki Kuma afia gabaki daya hankalina bayakai sbd ba hurumina bane Banda ikon saka kaina acikin maganarki da dad dinki.

Juyawa tayi tabar dining din ta nufi daki tashige tana Dan bubbuga kirjinta Dan har lokacin zafi yake Mata na sarkewarne koma na wani abin ne dabam batasaijin dadinsa.

Afia bayan tafiyan NURU sai alokacin yanda dad ya wuce Bai nuna yaji abin data fadaba kila baiji din bane Amma Kuma tanada shakka akan hakan Dan kuwa idan har yajita shareta yayi to tabbas zancen bamai karbuwa bane agaresa kenan sbd duk abinda yayiwa hakan Yana nufin Kar akuma kawo Masa maganar.

Jin tayi fargaba tashigeta sbd Koba komai yayi Mata gargadin sake tada maganar mum dinta cikin gidan Dan haka itadai bazata iya wannan tashin hankalinba kome mum zatayi bazata sake yiwa dad maganar ba.
Miqewa tayi tabar dining din ta nufi dakinsu Dan Kiran mum din saigashi tana shiga ta tadda NURUn kwance kan gado idanuwanta a lumshe sai takasa Kiran mum din tabari saita samu lokacinda Babu kowa akusa.

Qarasa shigowa tayi ta zauna kan sofa tana sake kallon NURU datayi shiru har lokacin idanuwanta a rufe ta nemi guri ta zauna tana tsirarwa kanta wani aikin da wayarta ranta dun a jagule.

NURU najinta Amma Bata bude idanuwanta ba saima numfashi data sauke tasake saukewa ahankali tana son bacci ya dauketa ko zata samu sararin Shan iska acikin kanta itama.

Da daddare bayan sungama cin abinci batareda MALEEK ba sbd har lokacin Bai dawoba kila basudai saniba suka koma daki afia tafara wanka tafito kafin ita dai Saida tayi sallar isha kafin tayi wankan tana fitowa ta Sanya riga da wando na bacci ta shafa body mist kawai ta fice zuwa dakin afia tana sake daurin gashinta dan Tasha iska gurin bacci.

Tana shiga ta taimakawa farhat tayi Shirin bacci suka kwanta bayan ta rage musu hasken wuta suna game a iPad sun Dade sunayi kafin bacci ya daukesu su duka.

Qarfe daya da mintuna goma Sha uku ya Murda kofar dakin ahankali cikin nutsuwa yashigo Dan duba farhat din sbd tafiya zaiyi gobe Kuma itace ba lafiyayya ba shiyasa yafi bada kulawa akanta.

Tunda ya bude yashigo yasan itama tana dakin sbd yaji qamshin night alien,acqua di Parma
Qarasowa yayi gadon ya tsaya akansu tareda zaunawa ahankali bakin gadon Yana kallon fuskarta kasancewar itace Baki farhat na kurya.

iPad din hannunta yazame ahankali tareda ajiyewa gefe ya janyo bargo ya gyara musu lullubinsu har zuwa kurji.

Fuskarta data juyo gefensa ya kalla zuwa wuyanta dake bayyane ya feso Masa kamshinta direct cikin hancinsa sai dumin numfashinta dake sauka ai tsaye kan hannunsa ya rintse ido ya bude ahankali sukai ido biyu da ita qamshinsa daya cika hancinta ya farkar da ita saidai Bata motsaba idanuwan kawai ta zuba Masa.

Kallonta yake ta lumshe ido tasake budewa cikin yanayi na daukan hankali sbd bacci baccin dabai saketaba duka.

Hakan datayi yasashi hadiye wani Abu dayasa maqoshinsa yin sama yadawo qasa tana gani sai hakan yasata Jin tsananin kunya baccinta na sakinta gabaki daya ta motsa ahankali zata juya ya Dora hannunsa cikin wuyanta tareda tallafo fuskarta daf da tasa tayi saurin lumshe ido daga kallonsa numfashinta na sauyawa ta matso da kirjinta ya mannu da nasa sosai take ya sake zuba Mata idanuwansa yanakai dayan hannunsa cikin rigarta ya shafi cikinta dayasata dauke wuta take tana qanqamesa tareda sake mannuwa dashi.

Bude idanuwanta tayi ahankali har lokacin fararen idanuwansa na zube akanta fuskarsu na Dab data juna sosai Dan dogayen hancinsu gugar juna sukeyi duk numfashinsa daya da qamshin spraymintt na Baki take shaqa Ahankali ta bakinsu sukazo daf da juna har lokacin cikin idonta yake kallo idanuwansa na sake rurrusa kuzarin jikinta ta sake Masa gabaki daya cikin jikinsa tana matse dashi.

Kallon bakinsa dake daf da nata tayi sbd lips din kusan suna gugar juna ta lumshe ido tana tunowa a dakin farhat ne Kuma farhat na tashin dare Shan ruwa Dan haka zata iya tashi kowane lokaci Dan haka ta dago idanuwanta ta kallesa ta motsa zata bude Baki tayi magana bakinsu ya hade saijin farhat tayi tana Kiran sunanta cikin bacci.

Wani irin mummunan sanyi jikinta yayi takasa dagowa ta kallesa hakama takasa fitowa daga jikinsa tanaji ya zameta tareda Miqewa ya fice batareda ya waiwayo ba tabi bayansa da kallo jikinta na sake mutuwa Dan bama zata iya tashiba yanzu daukowa farhat din ruwa kafafunta bazasu iya daukanta ba.

Tana kokarin tashi taji bude kofar dakin tana dagowa Yana aje Mata ruwan roba biyu agabanta ya juya ya fice mamaki na shirin shideta ta kalli ruwan da sauri tadago tasake kallon kofar daya fice mamakinta na sake ninninkuwa.
Da sauri ta dauki ruwan ta Dora kan jikinta saiga wani siririn murmushi ya sauka kan innocent face dinta tana waiwayawa ta kalli farhat da batama farka ba har lokacin wato dazun motsawane kawai tayi cikin bacci takira sunanta.

Bude ruwan tayi ta ‘dan Sha daya ta rufe ta ajiye har lokacin Dan boyayyan murmushinta Yana kan fuskarta ta zame ta kwanta tana lullubewa tareda rufe idanuwanta.

Washe gari sai 9 ta fito tana Yar miqa sbd tayi bacci me nutsuwa da qarfi ta nufi dakinsu ta shige Kai tsaye ta nufi toilet sai datayo brush tafito tazo gurin afia suna gaisawa tace”

Afia yaushe zakije siyayya akwai abubuwan danake buqata infact inason zuwa saloon yaushe zamuje?

Nima inason gyara kaina da qafafuna siyayya Kuma zanmana online shopping.

No banason online akwai abinda nakeso naje da kaina na siya dole sainaje da kaina.

Me kike buqatane?”afia ta fada tana zare dogon wandon baccinta Dan tubewa tashiga wanka.

Nighties Dina sun tsufa ina buqatan wasu and makeup stuff dai sai perfume danakeson sauya brand.

Ok Nima dai kusan duk buqatar dayace why not muje anjima.

No kikuma dai gobe ba.

Alright shikenan”afia tace tana qarasa cire kayanta ta nufi toilet tashige.

Bayan shigarta toilet din kenan wayarta tayi ringing NURU dake kusa ta dauki wayar zata daga tana dubawa taga sunan MUM baro baro akan wayar ta ajiye batareda ta daga din ba qarshema ta miqe ta fara gyara musu dakin tana kallo lailan nata Kira kusan ko bakwai kafin ta hkr zuciyarta na can na tafarfasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button