NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Neges na zuwa cikin tsananin jimami da tashin hankalin wannan mummunan al’amarin ya kalli MALEEK Yana bayyanarda damuwarsa da rashin Jin dadinsa akan al’amarin yace”

Ina me jajanta maka wannan al’amari
Saidai nayi maka alqawarin hukunta duk Wanda aka tabbatarda shine yayi kisan a tsakaninsu biyun Dan kuwa wannan al’amari babbane dazai iya tana darajarmu gabaki daya da ikonmu Dan Haka komai zai tafi abisaga adalci da doka wannan alqawarinane.

Sai alokacin maleek ya dago ya kallesa da idanuwansa dake bayyanarda zallar bacin Rai da wani irin zafi na iko da mulki dake yawo jininsa ahankali ya bude Baki cikin kamewa yace”

Godiya maleek yake Kuma Ina fatar zaka tuna wannan alqawarin naka Dan cikakkene jinin delas basa alwawarinda basa cikawa Ni nayi maka alqawarin tayaka cika wannan alqawarin za’a tafiyar da komai bisaga adalci da doka.

Jinjina Kai neges yayi Yana danne abinda yakeji gameda maleek din ya sassauta kallonsa zuwaga gawar da aka dauka za’a shigar ambulance ya waiwaya ya kalli yakoob Yana cewa”

A tabbatarda gawar kafin su tafi da ita.

Matsowa Mr Omar yayi Ya tarewa yakoob hanzari Yana sauke Kai cikin tsananin girmamawa ga neges Yana sassauta harshe da cewa”

Allah yaqarawa neges girma
Ina neman afuwar rashin barin abude gawa irin wannan agabanka sbd darajarka fifitacciyace dabazai yiyu irin wannan abudeta a gabanka sbd dukkanin suturarta a yage take Wanda ya nuna alamar Tasha dama da makashinta kafin samun nasararsa
Ni zanyi shedar tabbarda gawar aduk lokacinda buqatan hakan ta taso agurin Sharia.

Cikin jinjinawa yace”
Shikenan hakan yayi Allah ya kyauta Amma duk da hakan Ana buqatan tabbarwan.

Matsawa mr Omar yayi tareda bawa yakoob hanya ya wuce Dan ya tabbatar din saidai Yana Kai hannun zai bude jami’an tsaron dasuke jiran ambulance su tafi tare suka dakatar dashi cikin yanayi na dokar aikinsu da girmamawa ga neges shugaban yace”

Allah yaqarawa neges girma Babu Wanda zai sake taba gawar Nan ayanxu sbd Babu abinda mukai bincike akansa zamuje da gawar lab muduba komai ayi aune aune daga lokacin ne bayan angama komai zamu bayar da gawar ayi Mata janaixa daganan ne kowa zai iya tabawa Amma yanxu muna bawa neges matuqar hkr
Saidai idan hankalinka yafi kwanciya da kwakwariyar shedane zamu iya cewa tunda maleek yagani hakan zai gamsar da Kai.

Numfashi boyayye neges yasake Yana jinjina Kai tareda kallon maleek cikin yanayi na kulawa da damuwa yace”

Duk yanda za’a ayi kada abari media suji wannan mumman labarin ayi komai a sirrance tunda hukumarma a sirrance suka shigo suka fice.

Motar asibitin tafara wucewa daukeda gawar kafin akabar jamian tsaro uku da sauran securities din maleek a bakin sassan na maleek sbd shima Yana cikin wainda hukumar zata tsare sbd komai a qarqashin bangarensa yafaru Dan Haka an saka tsaro a sassansa babu inda zashi zai zauna aciki bame Shiga sai mr Omar kawai aka bawa dama shima abincin kawai zai ringa shiga dashi yafito sai zuwa headquarter aduk lokacinda aka buqaci ganinsa harsai antabbatarda cikin su biyun lailah ce ko jekadin ce tayi kisan.

Da hakan zancen yasake qamari hankalin jama’ar gizah yayi mumman tashi musamman Anneti tana tsananin buqatan ganinsa saidai ba dama Haka Takoma sashenta cikin tsananin tashin hankali da damuwa tana daga hankalinta da rokon Allah sassaucin wannan mummunan masifar har lailah take roqawa sassauci sbd ita uwace tasan wannan Abu wani babban al’amarine daga ubangiji kowa na neman doki daga garesa Dan Haka kowa zata rokar Masa.

Ta bangaren Mr Omar Yana fitowa gizah tareda maleek cikin sirrantacciyar mota sai motar jamian tsaro da securities dinsa fitowarsu gizah kenan ga tarin dibbin mamakinsu ‘yan media ne birjik suka yo kansu tareda zagaye motocinsu suna jeho tambayoyin dasuka kusan hargitsa tunaninsu su dukan Dan kuwa bayani ne akan cewa”
Shin me maleek zai iya cewa akan tsohuwar matarsa da jekadinsa dasuka taru suka kashe ‘yar uwar matarsa?????

Tsit sukayi dukkaninsu Mr Omar na dagowa ya kallesu kafin ya ‘dan waiwayo ya kalli MALEEK dake duba wayarsa hankalinsa kwance ya girgizawa Mr Omar din Kai take Mr Omar yabawa motar wuta sukai cikinsu da gudu sukaita kansu suna tsananta wutar al’amarin a social media da cewar tsohuwar matar UBAYD MALEEK M KALEEB tayi hadin gwiwa da jekadinsa gurin kashe yayar matarsa a Daren jiya.

Ganin yanda abin ke ruruwa Kamar wutar daji yasanya Mr Omar Kiran mum Sarah da gaggawa ya Bata umarnin duk wani Abu daya shafi kallon news ko wayoyin NURU da afia duk ta lalata kada tabari su samu news na abinda yake faruwa.

Ta bangaren iyayensu nu NURUn kuwa Abu Kamar hadin Baki Koda gari ya waye labarin ya baza duniya babusu Babu Wanda yasan Ina suka bace bat a dare daya ga ‘yan kawo rahoto da ‘yan jaridu daketa yawon gidansu sunason ganawa dasu akan al’amarin Amma babusu sai hakan yaqarawa tashin al’amarin girma sbd take aka fara kokarin Bata sunan MALEEK da cewar shine ya batarda iyayenta Dan boye laifin tsohuwar matarsa da jekadinsa.

Headquarter dasuka Isa wasu sabbin rubuce rubucen report aka shigar musamman akan ta Yaya ‘yan jaridu sukasan macece aka kashe Kuma Yar uwar matarsa sbd Babu Wanda yasan gawar waye dagashi sai mr Omar ko jamian tsaro Kai tsaye ya hanasu duba gawar aka barta akan se Yan asibiti sungama nasu aikin tukuna
Kuma ‘yan asibitin ma mutum biyune Kuma a asibitinda Babu Wanda yasan da ita aka aikasu to tayaya zancen yafita zuwaga ‘yan media.

Suna dawowa gida ya shige sashensa ya zauna tareda sauke ajiyar zuciya ahankali tareda rufe idanu ya bude ya kalli gefenda Mr Omar yake tsaye Kai tsaye yace”

Kayi komai kaje da kanka ka taho dasu at any cost kada wannan labarin ya samesu harsai sun iso.

Dan dagowa Mr Omar yayi ya kalli MALEEK yace”

MALEEK anan din aikin Nan barinsa nada hadari.

Kaje komai Yana yanda ake son shi.

Angama Inshallah maleek.

Ficewa yayi Kai tsaye yakira Yana booking tickets Allah ya taimakesa washe gari da asuba jirjgin zai tafi Dan Haka Kai tsaye ya wuce ba wani delay.

Sai tsakiyar dare sosai ya Isa gidan Bai samu shigaba ta waya ya sanarda mum Sarah ta sanarda NURU da afia su shirya gizah zasu.

Da mamaki suka kalli juna lokacinsa mum Sarah ta sanar dasu saqon
NURU ta kalli wayarta da jiya ta wayi gari taganta a farfashe ta waiwaya ta kalli afia da tata ma tafi ta NURUn tashi aiki cikin sanyin murya tace”

Kina tunanin lafiya komai yake?

Sauke ajiyar zuciya afia tayi tana Dan duba agogo tace”

Inshallah lafiya.”tafada hakan ne Dan bawa kanta qwarin gwiwa da bama NURUn positive answer Amma tun jiya takejin kanta cikin tsananin damuwa musamman dataga miscalls na mum dinta data kirata Bata kusa wayar na silent tunda ta karanta massage dinta taji tana kewar soyayyar uwa saidai Kuma zuciyarta na tunatarda da ita amfani mum dinta keson Yi da ita kawai tunda take nemanta.

Babu wani dogon musu sukahau shiru tsaf suka shirya hankulansu a tashe Babu me nutsuwa daurewa kawai kowannensu keyi Dan qarfafa Dan uwansa.

Sai washe gari da asubar fari jirginsu ya daga suka wuce Basu isaba sai cikin tsakar dare har lokacin ‘yan jerida na daddabe boye a wajen masarautar gizah suna jiran rahoto
Dayake Mr Omar yasani saida sukazo gate din Yan jaridar na tasowa yace driver yayi cikinsu da mota duk da hakan sama sama afia taji dayan na jeho tambayar data sakata kallon waje da sauri inda Yan jaridar ke kokarin biyo motar askarawan securities din makeken gate din shiga masarautar suka taresu da sauri suka koma maboyarsu suna jiran sa’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button