UBAYD MALEEK COMPLETE

Afia jitayi tana gigicewa da abinda kunnuwanta suka ji cewar
Tsohuwar matar maleek tayi kisa
Kenan shine dalilin daukosu da gaggawa ba shiri?
Rawa jikinta yafarayi ta dago idanuwanta nacikowa da hawayen tashin hankali ta bude Baki zatayi magana daidai tsayawan motar bakin sashensu a fixge tasamu damar fizgo maganar daqyar ta bakinta tace”
Mum tayi kisa?????
Da sauri NURU ta waiwayo ta kalleta gabanta na mummunan faduwa
Saidai ganin afian na kallon Mr Omar da idanuwanta da take sukai jajir yasa NURUn juyowa tana kallonsa da jiran amsarsa Dan kuwa take jikin NURUn yaso fin na afia daukan rawa Dan kuwa a yanda tasan lailah kila maleek ne kawai Wanda zata iya kashewa sbd kishi da baqin cikin abinda yayi Mata batasan lokacinda bakinta Yana rawaba ta furta”
Wa aka kashen???
Sauke Kai Mr Omar yayi cikin tsananin jimami da kasa fadar komai akan tambayoyinsu Wanda yasakasu tabbatarda maganar kenan Haka take abindaya faru kenan.
Take hawayen afia suka balle duk inda hankalinta yake Yana tsananin tashi
Mr Omar yayi saurin fitowa ya budewa afia kofa suka fito har NURUn tsabar rudewa ta manta da sashenta za’a qarasa da ita.
Afia tayi ciki da sauri ko gabanta Bata gani sbd tashin hankali wani takeson tambaya taji shin da gaskene kokuwa gizo maganar tayi Mata,
NURU kuwa sagewa dukkanin kafafuwanta sukai ta nufo cikin tana daga kafa daqyar farhat datai bacci saidai bayinda suke shigarda kayansu afian suka shigo da ita
Tana shigowa palon daidai lokacinda baiwar da afia ta dakawa tsawa tana cewa”
Ki fadamun abinda ke faruwa a cikin delah gizah nace..””taqarasa fada cikin tsananin karajin daya tsorata baiwar a firgice tace”
Kisa akayi a…a..sassan MALEEK.
Innalillahi’wainna ilaihirrajiun” shine abinda afia tafara maimaitawa cikin tsananin fita hayyacinta tana girgiza Kai da sauri da sauri.
NURU kuwa Jin sunan maleek a maganar yasa jiri dibarta Saida mutum biyu sukai saurin tarota dama Mr Omar yasakasu kiranta Dan qarasawa da ita Bata masaukin suka fito da ita ko ganin gabanta batayi sosai kokai dake aiki jikinta ya tsaya harta shiga mota aka ja Bata saniba,
Suna Isa bakin masaukinta mr Omar ya bude Mata kofar Motar
gabaki daya Bata lurada wani sashene aka kawota dabam ba asalin nataba Dan tafiyar kawai takeyi batasan inda take jefa qafa Haka Mr Omar ke bude Mata kofofin palukan dasuke wucewa har zuwa na karshe daya bude ya dakata ta shige ya janyo kofar ya juya ya koma Yana ficewa daga sassan gabaki daya.
Hankalinta baya jikinta saidata takunta yafara nisa cikin palon taji iskar numfashinta ya sauya da qamshin dayake shiga hancinta ta dakata ahankali tareda dagowa ta kalli inda take tana waiwayawa gefen damarta numfashinta saidaya kusa daukewa sbd bazatan yanayin datashiga ganinsa zaune kan kujera sanyeda jallabiya brown fuskarsa na fidda wani irin zatin kwarjini Yana kallonta da fararen idanuwansa dake zube tas akanta…ta rufe ido ahankali ta bude ta tabbatarda shi dinne
Zuciyarta da gangar jikinta sunkasa hakura ta nufesa da wani irin gudu dake bayyanarda dukkanin sirrin zuciyarta akansa idanuwanta na cikowa da hawaye,
Yana ganin hakan ya miqe tsaye ahankali daidai isowarta ta fada jikinsa yayi sama da ita kamar yarinya qarama Yana kallon idanuwanta da hawayenta suka tsinke take suna gudu kan fuskarta ya sauketa tareda matseta jikinsa ahankali Yana kallon kyakkyawar fuskarta da fararen idanuwanta dake fidda hawaye sosai
Ya dauke gira daya Yana sake boyayyan murmushi tareda kamo fuskarta da tafin hannuwansa biyu Yana kallon cikin idanuwanta data dago ahankali tana kallonsa itama har lokacin idanuwanta hawayen sun kasa tsayuwa
Ahankali ya matso da fuskarsa dab da tata yakai bakinsa kan kunnenta Saida ya sauke wani numfashin daya sanyata dauke wuta cikin sirrantacciyar muryar da Bata taba jiba a hankali yace”
Kukan menene wannan??
Rintse idanuwa tayi da qarfi tana sake qanqamesa kirjinta na mannuwa da nashi yayi baya Ahankali Yana dafe kan kujerar dake bayansu Yana riko numfashinsa dake neman sauyawa ya lumshe ido tareda budewa ya kallon idanuwanta zuwa hancinta dayayi ja sbd kukan datake
Ya zura hannunsa daya zuwa bayanta ya riqo qugunta Yana sake Kai bakinsa kan kunnenta can qasa yace”
Kina tsoron mutuwana ne??….
Wani sirirn kuka ta fashe dashi Jin abindaya fada sbd har lokacin Bata gama fitowa da mummunan tashin hankalin tunanin rasashiba
Ya kamo hannunta suka zauna Yana kallon fuskarta tareda tallafo fuskar da hannuwansa Yana cikin yanayi na kulawa yace”
Ok shikenan ya Isa haka,
Ban mutu ba,Babu abindaya sameni ok?.
Rungume kanta yayi Yana shafa bayanta ahankali Yana zuwa kanta hartagama kukan tafara sauke ajiyar zuciya sai alokacin shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya tareda lumshe fararen idanuwansa yanajin nutsuwa na shigarsa sbd kukan nata ya wargaza duk wata nustuwarsa dama tunanin komai.
Saidaya tabbatarda tadawo hayyacinta tagama samun nutsuwa ya dagota ya kalli fuskarta datai qasa da ita sai alokacin takejin kunyar kanta ta Dan juyar dakai tana Jin sanyi da nutsuwa na dawo Mata.
Hannunta cikin nashi suka nufi bedroom dinsa da komai ya nuna yakuma bayyanarda Nan din ne asalin turakar sarki Dan kuwa duk wani Abu dake tsare a dakin me adon zaibane(golden) sai makeken gadonsa dako rabinsa ya ishesu su biyun hadda saurama
Sai wasu dogayen labulayen windunansa dasukafi Kama da kofofi sbd girmansu ta waiwaya inda madubinsa yake ya cinye kusan Rabin bangon gefen dayake ta tsaya gaban madubin tana kallon kanta cikin nutsuwa da nazartar rayuwa sbd wato Babu Wanda yasan me ubangiji ya tanadarwa rayuwarsa agaba.
Ta cikin madubin suka kalli juna ta sauke kanta ahankali tana juyawa daga kallon madubin ta taka ahankali tabar gabansa ya riqo hannunta Yana dawowa da ita baya gabansa wannan karon kallo daya yayi Mata ya dauke Kai sbd kokarinsa kada ya tashi a banza Dan kallonta kawai na canja Masa tsarukansa da dama.
Zamewa tayi ahankali tareda nufar toilet dinsa tashige ta rufo kofa tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi tana rufe ido cikin sanyi tace”
NURU why did you loose your control¿
Ta Jima ahaka tana sauke numfashi harsaida tadawo nutsuwarta gabaki dayanta kafin ta zare kayanta ahankali ta daure gashinta tsakiya ta yanda bazai jiqeba tayo wanka ta janyo towel dinsa blue ta dauro ta fito.
Kwance tasamesa a tsakiyar gadon takasa kallon gefen ta nufi madubinsa turare kawai tashafa ta juyo tarasa abinyi sbd sallah takeson Yi
Dole doguwar rigarta ta Dora kan towel din tayi sallolinta tana idarwa ta miqe ta zare rigar ta waiwaya takallesa a sace taga kaman yayi bacci saita sulalo ahankali ta hau gadon ta kwanta gefensa tana fuskantarsa ta zubawa kyakkyawar fuskarsa idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya a boye, ta gangaro da idanuwanta kan dogon hancinsa da duk farhat shi ta dauko
Ta lumshe idanuwanta lokacinda taji hannunsa na sauka jikinta ahankali ta cikin bargon dasuke rufe dashi
Daga hakan Bai qare komaiba sukai bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
MAMUH
ZAFAFA 2021! NEXT LEVEL
ZAFAFA 2021! NEXT LEVEL
ZAFAFA 2021! NEXT LEVEL
????????☄️???? ????
INA MASOYA MAKARANTA ZAFAFA BIYAR MASU SON SAI ZAFAFA SUNYI NISA ZASU SAYA? TOH KU MATSO, DOMIN ZAFAFAN LITTATTAFAN NAKU SUNYI NISA, DAI DAI DAD’IN KARATU