UBAYD MALEEK COMPLETE

Karkice komai kiyi shiru Ina Nan
Gani tareda ke.
Shiru sukai ahaka tsawon lokaci NURU na shafa bayanta ahankali ahankali tana Dan lallashinta tareda tunatarda ita tana tareda ita komai zaizo da sauki inshallah har afia din tasamu Dan sauki tanata sauke ajiyar zuciya akai akai.
Miqar da ita NURU tayi suka nufi gado ta zaunar da ita tareda Dora Mata kafafunta kan gadon ta ja bargo ta Dan rufe Mata Rabin jikinta ta kalleta da nata idanuwan dasuka sauya cikin kulawa da sanyi tace”
Bari nasa akawo Miki wani Abu kici
Jikinki ba qwari.
Fita tayi zuwa Palo takira masu aikin sashen tace akawo abinci Mara nauyi sosai da tea me zafi Sosai na lemun tsami da Zuma.
Da sauri cikin tsananin girmamawa suka amsa da to suka juya da sauri Dan ciko umarninta ita Kuma ta juya Takoma dakin taqaraso ta zauna gefen afia tana shiga nazari da tunanin asalin abin dayake faruwa kokuma yafaru sbd haryanzu takasa sanin takamaimai abindaya faru zancen guntu guntu kawai ta samunsa
Ta kalli afia ahankali tanason taga Bata cikin halinda zata iya tambayarta wani abun a yanzu
Gashi dad dinsu afian ma batajin zata iya tambayarsa Dan kuwa tambayar maleek kaman rashin girmamawa ne garesa saidai shi ya tambayeka Dan Haka bazata iya tambayarsaba saidai ko jekadi, idan tafita Takoma sashenta zata tambayi jekadi komai inshallah idan harta dawo daga delah daga Kai padima gida.
Da kanta ta bawa afia tea da ‘dan flat filled bread guda daya ta taimaka Mata Takoma ta kwanta cikin kulawa tace”
Kiyi bacci kina buqatan hutawa Kona awa biyu zuwa uku ne ke likitace kinsan kina buqatan hutu kafin kisamu nutsuwar yin wani tunanin ok?
Lumshe ido tayi tana gyada Kai
NURU ta juya tana cewa”
Zankoma Nima nayi wanka naci abinci…..riqe hannunta daya afia tayi tana kallonta da idanuwanta dasuka sauya take suna neman cikowa da hawaye ahankali ta bude Baki tace”
Karki barni Ni daya NURU wlh ina buqatan wani atare Dani sbd zuciyata da shedan na ingizani kaman na kashe kaina na huta da wannan rayuwar,
Bana tareda soyayya ta uwata danake tsananin buqata da kwadayin samu Amma bantaba samuba tun Ina qanqanuwata mahaifiyata Bata taba zaunawa tabani soyayyar uwaba,
Mahaifina haryanzu Banda masaniyar ko fushin dayake Dani ya sauka Dan haryanzu bansamu ganinsaba bare yasan halindanake ciki,
‘yar uwata ta jini yarinyace qarama da banama fatan taji abindayake faruwa,
Kakanni na mulki da rayuwar mulkice kawai agabansu banida kowa saike Dan Allah ki zauna taredani.
Kallonta NURU keyi cikin yanayi na damuwa da tausayi jikinta nayin sanyi tadawo ta riqo hannun afia din ta tayar da ita zaune tana cewa”
Muje can sashena zakifi samun nutsuwar hutawa farhat ma na can jekadi na kulawa da ita inshallah..
Da sauri afia ta dago ta kalli NURUn bakinta na rawa da mamaki tace”
Jekadi Kuma????
Ganin yanda Afia din ta firgita da Jin jekadi yasa NURUn Dan dakatawa da Mata kallon mamaki tace”
Lafiya dai ko??
Girgiza Kai afia tayi da sauri tace”
Mum da jekadi sune abin yafaru dasu ta Yaya jekadi zata dawo??…
Mummunar faduwa gaban NURU yayi tana yiwa afia kallon tashin hankali jekadi aka kashe kenan ko me???
Innalillahi wainna ilaihirrajiun..
Juyawa tayi tana neman ficewa afia tayi saurin biyota ta riqota tana cewa”
Ta Yaya akai Baki saniba bayan kin kwana a sashenki kinkuma ga bakiga jekadin ba,
Shin tadawo ne?
Gabaki daya NURU kasa amsa tambaya daya tayi sbd toshewar Kai
Harga Allah jekadi tamkar uwa ko Kaka take agurinta wadda takejinta Kamar jininta sbd a rayuwarta bayan iyayenta jekadi tafara nuna Mata qauna tamkar ta jini Dan haka bazata iya daukar zancen mutuwar jekadi Kai tsaye daga sama ba tana buqatan cikakken bayanin abinda yake faruwa ta dago jajayen idanuwanta ta kalli afia da itama itan take kallo cikin zaquwar Jin da gaske jekadin tadawo tace”
Kimin bayanin abinda yake faruwa
Acikin duhun komai nake akan al’amarin, shin meya samu jekadin da mum dinki Ni komaima bansaniba
Meyake faruwa”” zuwa lokacin hankalinta yafara mummunan tashi sbd Jin take al’amarin toko yayane ya shafeta sbd yanda rashin nutsuwa da tsoro dayake shigarta.
Afia ma sake rikicewar tayi tana kallon NURU zatai magana saita fasa ta koma ta janyo jallabiyarta me hula ta saka ta fito ta fice sbd dad dinta kawai zata iya gani yanzu kanta neman kuncewa yakeyi ta tsaya gaban NURU data kasa cewa komai tace”
Muje sashen naki Ina buqatan ganin Mr Omar Dan Allah.
Da ido NURU kawai ke binta sbd ita idan tashiga shock kasa komai takeyi Kamar Mara tunani Haka takama hanya suka Isa sashenta tun a palon ta tsaya tana kallon sauran masu aikinta dake tsatsaye suna jiran isowarta tun jiya Bata isoba gari na wayewa sukai ayyukansu suka Gama suka sake dasa jiran isowartata
Ko gaisuwarsu Bata samu amsawa Kai tsaye ta kalli Akira wadda take matsayin babbarsu idan Jekadi Bata Nan tace”
Akira menene yafaru akan matsalar mum dinsu afia??
Shiru Akira tayi tana sauke Kai Suma tuni kowa ya sauke Kai
Akira ta Dan dago cikin shakkun tsoma Baki cikin al’amarin sbd babban gargadi daga mr Omar na kada Wanda yafadi Wanda aka kashe din wa NURU Koda Wasa.
Sake maimaita tambayarta tayi wannan karon da ‘dan daga murya
Akira ta sake sauke Kai ahankali cikin tausasa harshe tace”
Kisa akai a sassan maleek a Daren shekaran jiya, Matar MALEEK ta farko itace ake zargin tayi kisan sai jekadi da aka tafi da ita itama sbd ansameta a gurin da abin yafaru…….
Kai tsaye NURU tace”
Waye aka kashen???
Tsit sukayi Akira na sake sauke kanta
Qasa cikin nutsuwa tace”
Babu Wanda yasani tukuna.
Shiru sukayi dukkaninsu daga NURUn har afia sbd tashin hankalin da mamakin al’amarin.
Zamewa afia tayi ta sulale kan kujera ta zauna tana rasa tunanin Yi
NURU ta zauna kusada ita tareda kallonta cikin tausayawa da sanyin yanayi tace”
Kaddarace wannan ki dauka daga ubangijine Kuma Inshallah zata samu kanta idan har batada hannu aciki
Sbd dad dinku bazai taba barinta cikin wannan halin ba komai zaizo ya warware Inshallah.
Kasa dagowa afia tayi tana sauraren abinda NURU take fada Mata Wanda hankalinta baya Kai tayi zurfi cikin tunani ta dago ahankali ta kalli NURU da jajayen idanuwanta tace”
Idan ta tabba cewan itace ta aika wane hukuncine zai hau kanta a shari’ancen Court??
Shiru NURU tayi tana kallonta cikin tsananin tausayawa kafin ta Dan dauke Kai cikin sanyi tace”
A shari’ancen musulunci shine Wanda ya kashe da gangan a kashesa,
A shari’ancen kotu ma idan dukkanin shedu sun bayyanarda yayi kisan da gangan ne ba bisaga qaddara ko dalilin Kare Kai ba ko dalilin ceton Rai to tabbas kisa ce ta Kai tsaye zata hau kansa….
Saurin dafa afian tayi ganin tana neman fita hayyacinta cikin sauri tace”
Dukkanin wannan kadaki yanke ko daya sbd bakisan akan me kisar ta afkuba kika tayine Dan kariyar Kai ko bisaga kaddara kadaki cire Rai daga sauqin ubangiji kiyi kokari kiriqe jarumtar fuskantar komai Inshallah ba hakan bane Ina Mata fata.
Miqewa NURUn tayi Jin tahowar farhat dake kiranta tun daga cikin bedroom ta juya ta kalli kofar dakin kafin ta dawo da kallonta kan Afia a natse tace”
Ina zuwa Bari nadubo ta.
Wucewa tayi zuwa dakin dake gefen nata Wanda aka tsarashi da komai na yara domin farhat din tana shiga ta qaqalo murmushi tana kallon kallon farhat din data shirya cikin riga da wandon asalin yadin qasar na sarauta me kyau ta qaraso gurinta tana cewa”