UBAYD MALEEK COMPLETE

Akwai lokutan da ba’a Kiran KALEEB kaman dad dinta dashima akwai lokacinda ba’a kiransa Amma yau dole zata kirasa sbd shikadaine zai Hana wannan rabuwar sbd iyayen nata Babu Wanda ya tsaya ya saurareta.
Cikin sa’a Kira biyu a na uku aka daga cikin sauri tayi bayanin ita wacece tanason mgn da KALEEB sanin matsayin UBAYD da iyalansa agurin KALEEB yasa aka Kai Masa wayar cikin girmamawa aka miqa Masa ya karba sbd sanin ba’a kawo Masa waya sai me mahimmanci idan bashi yace akawoba.
Tanajin nutsatsiyar muryar Kaleb ta nutsu jikinta na rawa zata fara Masa bayani taji durin motar dad dinta yadawo Wanda yasa gabanta faduwa.
A nutse ya zuro dogayen qafafuwansa dake sanye cikin black brian Atwood brand loafers kafin yafito gabaki dayansa cikin Ralph Lauren brown suit data fiddo da dukkanin hasken fatarsa ta asalin amhara ethopiano.
Kallo daya zakai Masa kasan shine ya haifi AFIA sbd Kamar dasukeyi tayi yawa duk da Kamar yanda bazakace LAILAH ce ta haifi budurwa kamar afia ba haka Kai tsaye Shima bazakace shine ya aje budurwar ‘ya ba sbd kyawun jikinsa da dukda yafara girma bai rabu da geamin ba ma’ana motsa jiki uwa uba ajinsa da asalin kyawunsa tareda izzarsa datake cikin jininsa da har gobe fresh take zamar masa Dan ko ita lailar har gobe duk gayunta da kyanta da Jan ajinta Rena kanta take agabansa shiyasa har gobe take kishin tazama wadda zata tsayu da kanta duniya tasanta da sunanta bada sunan waniba.
Ciki ya nufo qanshinsa na sauya atmosphere din gidan afia na ganin hakan tafara fadawa Kaleb abinda yake faruwa cikin nutsuwa da sauri….
Daidai shigowarsa farhat tasaki Laila tayo kansa da gudu ta fada jikinsa tana sakin sabon kuka Wanda yasashi sake tsuke fuskarsa tsaf wadda tasa Laila dauke Kai daga kallonsa ta nufi qofa zata fita baice Mata qala ba hakama AFIA qafafun lailan dasuka fita ta qurawa ido daidai Kaleb yagama jin komai zaiyi mgn sukaji daddadar muryar dad dinta data ratsa har cikin wayar zuwa kunnen Kaleb yace”
Na datse igiyan aurena dake kanki na sake ki you’re free to go MSS LAILAH OMAR.
Dif afia ta dauke wuta cikin tsananin tashin hankalin jin abinda dad dinta yafada Kamar daga sama taji muryar Kaleb cikin ikonsa na tsohon sarki yace”
Ki dakatar da ita injini.
Muryarta na rawa idanuwanta na dishi dishi tace”
Mum Kaleb yace ki tsaya karki tafi Injishi.
Qin juyowa tayi bayan Sarai taji me afia tace saidai bazata iyaba ta daga qafafunta ta isa bakin mota aka bude Mata tashige suna kallo ta tafiyarta idanuwanta na cikowa da hawaye ta maida tana qoqarin kawarda abinda yake taso Mata saidai takasa Saida ta fashe da qaramin kuka tana rufe fuskarta da hannuwanta har suka fice daga qatuwar harabar gidan.
Murya na rawa cikeda firgici afia tace”
Kaleb Ta fita,ta tafi tabarmu.
Wani numfashi Kaleb ya sauke akaro na farko a tarihin rayuwarsa da wani ya bijire Masa Kai tsaye Kamar agaban idonsa Wanda shikansa ubayd hakan yasa dukkanin wata sauran kaunar Laila yaqarasa fice Masa daga zuciya har abada.
Cikin wata irin murya me babban sauti Kaleb yace”
Ki sanarwa da mahaifinki Ina buqatar ganinsa cikin gaggawa zuwa delah.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR????????????
SAFIYYAH HUGUMA
BILLYN ABDULL
MISS XOXO
HAFSAT RANO
MAMUH GEE
DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN..
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
08085405215
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899[10/7, 9:09 PM] Xynerv Sadeeq Aderm????: UBAYD MALEEK
(Royalty versus love)
Mamuhgee
5
Zubewa AFIA tayi kan kujera tana sake wani irin kuka tana cusa kanta cikin tafukan hannayenta dasuke rawa.
Kamar zai wuce saikuma yaji afian na buqatarsa ayanxun sbd yasan tana cikin radadi.
Cikin takunsa na zallar nutsuwa ta asalin jinin sarauta yatako ya iso gabanta tareda miqa mata hannu batareda yayi mgna ba ta dago jajayen idanuwanta dake tsiyayar hawaye ba kakkautawa ta damqe hannunsa tana Kiran sunansa ahankali cikin kuka mara sauti.
Janta yayi farhat na jikinsa ya haye sama dasu zuwa ainihin babban bangarensa dake daukeda qaton palon farko Dana biyu Wanda baiyi girman na farko ba acikin palon na biyu Nan qofar qaton master bedroom dinsa yake ita Kuma lailah qofar bedroom dinta na tun a palon farko sukuma su afia din sukeda manyan bedrooms dinsu guda biya ata cikin Palo na biyu dake qasa ita daya farhat daya Amma a dakin AFIA din take kwana da farhat sbd tazama tamkar itace uwar farhat din duk da akwai tarin Nanny’s da masu aikin dake kula dasu duk su duka din sbd Sam tun tashinta kafinma haihuwar farhat mum dinsu tabarwa masu renonsu dawainiyarsu Sam batada lokacin kantama bare na ‘yayanta shi koyaushe tana gurin aikinda zata Gina sunanta duniya tasan da ita shiyasa acikin kadaici afia ta taso harsai bayan uwan farhat duniya tasamu sauqi sbd duk da akwai masu kula da farhat itakam Bata barmusu ragamar farhat din dukaba musamman da watanta goma cif aduniya lailah ta yayeta daga Bata nono tun afia Bata iya dawainiyar farhat ba harta iya shiyasa farhat din duk duniya tafi shaquwa da afia da dad dinta duk da tanason mum dinta Amma tafison dad dinta da afia itama afian sbd sanin mum ba lokacinsu takedashiba yasa girman dole yahau kanta duk da qananun shekarunta tazama itace madam din gidan dole masu aikin gidan kaf umarninta kawai suke jira sbd ita suka gani Matar gidan ko lokacin jininta tayi baresu masu aikin shiyasa basa Sonta bakuma su tsanetaba tunda batai lokacinsu bama bare musgunawa ko wulaqantawa da tozartawa ‘yayanta dai Kam suna tsananin sonsu da qaunarsu tareda tausayinsu duk sbd mahaifinsu UBAYD MALEEK Wanda suke tsananin jin dadin aiki a qarqashinsa duk da tsananin miskilancinsa da ikonsa mulki dake jininsa Amma baida tsanani ko tsauri ko kadan.
Table din lunch aka gama gyarawa yaja ‘yayansa suka isa dining room din farhat Kam harta sakewarta ganin ga dad dinta ga afia to itakam batada damuwa tunda dama haka suke rayuwa mum batanan koyaushe.
AFIA ce dai Saida qyar ta iya tuttura abincin Shima yacine kawai saidai Babu Wanda ya isa yace ya karanto kokuma ya fahimci halinda zuciyarsa da tunaninsa suke ciki cikin nutsuwarsa kaman koyaushe yaci abincinsa.
Ranar baisake fita ba yini yayi da yaransa cikin tsananin kulawa da qauna har dare sukai dinner sukaje sukai sallah da wanka suka kwanta AFIA na rungume farhat cikin jikinta sabbin hawaye masu zafi suna gangaro Mata.
Washe gari ma tare sukai breakfast da dad dinsu su suka fara wuce school da driver dinsu kafin shi daga baya ya fice.
Ahankali kwanakin suka fara tafiya damuwa tashigi afia sosai sbd yanda ta Sanya rabuwar iyayenta cikin ranta har abin ya tabata yafara taba karatunta komai Bata ganewa a makaranta tun Ana Mata mgn har Saida school din suka nema dad dinta sukai Masa bayanin kwata kwata Bata gane komai na karatu ko exams dinta gabaki daya Babu Wanda taci hakan yasa ya ragewa kansa aiki sosai sbd samun lokacin zama da yaransa Dan afia idan akai wasa zata iya samun matsalar qwaqwalwama.
Kullum takan Kira mum dinta Amma Bata wani Bata lokacin mgn she’s always busy with aiki aiki aiki hakan yafara Sanya afian jin haushi musamman da ita mum din Bata taba kiraba saidai ita takira ta bangare daya ga dad dinsu Yana iya kokarinsa duk kasancewarsa me tarin abubuwan Yi Amma duk ya taqaita sbd su ‘yayansa sai hakan yasa tafara dawowa hankalinta taji inama dad zaisamu farin ciki Kamar kowane mijin aure.
Ahankali ahankali trauma din rabuwar iyayenta yasaketa sbd watanni da aka ‘diba tuni ta sakewarta yanzu suna rayuwarsu cikin walwala musamman Mum Sarah dake kulawa dasu sosai yanzu kamar itace ta haifesu matarda tun haihuwar AFIA Amman UBAYD ta Aiko musu da ita daga delah gizah gashinan haryanxu tana taredasu tana musu aiki danma ta zama Kamar kakarsu Amma Mum Sarah suke ce da ita sbd tun afia na qarama da farko ma ta dauka itace ta haifeta saidatai wayo tasan lailah ce ta haifeta Amma duk da haka qaunar kamr uwa da ‘yace tsakanin afia din da mum Sarah,
Yanzu gidan rayuwarsu suke Kamar dama haka suke Basu taba rashin waniba agidan hakan yasaka hankalin dad dinsu kwantawa ya maida hankali kan harkokinsa musamman idan Yana dubin shekarun sauka mulkin NEGES ABDUL-SAMAD MUH’D KALEEB wato sarki na yanzu qanin mahaifinsa Kuma mijin mahaifiyarsa Wanda sbd Yana yarone mahaifinsa yarasu shiyasa akabada mulkin wa qaninsa kafin shi dansa ubayd ya girma Wanda Sam shi yanzu ba wani mulki dayakeso ko yake gabansa shiyasa bai taba sha’awar zama kusada mulkin ba yayi nesa dasu sbd ma kada son abin yasamu damar shigarsa Amma gashi lokaci na son qaratowa.