UBAYD MALEEK COMPLETE

Da wannan aka Isa gidan jaridar Kai tsaye aka kama shugaban companyn zuwa headquarters Kai tsaye Maleek yabada umarnin rashin sassauci ga binciken mutumin Wanda dam jira suke su Kuma jamian tsaron suka hau gana Masa azabar data sakashi saurin bada bayani Nan take cewar wani ne acikin Daren yakawo Masa information din saidai baiga fuskarsa sosaiba.
Kallonsa commissioner din yayi Yana jinjina Kai yace”
Me kagani Wanda zaka iya tunawa game dashi Wanda zai taimaka Mana nemosa da kanmu?
Wahalallen numfashi ya sauke Yana hadiye yawunsa dasuka gama gauraya da jinin dukan da akai Masa yace”
Idanuwansa zuwa saman hancinsa sbd Yana sanyeda baqin nose mask.
Ajiyar zuciya commissioner ya sauke tareda Mr Omar Wanda dama Allah Allah yake su samu bayani me kyau dazai bada hujja me ma’ana ya kalli commissioner Yana cewa”
Zansaka aturo Mana Wanda zai Mana sketch yanzun Nan kafin safe nakeson agama inshallah.
Juyawa yayi ya fice commissioner yasa aka maida managern aka rufe Kafin a me sketch din yazo.
Daganan Kai tsaye Maleek Mr Omar yakira ya sanar Masa komai
Shiru MALEEK yayi na ‘yan mintuna kafin ya Dan motsa tareda bude Baki yace”
Kaje da kanka gurin tareda wani me sketch din gurinta itama ayo na idanuwan Wanda yakai Mata meriz sai ahada agani Dan nasan mutum dayane sbd tabbatarwa.
Bayan Mr Omar ya tabbatarda anfara zana fuskar Wanda managern gidan jaridar yagani tukuna cikin tsakiyar Daren ya wuce delah Ana fitowa sallar asuba Yana sauka ya wuce Dan aiwatarda dayan aikin.
Qarfe takwas na safe afia ta Isa sashen NURU Kai tsaye bedroom dinta ta nufa har lokacin NURUn na bacci ta tashi ba saidai kasa hakurinda afia tayi yasa ta tada ita ahankali tana Kiran sunanta.
Bude ido NURUn tayi ahankali tana kallon afia dake tsaye tana kallonta cikin kulawa tace”
Sorry na tasheki
Ina tsananin buqatan taimakonki ne Dan Allah.
Da mamaki NURUn ta tashi zaune tana tattare gashinta ta dauki band gefen gadon ta daure gashin tana yaye bargonta tace”
Lafiya dai Ina ko??
Ajiyar zuciya afia ta sauke tareda juyawa ta nufi sofa ta zauna tana kallon NURUn tace”
Ki kimtsa tukuna sai muyi mgnar.
Zuro qafafunta qasa tayi tareda miqewa tsaye sanye cikin kayan bacci riga da wando masu santsi farare tas sun lafe jikinta ta nufi toilet tashige tana waiwayen afia akan tunanin ko wani abun yakuma faruwane.
Brush kawai tayi takasa wanka sbd hankalinta yafara tashi akan tunani da wasi wasin lafiya.
Tana fitowa Palo ta fito inda afia din Takoma ta zauna tana Dan kallon tv sama sama Amma hankalinta nakan yanda NURU zata karbi zancen saidai tasan yanada wuya takasa Mata wannan alfarman tunda aikintane.
Zama NURU tayi kusada afia din tana kallonta dukkanin hankalinta akanta tace”
Gani menene??
Numfashi afia tasake sauke akaro na biyu tana kallon NURUn cikin nutsuwa da nuna damuwarta da mahimmancin da maganar take dashi agurinta tace”
Maganar mum dinace yau nazo neman alfarma dama taimako agurinki,
Kinsan yanda nakeson mahaifiyata dakuma yanda nasamu wannan sassaucin yazo gareta, Dan Allah ko Zaki min alfarmar cika sauran formalities na karbota a matsayinki na lawyer duk da nasan Baki Gama zama cikakkiyar lawyer din ba Amma dai kinada damar zuwa.
Akaro na farko yau Ina roqonki wata alfarma Ina fatan Kuma Zakiyi sbd Ni Dan nasan abinda mum tayi Miki Bata cancanci ki taimaka din ba Amma Kuma Ina roqonki kiyi sbd Ni da farhat.
Tsit NURU tayi tana dauke wuta sbd Bata taba tunanin wannan maganar ba bama ta taba kawo tunanin shiga cikin wannan al’amarin ba gaba daya
Musamman na mum din afian Wanda shigarta kamarba bazai yiyuba sbd ba ita ke ikon kanta ba hakama ita tayaya zata iya zuwa Kai tsaye wannan aikin?¿
Kasa cewa komai tayi ta dago ta kalli afia batamasan me zata ce Mata ba Dan neman alfarma agurinta da afia tayi kamar abune da bazata iya cewa aa ba hakama Kuma tanajin shakkar amincewar sbd batamasan ta Yaya zata sanar da Wanda yake ikonta zancen.
Ganin Shirun NURUn yasa afia shiga damuwa takira sunan NURUn tana cewa”
Bazaki iyaba right???
Zubawa afian ido NURU tayi tana sake shiga tunanin rasa abin cewa ta girgiza Kai ahankali ta bude Baki tace”
Afia Babu alfarmar dazaki roqa gurina nakasa Miki matuqar Bata sabawa ubangiji bace saidai ta Yaya za’a sanarwa dadynki Kuma Kinga…..
Katseta afia tayi da cewa”
Dad dakansa jiya gabanki yabada damar komai gameda case din mum din wannan maganar ta sirrice yanzu idan nace zamu dauko lawyer daga waje then komai zai iya sauyawa
So please NURU ki amince dan Allah dad Bai taba dakatar damuba ko hanamu harkan data shafi karatu bare yanzu aiki Dan Allah ki yarda Ina roqonki.
Dagowa NURU tayi takalli afian tareda Dan sauke ajiyar zuciya tace”
Na amince Amma sai dad dinki ya amince Zan nema izininsa.
Shiru afia tayi tana kallon NURUn tana nazarin abin data fada din saidai tunda ta amince batada zabin daya wuce itama amincewa da bayanin tace”
Thank you.
Miqewa tayi zata fice ta dakata da cewa”
Anjima Imran zai iso inshallah saikuyi mgna.
Ficewa tayi tabar NURUn zaune mamaki na kasheta Jin da Imran zasu tafi kenan.
Faduwa gabanta yayi sbd tunani biyu dasuka shigeta take,
Na farko ta Yaya zata fadawa MALEEK maganar zuwan harda qarin Imran ne abokin aikin,
Ma biyu tayaya zata iya fita daga ita sai Imran bazata iyaba sbd tasan Imran din sai yayi kokarin tado Mata da maganarsu data wuce wadda hakan baya cikin abindata shirya dawowa dashi.
Bangare daya afia nason daureta da jijiyoyin jikinta.
Daqyar ta iya tashi daga Inda afian ta barta ta nufi bedroom tafada toilet jekadi dake jinsu batace komaiba ta juya ta fice daga sashen Kai tsaye ta nemi numbern Mr Omar ta fada Masa komai yace idan yadawo zai sanarda maleek.
Qarfe goma Sha biyu na ranar Mr Omar ya sauka a airport na gizah na dawowarsa Dan yagamo abinda yaje Yi Kuma adaidai lokacin Imran jalal ya sauka a airport din cikin sa’a suka hadu dukkaninsu motar masarauta tazo daukansu shi Mr Omar drivern maleek yazo daukansu shikuma Imran drivern Anneti afia tasaka yazo daukansa.
Kallon kallone yashiga tsakaninsu Mr Omar ya saki wani murmushi Yana miqawa Imran din hannu yana kallonsa yace”
Barka da zuwa Barr Imran jalal and all the best.
Miqa Masa hannu Imran yayi Yana cewa”
Thank you Mr Omar.
Murmushi Mr Omar yasake sakewa Yana Dan kallon gefen Imran din yace”
Kai kadai kazo??
I mean nasan kasan kana buqatan wani lawyern ga aikin.¿
Sai alokacin Imran yasaki murmushi Yana kallon Mr Omar din yace”
Aikina ne Kuma nasan da hakan shiyasa lawyern da nake buqatan muyi aikin tare tana Nan Dama
Fata dai kawai idan zaka iya jimirin ganin hakan.
Wani irin Murmushi me Fadi Mr Omar yasake Yana sake cewa”
Good luck with that too.”ya juya ya wuce Yana sake sakin murmushi yashige mota aka jashi sukabar Imran din a tsaye Yana bin motar da kallo kafin ya sauke numfashi me zafi yashiga tasa motar da akazo daukansa suka wuce Suma Yana Jin tamkar zuciyarsa nason karbuwa da qiyayyar Mr Omar sbd koyaushe shine yake shiga hancinsa da kudundune Amma sbd qiyayya bata cikin abindayake Bari Yana shigarsa yasa yake yaqar hakan Yana dannewa sbd ya dauki qiyayya wani aikin wahala da kake dorawa kanka yazo Kuma ya ringa wahalar dakai ka rasa focus da sukunin rayuwa karshe ka wargaza kanka agurin qiyayyar wani.