UBAYD MALEEK COMPLETE

Mum.
Zarewa Lailah tayi ta kurawa afia ido idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin baqin ciki da dumuwa tarema da tsoron halinda rayuwarta tashiga kokuma ma Wanda tariga tashiga,
Ahankali ta bude Bakinta dake rawa wani tsamin Baki ya feso yacika motar Amma afia ita Sam batama jisa sbd Babu abinda uwarta zata zama ta gujeta da rawar murya tana hawaye tace”
Afia,afia my baby,afia my little princess I’m sorry baby ki yafewa mum dinki Amma ki yarda Dani bantaba aikata kisa ba Kuma bazan taba aikatawaba…ban aikata ba…bazan taba iya aikatawaba…ban aikataba…banyiba…
Riqota afia keyi tana cewa”
Mum mum na yarda Baki aikataba
Mum na yarda
Na yarda mum”.ganin mum din takasa daina fadar Bata aikataba cikin firgici Kamar lokacin abin ke faruwa yasa afia rikicewa tana korarin kwantar Mata da hankali cikin kulawa hankalinta na neman tashi sbd ganin alamun kaman mum din har lokacin tana cikin shock saidai Kuma….
Imran ne cikin hali na damuwa daya shiga akan lailan tun lokacinda Mr Omar yayi Masa bayanin komai gameda Dan tabuwa da kan lailan yayi sbd Shiga hali na shock lafiya zata ringa komai Kamar yanda take sai dai idan ta tuno abindaya faru na kisan abin zai dawo Mata zata fara fizgewa tana fadar ba ita tayiba cikin tsananin tsoro da firgici,
Shi kansa bazaiso afia tasaniba sbd hankalinta zai tashi yakoma kan kula da neman lafiyar mum dinta bazata taba maida hankali kan karatuntaba Kuma Dan Haka shima ya shirya kula da al’amarin bazai Bari tasaniba yanzu sai tagama kammala karatunta tsaf yanama fatan zuwa lokacin lailan tasamu lafiya Dan Haka shima ya yanke shawaran komawa Vegas gabaki daya zai zauna da lailah Dan nema Mata lafiya ta dawo daidai ta gyara rayuwarta ta ingantata yanzu kan tunani da hanyar dazata bullar da ita sbd Lailah tamkar uwa ya dauketa Dan kuwa itace wadda tafi sonsa aduniya bayan iyayensa sbd itanema yake Paris baibi iyayensaba Koda tabar maleek dasu afia Basu rabu ba shida ita Kuma sbd itane yake tareda maleek Yana aiki a qarqashinsa farko sbd ya kula dasu farhat dasuka shaqu.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda fitowa ya zagayo yashigo bayan ya zauna dayan gefen lailan suka sanyata tsakiyansu ya dago ya kalli afia data fara shiga firgici cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace”
Tana cikin damuwar abin daya faru sbd case na zargin kisa wani abune da bakowa ne zai iya daukaba
Dole zata shiga wannan halin musamman yanzu data fito Kuma taganta agabanki Dole zataji wannan damuwar da shauqin son sanar dake ba halinta bane.
Hawayene suka gangarowa afia ta rungumeta tana sakin siririn kukan tausayin mum dinta ta dago tana kallonta tace”
Mum Inshallah komai yariga ya wuce bazai sake dawowaba
Ki yarda da wannan wata jarabawace Allah yayi Miki danki gyara Kuma Inshallah nasan kin gyara mum kimin alqawarin bazaki sake zuwa gizah ba sbd bakida abinda yarage Miki anan sai tarihi.
Kallon afia kawai lailah keyi da idanuwanta dasukai jajir tanajin radadin abubuwa da dama data rasa arayuwarta sanadin son zuciya da son Rai,
Ta rasa MALEEK namijin da bazata taba samun kamarsa ba a fagen komai Dan kuwa ya nuna Mata so da kauna da gata da kulawa da komaima Amma duk ta watsar ta tsallake a tunaninta zai zauna dakon jiranta,
Ta rasa Farhat dinta yarinyar da Bata morewa komai na soyayya ko kulawar mahaifiyaba da shaquwa Dan kuwa tasan NURU tariga tashiga ran farhat ta yanda bazata iya rabuwa da itaba ko yiwa wani kallon uwa idan ba NURUn ba,
Ta rasa darajarta,sunanta,mulkinta, dukiya da career dintama gabaki daya
Afia ce kawai abindake gareta yanzu sai Imran datasan har abada shima bazai gujetaba adaidai yanzu datafi buqatan masoyanta atareda ita.
Kama hannun afia tayi ahankali hawayenta suka gangaro kan fuskarta ta kalli afian tareda gyada Mata Kai tace”
Nayi alqawarin Inshallah bazan qara zuwa gizah ba sbd Nima na tabbatarda banida sauran komai anan sai tarihi Wanda bana alkhairi ba Dan kowa zai ringa tunoni amatsayin wadda tayi kisa labarinta ya Bata.
Sake karyewa zuciyar afia tayi da tausayin mum dinta ta yanda lokaci daya ta rasa komai Kuma tana fatan zatai tawakalli ta karbi hakan.
Kayan data shigo Mata dasu ta Sanya Mata tareda rufe Mata fuska ta Sanya Mata goggles din ta bude motar suka fito dukkaninsu ta sake damke hannun mum din cikin kulawa da qauna ta tsakanin ‘da da mahaifi tace”
Mum ki kula da kanki Zan ringa kawo Miki ziyara lokaci lokaci kinji¿
Ajiyar zuciya lailah tayi tareda kallon afian akaro na farko rayuwarta tace”
Allah yayiwa rayuwarki albarka afia
Allah yabaki ‘yayan dazasu San darajarki irin Haka da Miki biyayya.
Amin tace ahankali tana dagowa ta kalli Imran tace”
Mum na hannunka.
Guntun murmushi ya saki Yana gyada Kai yace”
tana hannu mekyau.
Murmushin yaqe tayi tana cewa”
Thank you.
Kama hannun lailan dake waiwayen afia tana daga Mata hannu yayi suka wuce itama afian tana musu har suka bace Mata ta saki numfashi a hankali tanajin nutsuwa ta juya ta fada motar da kanta ta jawo ta tada taja tabar airport din.
Ko data koma sashenta ta nufa sai alokacin tasamu nutsuwar cin abincin data manta rabon dataci
Taci ta koshi ta miqe ta wuce bedroom dinta tayi sallar azahar ta kwanta Dan tasamu baccin dazai qarasa wargaza damuwarta Dan kuwa dukkanin damuwarta ta yaye takeji.
NURU zazzabi yakamata sosai Wanda ya Hana musu bacci da daddare daga ita har maleek din sbd sosai jikinta yayi zafi tana kwance cikin jikinsa Yana rage Mata zafin jikin da nasa Dan kuwa yanajin yanda dumin jikin nata ke shigarsa Yana saukan Masa da kasalar sake shigar da ita jikin nasa itakuma tana lafe tana sauke numfashi ahankali cikin sanyi.
Kallonta yayi cikin Dan qaramin hasken dakin Ya shafa bayanta ahankali Yana sake ce mata”
Azinalehu (Sorry) cikin kunnenta da wata sirrantacciyar muryarsa da tsakanin jiya zuwa yau tasanta.
Ahaka yayita lallabata suka samu bayan sallar asuba tasamu bacci ya dauketa me nauyi sai alokacin yasamu nutsuwar kansa ya gyara Mata kwanciya tareda fitowa Palo sanyeda milk jallabiya me taushi ya zauna Yana daukan wayoyinsa ya kunna sbd yau yakeson Kai qarshen matsalar komai tunda sungama hada dukkanin shedodinsu dasuka tabbatar musu da zarginsu Akan Wanda suke zargi
Yana buqatan komawa Paris kodan rashin lafiyan Nan daya sameta.
Mr Omar yakira Kai tsaye yace”
A bayyanarda duka shedu akan yakoob a cikin kotu yau.
Cikin girmamawa Mr Omar yace”
Maleek haryanxu Yana maganar son ganin ‘dansa Kuma idan aka bayyanar a kotu cewan ‘dansa ne ya mutu zai iya bayyana komai a gaban kotu Wanda zai taba gizah da Kuma Anneti sbd al’amarin zaizo Mata da tashin hankali tunda Bata taba tsammanin hakan ba daga Wanda take aure
Kana ganin yakamata mu fitar da zancen duka a kotu?
Yan media zasu yada abin fiyeda komai ta yanda zai Yi Muni.
Shiru maleek yayi na wasu mintuna kafin yace”
Yanada damar yasan mutuwar dansa saidai baida damar fadar komai bayan abubuwan daya aikata da wannan za’a yanke Masa hukunci basai anbari yafada komaiba bayan wannan…..
Shiru yayi Yana kokarin daure abin dayake ji a zuciyarsa dasuka bayyana a idanuwansa yaci gaba da cewa”
Neges Kuma sbd daraja ta auren Anneti zanji da matsalarsa ta cikin gida batareda duniya tasan abin daya aikataba sauran haqqin Rai dake kansa Kuma tsakaninsa da ubangijinsane.