NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Sweetie nayi missing naki da surutunki sosai.

Miqewa tayi ta zare rigar jikinta ta jefa cikin wardrobe ta nufi toilet ta shige.

Kodata fito komawa gadon tayi ta haye ta kwanta gefen farhat ta gyara musu rufa Takoma bacci sbd baigama isartaba.

Qarfe tara ta farka lokacin har farhat ta Jima da farkawa ta bude idanuwanta ahankali tana kallon farhat dake Kiran sunanta cikin murna da farin ciki tace”

Aunt NURU yaushe kika dawo?

Tashi zaune tayi tana gyara gashinta da murmushi akan fuskarta tace”

Sweetie na barci nadawo
Ya kike?

Fadawa jikinta tayi ta rungumeta tana cewa”

Next time idan zakije tare Dani Zaki Zan biki kinji Aunt NURU.

Wani irin Murmushi ne ya saukowa NURUn ta kalli hancin farhat din zuwa bakinta dasuke Zak Zak Dana dadynta saita sake sakin murmushi tana saukowa gadon tace”

Kinyi brush?

Biyota tayi tana cewa”

Eh nayi nace next time zakije Dani??

Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalli farhat din ta kamo fuskarta taja hancinta ahankali tana murmushi tace”

Wannan hancin Ina sonsa sosai kaman yanda nake son sweetie dan haka kidainama tambayan idan zanje wani guri ba dakeba ok¿.

Cikin murna tace”

I love you too lewa.

Knocking kofa akai ahankali tareda bude kofar aka shigo
NURU ta dago tana waiwayowa kofar sukai ido biyu da afia dake kallonta da dukkanin hankalinta tana nazarin NURUn da akace batada lafiya saidai bataga alamar ciwo atareda NURUn ba jikinta ba inda ya nuna alamar akwai ciwo tareda ita ta karaso ahankali cikin ‘yar kulawa da alamar tambayarta tace”

Jekadi tace bakida lafiya da fatan dai ba wani serious ciwo bane ko??

Murmushi NURU tasake tana matsowa gaban afia din tace”

Naji sauki kawai gajiya ce da rashin isashen bacci Amma yanzu lafiyana kalau.

Kallon cikin idanuwanta afia tayi tana kokarin karanto idan da akwai ciwon atareda NURUn tace”

Mezaisa ki kasa samun isashen bacci bayan kina samin hutu sosai bakida aikin komai a gabanki….

Aiki dad dinku yabani Wanda duk ya kawo hakan yanzu dai inason Baki hakuri akan rashin samun damar zuwana gurin mum dinki I am really really sorry for that Kuma Ina fatan komai yatafi yanda ake fata?

Ajiyar zuciya afia ta sauke tana qarasawa bakin gadon dakin ta zauna tana cewa”

Komai yatafi yanda akeso mum Dina tana Las Vegas tareda Imran Wanda yakoma can yanzu da zama da aiki sbd su manta rayuwarsu ta baya su fara sabuwar rayuwa Mara damuwa da Danasani.

Numfashi NURU ta sauke cikin ahankali tareda ajiyar zuciya tana kallon Afia da taushin murya tace”

Ina musu fatan kyakkyawar rayuwa me Dadi da amfani.

Thank you afia tace tana kallon fuskar NURUn data sauya Mata gabaki daya.

Wanka NURU tashiga ta fito cikin nutsuwa ta shirya cikin doguwar riga golden me sequence ajiki suka zauna dukkaninsu su ukun anan sashenta sukai breakfast tare suna gamawa suka dawo Palo suka zauna NURU na Shirin zuwa gurin Anneti afia ta kalleta tareda dawowa gefenta ta zauna cikin nutsuwa ta kalleta tana tattaro abinda zata fada Mata tace”

Shin kinsan case din kisan da mum take ciki padima ce wadda ake cewa ta kashe……

Wani irin kallo NURUn juyo tanayiwa afia din da dukkanin fararen idanuwanta.

Wata ajiyar zuciyar afia takuma saki tana dafa hannun NURUn tace”

Padima ce wadda dukkanin labarai da duniya ta shedarda an kashe….
Hawayen dasuka ciko fararen idanuwanta dasuka koma ja Nan take suka gangaro kan fuskarta ta sake kallon afian da kyau tana kasa gasgata zancen sbd bazai yiyuba babban zance irin wannan a boye Mata
‘yar uwarta jininta aka kashe ace Bata saniba sai yanzu bayan wadda tayi kisan har ansaketa ta tafi Kuma maleek na sane da hakan,wane hali iyayenta suke ciki gameda wannan mummunan al’amarin na rasa padima itakuma Bata tareda dasu a lokaci irin wannan miqewa tayi zuciyarta da idanuwanta na rufewa da wani irin yanayi Mara Dadi da damuwa
Afia tayi saurin riqota tana Miqewa tsaye cikin nutsuwa da kulawa tace”

NURU ki kwantar da hankalinki anyi bincike angano komai da cewan ba padima bace kawai yan media ne suka juya zancen sbd basusan ainihin wayeba aka kashe angano komai yanxu tareda gano Wanda sukeda hannu a komai har kisan tsohon NEGES wato mahaifin dad dinmu komai ya wuce yanzu Inshallah…

Girgiza Kai tafarayi ahankali hawayenta na tsananta gudu cikin wani irin yanayi na toshewar Kai tace”

Bani wayanki inason Kiran abal Dina Ina buqatan Jin halinda suke ciki,
Ina buqatan magana da padima
Mezaisa padima ta zauna Nan har irin wannan Abu yasameta,
Ni gabaki daya ban fahimta ba,abal nakeson magana dashi yanzun Nan……

Cikin sanyi da son kwantar Mata da hankali afia ta miqa Mata wayarta tana cewa”
Dan Allah ki nutsu kada ki dagawa su abal din naki hankali idan har Basu saniba, ki tambayeshi ta yanda bazaki daga hankalinsu ba muji idan padiman na taredasu.

Bata tsaya sauraren sauran bayanin afia ba ta hau saka numbobin abal dinta ta Danna Masa Kira zuciyarta na rawa.

Kamar zata tsinke saigashi ya daga cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yayi sallamar data Sanya NURU saurin riqe numfashinta tana seta muryarta tace”

Abal.

Jin muryar NURU yasa abal din tashi zaune daga kishin giden dayake Yana kallo a tv cikeda kewarta da kaunar ‘yarsa yace”

NURU kece?
Kina lafiya?
Ya kike?
Yaya maleek da yaransa?

Shiru tayi zuciyarta na sake bugawa ahankali muryarta na rawa tace”

Abal Ina padima?

MAMUH

[10/11, 7:40 AM] +234 806 789 0769: Mamuhgee 49
Shiru yayi Yana kallon padima data lallabo ta tsaya gefensa Jin sunan NURUn daya ambata tana kallonsa da idanuwanta dasukai wasu iri kaman me jiran sammaci ya Dan gyara zama Yana sake murya cikin farin cikin Jin NURUn yace”

NURU me padima zatai Miki??

Shiru tayi sbd jikinta daya fara sanyaya ta bude Baki da qyar tace”

Abal labarin rasuwarta nake samu yanzu duk tsawon lokacin Nan bansan meyake faruwaba Ina matsayin ‘yar uwa Kuma ‘ya acikinku
Dan Allah abal ka sanar Dani komai Kuma idan padima na Nan inason jinta ko yayane..

Wasu hawayen takaicine da sanyin jiki suka gangarowa ammynsu Jin abinda NURU ke fada
Abal kuwa nutsar da murya yayi cikin kwantarwa da NURUn hankali da murya Kai tsaye ta matsayinsa na mahaifinsu su duka yace”

NURU dagani har ammynku da meryam munanan lafiya cikin kwanciyar hankali da nutsuwa sakamakon Miji na gari me adalci da Allah yabaki,
Muna cikin masarautar delah a kebe cikin walwala da wadata tareda ni’imar duniya,
Saidai har gobe da kullum zuciyata takasa samun kwanciyar hankali na uban daya haifi ‘yar da Babu Allah ko miskala zarratin acikin ranta face zuciya irinta kafiran farko da qyashi da hassada tareda taurin Rai yagama cikata,
Padima na nan da ranta saidai banajin tanada sauran qimar da Zaki cigaba da kiranta ‘yar uwarki sbd ta nunawa duniya cewan Babu qauna ta jini a tsakninku har abada
Muda muka haifeta Dole zamu zauna da ita Amma ke Kam ba Dole sbd ta wuce iyakarta….

Tsananin sanyi jikinta yayi da kalaman abal dinsu ta sulale ta zauna bakin kujera ta zauna cikin sanyi da sagewa tace”

Abal meya faru?
Me padima tayi wannan karon?

Kai tsaye yace”

Padima taje gidanki da niyar rusa kyakkyawar rayuwar da Allah yabaki ta hanyar niyarta ta kashe mijinki Wanda tabawa gubar meriz yasha wadda Allah ne kawai yayi da kwanansa agaba da babushi Kuma niyarta shine su maqala Miki wannan sharrin da ita da mahaifin amed dama amed din….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button