NOVELSUBAYD MALEEK COMPLETE HAUSA NOVEL

UBAYD MALEEK COMPLETE

Innalillahi wainna ilaihirrajiun
Innalillahi wainna ilaihirrajiun”
Shine kawai abinda tasamu bakinta yake iya furtawa ahankali idanuwanta na bushewa sbd tsananin firgici da tsoron maganar da abal din yafada cikin rawar murya tace”

Abal abawa padiman wayan Dan Allah…

Shiru yayi Yana shakkar hakan sbd har cikin ransa baya buqatan alaqar NURU da padiman yanzu ya dago ya kalli padiman datai tsamo tsamo da idanuwanta dasuka Gama jemewa ya miqa Mata wayar.

Karba tayi ta Dora akan kunnenta cikin sanyi tace”

NURU

Dakakkiyar ajiyar zuciyar karfin hali NURU tasake cikin kasa gasgatawa tace”

Padima menene abindaya faru???

Numfashi padiman ta sauke cikin muzantuwa da wata irin kunya da wulaqanta saidai Babu yanda zatayi bayan fadan gaskia ta bude Baki ahankali tace”

Dukkanin abinda abal yafada hakane,
Banida ciwon komai nai Miki karya naje gurinki da burina na dabam Wanda yakaini ga sawa maleek garin meriz Wanda zai kawo karshen rayuwarsa saidai hakan be faruba suka gane nice na aikata hakan
Sukaso hukuntani saidai Kuma Basu kaiga yin hakanba amed sukaso kasheni Dan boye tonuwar asirin dayasa na kashesa batareda nasan Yaya zanyiba
Maleek ya zabi da a boye Miki komaine sbd gudun shigarki damuwa….
Zubewa qasa tayi duk da NURUn Bata gabanta cikin tsananin damuwa da kanta daya fara juyawa alamar zata birkice tace”

NURU ki yafemun kinji
Kisa maleek ya yafemun kinji
Kisa abal ma ya yafemun kinji
Kisa ammy ma ta yafemun kinji
Bani nakashe amed ba shine ya kasheni na gudu na boye bayan maleek kinji,
NURU kisa mutanen gizah ma kowa ya yafemun kinji
Nima kisa na yafewa padima kinji,
Padima Tama lalata rayuwarta gashi yanzu takoma Kamar Mara hankali nake gani
NURU kinyafemun ko???…….

Shiru NURU tayi dukkanin jikinta na sake yin sanyi sbd daga maganganun padiman tagama gane kanta ya juye wannan rayuwar dame tayi Kama?
Wannan wace irin masiface me mummunan karshe Wanda zaikai bawa ga irin wannan makomar gashi padima da kyanta da cikar zatinta Takoma kayan kwankwani saika kwankwasa kaji sauti.
Cikin sanyin jiki da muryarta data toshe tace”

Na yafe Miki padima Allah ma ya yafe Miki yabaki lafiya idan kinada rabon warkewa.

Karban wayar abal yayi Yana cewa amin dukkaninsu jikinsu a Sanyaye sbd idan abin ya juyo padiman nada tausayi wani lokacin sbd lafiyayyan budurwa takoma saidai zaman gida sbd Babu Wanda zai iya aurenta ahaka saina Allah musamman abubuwan nata sunyi yawa,
Ga rashin budurci,ga mummunan zuciya data kaita ga hakan ga na karshe rashin hankali daya shigo.

Kallon meryam ammy tayi tana cewa”

Rakata daki ki zaunar da ita har abin ya lafa ta ‘dan dawo daidai.

Kallonta Meryam tayi tana kamo hannunta ta jata itakuma tabita tana ‘yan maganganunta qasa qasa batareda kowa yamaji me take fadaba sbd sanin batada zance saina a yafe Mata ba ita takashe amed ba amed ne ya kasheta.

NURU najinsu tayi shiru tana sake Jin al’amarin har cikin ranta dukkanin gabobinta sun saki takasa cewa komai
Abal cikin sanyi shima yace”

Maleek da kansa yasa aka kawomu Nan Dan mu samu sauyin rayuwa tareda boyewa duniya abinda padiman tayi Wanda bazamu taba daina gode Masa akan hakan ba
Ya allah yakara rufa Masa asiri duniya da lahira yayiwa rayuwarki taredashi albarka da zuriar dazaku samu agaba.

Amin ta furta daqyar sbd toshewar da muryarta tayi da mamaki da firgicin dukkanin abin dataji yanzun.

Miqawa ammy wayar abal yayi ammyn najin muryan NURU taji hankalinta ya kwanta sbd Koba komai sunada sauran ‘yaya biyu dasuke fatan su zamo tafarki na gari agaresu Wanda zasuyi alfahari dasu duniya da qiyama.

Meryam ce ta sake sosai tayi magana da NURUn Wanda har lokacin Bata dawo hankalinta duka ba da Haka ta ajiye wayar tanajin sauran bayanin da afia ke koro Mata na NEGES da sauran labarin.

Sai alokacin hawayen tsananin son mijinta Da kaunar iyayenta suka gangaro Mata ta miqe ta nufi dakinta ta turo kofa ta zauna bakin gado tareda fashewa da wani irin kuka Mara sauri sosai tana rufe fuskarta da tafin hannuwanta sbd tabbas idan tace batajin tausayi da kaunar Yar uwarta tayi qarya saidai Kuma bazata iya cigaba da rabartaba Dan kuwa wannan wani al’amarine me girma daya rusa rayuwar farin cikin gidansu dasuka taso dashi Dan kuwa iyayenta har abada bazasu daina Jin damuwa da baqin cikin ganin padima acikin wannan halinba Dan haka tasan farin cikinsu Yi zai ringayi Yana daukewa Dan ‘da duk lalacewarsa acikin Rai yake.

Sai yamma lis tasamu damar fitowa bayan ta sauya wanka da Kaya idanuwanta da fuskarta a ‘dan kumbure
A shirye ta fito Dan zuwa gurin Anneti farhat da afia ma dake sashen har lokacin sbd takasa tafiya tabar NURUn cikin wannan halin suka miqe tareda jekadi da Akira suka nufi sashen Annetin wadda itama tana Dan daurewane sbd ita qaddara ba’a canzata Amma tana cikin hali na damuwa da baqin cikin wannan al’amari daya faru na NEGES Wanda a safiyar ranar ya tattara yakoma delah gabaki daya da zama sbd shirye shiryen Nadi da aketayi Wanda ake qara la’antarsa akan wasu abubuwan da dama
Anneti kuwa maleek ya hanata zuwa koina yace tayi zamanta a gizah sbd dama auren kawai sukedashi a tsakaninsu babu wani kebewa irinta ma’aurata dasukeyi sbd tsufa da manyanci daya Kama.

Ganinsu yasanyaya ranta musamman NURU wadda tagama samun tabbaci daga gurin jekadi cewar tazama cikakkiyar macen UBAYD MALEEK wadda a fili ya nuna hakan Kuma ko agurin kwanciya da ita ya nuna hakan sbd alamu dasuka nuna ba so daya ya sadu da itaba acikin daren wannan shine cikakkiyar alamar tasace ta har abada tasamu guri me girma a zuciyarsa da rayuwarsa da yardar Allah.

Kayan marmari aka kakkawo aka jere musu Anneti tasa aka kawowa NURU nata hadin wani sirrin daban suna ‘yar Hira sama sama jekadi na miqo Mata tana Sha a Dan kunyace harsuka Gama sukai sallar magriba Basu barota ba sai bayan ishai
Suna fitowa afia ta kalli NURU cikin sakewa tace”

Meye sirrin wanna maganin da Anneti ke Baki?
Kodai na……

Kallonta da NURU tayi yasata dakatawa da zancen tana ‘yar dariya.

Murmushi NURU tayi tana tafiya a natse tana cewa”

Idan nafada Miki sirrin bazaki iya bacci ba nikuma inason ki ringa samun bacci yanzu sbd ki koma AFIA UBAYD MALEEK dinki ta asali duk wannan ‘yar ramar ta fice.

Murmushi afia tayi tana cewa”

Thank you Ms NURU YONAS.

Suna Isa ko zama basuyiba saqon mr Omar ya samesu na cewa gobe zasu koma Inshallah Dan Haka su shirya.

Wanka kawai tayi tayi Shirin bacci ta haye gado ta kwanta da wuri sbd ciwo ciwon Kai datake ji.

Washe gari da safen kayanta ta hada acikin qaramar akwati saina farhat data saka Akira ta hada Mata ta shirya tsaf ta nufi sashen Anneti tareda jekadi dake gefenta tana sake nanata Mata wasu maganganun akan zama na aure.

Koda suka Isa ga mamakinta kusan kayayyaki ta tarar jere a tray Ana jiranta Kai tsaye Anneti ta nuna Mata kujera tana cewa”

Zauna jekadi ki nuna Mata komai yanda yake ta shanye shekara daya zasuyi ajikinta suna aikinsu.

Miqewa tayi ta shige sbd ganin yanda NURUn kejin kunyar Sha din
Tana shigewa jekadi ta zage tana zuzzuba matasu tana Bata tana shanyewa a wahalce sbd sunyi Mata qarfi sosai a Baki daqyar ta shanye kusan duka sauran daya rage ganin tana neman yin amai yasa Dole jekadi ta qyaleta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button