UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shureim ya girgizakai kan yace”No Stop saying dat..Any tin will be fine kaji.Just keep praying,in nadawo aiki zamuyi..mgana”Dagahaka sukayi sallama zukatansu babu dadi..

   bai koma barcin ba ya mike bayan ya duba agogon bangon dake kafe gefen side drower gadonsa, yaga har pass 8 salati yayi tare da mika dabadon Dan’uwa ya tashesa ba dayayi missing din wata shari”a dazai gudanar yau dinnan da safe,mikewa yayi yafada tiolet agurguje ya fito ya shirya cikin shigansa na Suit, dinsa na yau din Ash and black ne yadaure wuyansa da nektie dinsa kafafunsa yana sanye da Rufaffan takalmi kan nasa yasha gyara kamshin turaran MAN kawai ketashi duk inda yabi koya gifta yar jakarsa yadauko ya nufi falon fuskarsa na Fitar da Annuri da kwarjinsa mai karamasa kima a idon jama”a.

     Shigowarsa baban Falon ne yacikaro da karime na goge tana gashininshi tazube kasa gwiwa bibbiyu tana Fadin”Barka da fitowa yallabai”Kallonta yayi kan yace”Wai baba sau nawa zance miki bani son wanna dukamin dakike yi ne ehe’yafada Ranshi abace,Dukar da kai karime tayi kafin tace”Yallabai don…bani so kawai kidaina Nifa danki ne Baba kokuwa uwar tawane, baki so kizama ai shikenan”Yakatseta lokaci daya.

  Saurin mikewa karime tayi tana fadin”wane ni Ranka yadade,Kowacce uwa zata so ta mallakeka amtsayin danta”Rausayar dakai yayi kafin yayi mgana lami tafito daga kichen hannunta dauke da kololi itama cikin girmamawa ta rusuna tana gaisheshi amsa yayi yana Fadin”Allah nakusa yimuku yaji agidan nan”Yafada fuskarsa ba alaman dariya da Sauri sukace”Tuba muke yallabai bazamu kara ba”Suka fada suna dariya don susan laifinsu.

Mirmishi yayi kafin Lami tamike ta isa ga dining tana Fadin”yallabai An kammallah kalacin fa”Shuru yayi mata still yana tsaye kamar bazai tankaba Sai chan yace”Ummi tafito kuwa”cikin  Fuskar damuwa karime ta girgiza masa kai Kada kai kawai yayi yawuce saman cikin sanyin jiki binsa sukayi da kallo cikin tsausaya maasa saboda yadda bai iya hada komai da mahaifiyarsa..Basu taba ganin Mutum mai mutumci da daraja talakawan dasuke karkashinsa ba kamar ubangidansu Mu”azzam.

       Cikin Sanyin jiki yasaka hannu da Niyar nooking din kofar sai kawai yaji ta bude kai tsaye yasakai dakin na Ummi wanda ke tashin kamshin Turaran wuta na yan maiduguri,Bedroom ne mai girma da fadi wanda yaji kayan alatun na more rayuwa Tamfatsetsen gadonta Royal bed mai hade da makeken wardrope,wanda yakusa cinye Rabin dakin sai dressing mirror din dayake shake da kayan kwalliya na mata dakin Gabadayansa Coffea colour ne.

  Zaune Ummi take kan Wata yar kujera gaban mirror tana taje kanta wanda yake da tsawo da sansti ta shirya cikin Riga da zaninta na Atamfa tayane jikinta ta lifayanta wanda bata rabo dashi,cikin sauri ya karisa kusa da ita yasaka hannu ya karbe Cumb din datake amfani dashi yacigaba da sharcemata kan,yana kallon Fuskarta ta madubi idanunta sunyi jawur alaman Tasha kuka kenan,ganin yana kallonta yasa tayi Saurin kauda kanta yana gama taje kan nata, yasaka band ya tamke matashi dam,daman yasaba Mu”azzam din Ummi babu Abunda bai iyaba indai na matane, don Mata suka Renesa lol.

    yana gamawa ta rufe kanta da lifayanta,ta mike tana ganinsa sai ta juya fuska zata wuce da Sauri ya zube agabanta yana Fadin”plz Ummi karkiyi Fushi da mu”azzam dinki,”yafada yana karya murya kamar zaiyi kuka cikin hanzari ta juyo garesa tasa hannuwanta ta dagosa kai tsaye ta rumgumesa lokaci daya tafashe da kuka mai cin rai.

Riketa yayi sosai yana Fadin”Haba Ummina so kike Tsinuwan mala”iku sukamani? Don Allah Ummi kidaina zubar da hawaye akaina don Allah inhar kinaso na mutu nasamu Rabauta Ranar gobe kiyama”yafada muryansa tafara chanzawa dago da kanshi yayi yasa hannunsa yana sharemata hawaye itakuma tana kallonsa lokaci daya suka sakarma juna mirmishi kallonsa take kafin tace”My Son..Dont leave me..Kaikadai gareni kai ne Sanyin idanuwana..Kada kabari Shettima yarabani dakai kamar yadda yarabani da mahaifinka lokacin danake tsantsan bukatarsa”Takareshe fada hawaye suna gangaromata…

   Sharemata hawayen yasakeyi yana fadin”UMMINA..ke mahaifiyace mafi soyuwa azuciyar mu”azzam dake nafara bude ido aduniya,Kece ginshikin mu”azzam da kokarinki da himmanki na kawo iyanzu..,Wlh tallahi bazan taba gazawa da bauta miki ba har Sai Ranar dana daina Numfashi”Saurin Rumgumesa tayi tana Fadin”I love u Son..”Love u too Ummina yafada yana kara kamkameta.

 
   Tare suka sauko hannunsu sarke da juna Karime da Lami Tunda suka hangosu bakinsu yaki rufuwa,suna ta mirmishi na jin dadin ganin Uwar dakinsu ta sauko..Gabadayansu zubewa sukayi suna fadin”Brka da Fitowa hajiya”Kayatattacen Murmishi tayi musu kan tace”Yauwa,karime da lami kuntashi lafiya? ina Uwani”? Lami tace”Uwani na kichen tana ida wanke wanke ne”Tafada tana sanda kai, Wucewa tayi hanunta cikin na mu”azzam,tana Fadin”Breakfast fa,Son zai Fita”Da Sauri karime tace”Tuni aka kammallah Hajiya”Gyada kai tayi kan tace”Yayi kyau.kuje sai na kiraku”Rankwafawa sukayi suna Fadin”agama lafiya hajiya”Daga haka suka fice daga Falon.

  Ummi da kanta taciyar da danta wanda daman,haka takemai bayan tagama bashi,itama yabata kafin ta yagi Tissue ta gogemai, baki ita tariko mai yar jakarsa suka jera hannunsu sakale cikin na juna,suna hiransu har haraban gidan,Ushe da Sani maigadi dake zaune sukayi Saurin tasowa suka zube suna kwasan gaisuwa,Amsawa tayi cikin Sakin Fuska kafin tace”Ina Falalu ne”? Sani yace’Falalu ya zagaya baya hajiya Fulawoyin ne duk sunyi ciyayi shine yake ragewa’Yafada cike da girmamawa.gaisawa sukayi da mu”azzam din wanda shima yake amsa musu cikin sakewa

   Ushe yayi Saurin amsa jakar hanunun hajiya kafin tarakasa har bakin mota sani maigadi shiyabudemai kofar motar nasa 320 kirar Toyota black colour, Da kanta tasakashi cikin motan kafin tamai kiss a kumatu tana Fadin”My son..Allah ya tsaremin kai..Yacigaba da karemin kai,Allah ya albarkace dan albarka”Tafada tana sakin mai mirmishi.

Fuskar mu”azzam tacika da Fara”a lokaci daya yana amsa da Amin Amin Ummina sai nadawo”Rufemasa murfin motan tayi sai lokacin Ushe ya shiga bangaren direba yaja motan Sani maigadi ya bude musu get suka fice Ummi na daga musu hannu..Harsuka fice tana nan tsaye kafin takoma cikin gidan..Sani maigadi ya murmusa shifa tunda yake aduniya baitaba ganin soyayyah uwa da da, irin na Hajiya da yallabai ba.Haka take kullum ita zata rakosa tasashi amota harsai yabacema ganinta.

  Tana komawa ciki kandaya daga cikin kujerun tazauna tana kwalama karime kira,karime tafito da hanzari ta zube gabanta tana Fadin’gani Hajiya..”Hajiya Suhaima takalleta tace”dauko min phone dina abedroom”Tafada tana jiginar da kanta jikin kujera,karime ta mike da hanzari tahaura sama ta dauko mata wayan Rankwafawa tayi cikin girmamawa tamika mata wayar cikin hanzari tayi latse latsen ta kafin takara akunni.

       “Yaya..”Naji ta ambata lokaci daya Fuskarta ta washe da Fara”a, Dagachan, bangaren Hajiya baraka tace”Suhaima ya kuke”Ta amsa Da” lafiya kalau muke..Ya kafan kuma yaya?Hajiya baraka tace”Tayi sauki wlh, harma ina zagayawa ni kadai”Washe baki Ummi tayi kan tace”Alhamdulillah yaya jiki kam yayi sauki…Naso zuwa cikin satin nan but zan bari wekeed muzo Da Mu”azzam”Hajiya baraka tace”Ayya bakomai kullum kuna hanya da kunbarshi sai nazo ni tunda kafa tayi Sauki”da Sauri Ummi tace”A”a yaya mu zamu zo,ina son yake”Tace”Yafita tun Safe ina khalilullah yake?Ummi ta amsa da cewa”Shima ya fice Tunsafe yaya”Hajiya baraka ta Murmusa kan tace”Allah yacigaba da musu jagora”Ummi ta amsa Da Amin sun cigaba da hiransu kafin suyi sallama kowannensu ya jiye wayar Ransa na masa Dadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button