UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dakyar Yakura talallabata tasha kunun kanwar data dama mata,sai dumamanman Tuwon data zubomata duka ta sharesu don ba laifi taji yunwa,yaran kuma zamzam aka cigaba da basu dayake basu da rigima kafin Ruwan Nonon yazo.


Mu”azzam kuwa Tun ficewar Zahirah yarasa control dinsa,kuka yake kamar wani karamin yaro,Ummi na zaune tana kallonsa ko ajikinta,mikewa yayi yana tangadi ya nufi shashensa ganin yana layi yasa ummi mikewa tana kwalamai kira,ammh yayi mata banza ya shige shashensa ya rufe kofa,Ummi ta zata abun nashi wasa ne shiyasa tayi komawarta ta zauna tana fadin”Ka ma dawo dai dai ne yaro..”

  shiko cikin wannan halin ya lalubo Dr Abduljabar awaya yana rokonsa ya taimakeshi yazo unguwarsu ya duba masa zahirah,yana ma tambayasa lafiya ammh yakasa mai mgana saboda yadda Saitin zuciyarsa ke bugawa,Dr.Abduljabar yazo har maitama yagama karadeta babu Zahirah babu dalilinta,mu”azzam yakara rokonsa yaje masa har tashan mota nan ma lbrin daya ne bata ba mai kama da ita,sai gashi dalilin dalilai yasa Dr.Abduljabar yaje har gidan minister Alhaji gaddabi Nura neman Zahirah,Sakamakon mu”azzam ko mikewa yayi jire ke neman gadasa shi,shiyasa ya wakilta Dr ammh shima lbrin daya bata zo ba.
  

  Asma”u da mamanta sun shiga tashin hankali don babu shakka Ummi ta samu lbrin cikinan koma miye to abun bamai dadi bane,gashi tana ta kiran wayanta akashe balle taji meyafaru kuma bata da wanda zata kira yafadamata abunda ke faruwa.

Lokacin da Dr.Abduljabar kefadama Mu”azzam bai ga zahirah ba kashe wayar kawai yayi ya sulale bisa kafet hawaye suna kwaranyo masa,yasani Shikenan Ummi ta saka Almakashi ta datse Farincikin Rayuwarsa harda cigabansa,yanajinta tazo da safe tana bugamai kofa yayi banza da ita,yanzu ko sha’awar kallon Ummi bayaso saboda yadda yaji lokaci daya Ummi taficemai daga rai duk da tana mtsayin mahaifiyarsa,Wuni yayi adaki ko fitowa baiyi ba,yana kwance babu ci babu sha,sallah kawai ke tadashi,itama din azaune yake yinta,cikin kwana daya kawai ya zabge ya rame kamar wanda ya shekara yana ciwo,ga saitin zuciyarsa dake zafi ga jirin dayake fama dashi saboda yunwa ammh bakinsa bazai iya koda saka kwaran abinci ba,saboda yadda ya yankema Rayuwarsa jindadinsa ya kare har abada tunda Ummi ta rabasa da Matarsa uwar ya’yansa,yana son kiran maiduguri yaji ko zahirah ta isa,ammh ina yakasa bakinciki da kunya sun kasa barinsa yakira,mai zaicema mahaifinta,bayan ya tozarta musu ya” ya sakota da tsohon dare ga kuma ciki,wanda yana kyautata zaton koda ta fita yakusa zuwa Duniya.

*

Lokacin da bukar yazo gaida baffa yaci karo da wani lbri mai tada hankali da bakinciki,haka ya zauna dirshan yana kallon zahirah da ya”yan data haifa idanunsa sunyi jawur,baitaba kawowa ransa haka zata iya faruwa ba,baitaba tsammanin rashin imanin mahaifiyar mu”azzam yakai haka ba,bai samu zarafin mgana ba saboda yadda tsausayi yaran,ya shigesa lokaci daya amaka saki uku,gata yarinya ga kuma rabon ya”ya innalillahi wa”inna Alaihirraju”u..”kawai yake nanatawa ficewa kawai yayi daga gidan,da kanshi yaje kasuwa yajido kaya nata dana yaran,harda su kayan tea duk abunda zata bukata yakawo,yanaji aransa wannan karon bazai bar kowa yamasa iko da diyarsa ba wacce yake matukar so,gida yakoma yace ma mahgana tagyara tsohon dakin zahirah zai dawo da ita gabansa ne,lokacin da magahna taji lbrin itama fashewa tayi da kuka tana tsinema Ummi.

 
Lokacin da bukar yakoma shida mahgana da niyyar daukan zahirah takoma gunsa tayi jegonta,daga yakura har shettima babu wanda ya musa,domin yanzu basu da iko kan zahirah in abaya shettima yayi iko da ita,yanzu kam Bukar yahau dokin zuciya zai bama yarsa kariya da kuma farinciki insha Allah,sunaji suna gani suka sakata a mota ita da ya”yan tare da rakiyan yakura suka tafi,shettima sai da ya zubar da kwallah,ammh duk da haka yana godema Allah,koba komai zuru”ar da”ake neman hadawa ta haduwa,haduwa ta har abada.

Lokacin da dangin Bukar suka samu lbrin sunso bore don akwai wa”inda sukayi damaran zuwa har abuja suci mutumcin Ummi wasu kuwa mu”azzam din suka ga laifi,wasu kuma shettima saboda sunce shine yaso kansa dayawa, yadauki yarinya ya bada, inda yasan cewa daman Tuni an tsaneshi to in ba zalunci ba meyasa yayi haka,babu yarda zasuyi illa hakuri domin bukar ya fadamusu cewa yarinya dai itace tasu kuma sunkarba,yara kuma suma nasune, saboda haka zasu cigaba da kulawa dasu duka indai itane basu so to har abada bai fata zahirah ta sake komama mu”azzam har abada.

Bayan kwana uku

Tuni aka cigaba da bama zahira da yaranta kulawa, kanwar babanta Ashe ,ita da yakura suke kula da ita,komai kuwa na bukatar rayuwa bahna dinta ya ijiyemata don dai duk yasata Farinciki,yara kuwa tuni rafara basu nono in tana kallonsu bata sanin sadda take fashewa da kuka,intana kallon macen yadda hatta yatsunta irin na Ummi ne,sai ta kamkameta tana kuka tana fadin”Wayyo Ummi da kinsan haka da baki aikata ba,Shi Allah ba”a mai dabara kalli cikin dakika tsana na haifo mai kama dake,wayyo ya mu”azzam kana ina nasani dakana nan Allah kadai yasan Farincikin dazakayi,ammh kamin Nisa,nisa na abada,..”haka zatayi ta fada tana kuka,wani lokaci aboye takeyi bata bari su yakura su sani kada sufadama bahna dinta ya shiga damuwa,ammh tabbas gangar jikinta ne ke maiduguri ammh zahirin batu Ruhinta da zuciyarta na Abuja tana son sanin wani hali ya mu’azzam ke ciki koma wani hali ne ta tabbata bamai dadi bane.


ABUJA

Yau kimanin kwana uku ko kofar daki Mu"azzam bai Fito ba,yana cikin daki duk ya zabge ya rame ya lalace,baya zuwa office,duk wani abu najin dadin rayuwa ya dakatar,ko wanka bayayi sallah ce tazama dole yakeyi itama azaune,yunwa kuwa takusa mai illah sai yaji kamar zai mutu ne sai yasha ruwa,ko yadan ci Fruit haka,yakoma ya kwanta saboda baya da karfin jiki,ga ciwon kai mai tsanani dayake fama dashi,ga jiri wanda shiyama fi damunsa,wayoyinsa kuwa har an gaji da kira baya dauka,kullum kwana yake kuka,kukan bakinciki da tunanin wani hali hiransa ke ciki,? ta haihu ko bata haihu ba? taje gida ko wani abu ya sameta a hanya? duk baya da wanda zai bashi wannan amsar.

Ummi kuwa kwana daya ta shareshi ita azatonta yana gama fushinsa zai fito ya warware ammh sai mai har aka kwana biyu ba mu”azzam ba dalilinsa ba ita kadai ba kaffa ma’aikatan sun shiga damuwa sosai,Ai ummi dakanta ta isa kofar dakin nasa tahau bugawa tana rokonsa ya bude ammh yaki budemata tayi magiyan duniyan ammh shuru kakeji,shiko yana jinta ammh bazai ma iya tashi bane har ya bude kuma shi yanzu yafiso,Ummi ta kyalesa yayi rayuwarsa shikadai Tunda burinta kenan kullum ta dinga nakasa mai Farincikinsa.

Ummi falo takoma tayi tagumi tana hawaye su karime na zaune gefe suma suna cikin halin damuwa,ita lami ko damuwa batayi ba illa fadin datake aranta”Komai yafaru ke kika jawo..”Karime ce ta kalli hajiya tace”Don Allah Hajiya kibar kukanan hakanan kada kema wani ciwo yakamaki..”share majina tayi tana fadin”Dole nayi kuka karime Mutum mai rai ya kwana uku bai sa komai bakinsa ba,ina lafiya kuma wlh nafikowa sanin halin son zai azbtar da kansa da yunwa ne hartazo ta mai illah..”tafada tana share kwallah

Shuru sukamata suna mamakinta kin janyo abu kuma kizo kina kuka,Allah yakara sukayita mata aransu,damuwarsu daya rashin sanin halin da yallabai yake ciki, ammh da ba don haka ba,wlh ko damuwa da ita baza suyi ba,tunda ita batasan Farincikin dan ta ba.

Ranar da”aka kwana hudu Ummi na kuka tana rokon mu”azzam ya bude ammh,yaki budewa,tayi magiyan hartagaji ammh tarinsa bataji ba,sai jikinta yafarawa tafara zargin tabbas babu lafiya,dakinta ta ruga ta dauko wayanta ta kira shureim tana kuka tana fadin yazo ya taimaketa kada mu”azzam ya mutu ya barta, yana ma tambayanta lafiya takasa mai bayani dole ya yanke wayar yakoma yakira na mu”azzam nan kuma harta katse ba”a dauka,ba cikin rudewa ya Fito daga Asibitin ko gida baije ba,yakamo hanyar Abuja

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button