UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Yagana ko dariya take kasa kasa daga,gani abun nayimata dadi matuka,zahirah takara gyara tsayuwa tana fadin”wlh babu inda zani sai ka fadamin dalilinka na yankemin wannan danyen hukuncin alhalin kace ban maka komai ba..”Alhaji ya dago yana kallonta yadda ta kafeshi da ido tana kallonsa cikin zubar kwallah,ajiyar zuciya ya sauke kan yace.

‘” SABODA KE BA MATATA BACE YANZU..,YAU KIMANIN KWANA GOMA KENAN KINA CIKIN IDDARKI NE..

      Da wani rawan jiki da firgici,Zahirah ta dafe kirji lokaci daya Tace” Ina..Ci..Ki..n..Idda..Ta ku..ma.. me k..a..Ke…Nu..fi..”? tafada bakinta da muryanta na rawa lokaci daya hawaye na wankemata fuska,kallonta yayi kafin yayi wani mirmishin yake yace”Ma”ana na SAKEKI KWANA GOMA DA SUKA WUCE,SAKI DAYA..”

      Saboda razana zahirah batasan sadda ta aza duka gwiwoyinta akasa ba tana fadin”ka sakeni Alhaji,na shiga uku menayi maka..? tafada tana zubar kwallah daidai lokacin da moodu dake hannunta ya subuce ya fadi akasa yana kuka,guda yagana ta saki kafin tace”gaskiya wannan karon kayi abunda ya dace,kama saki tunkan asaka ka,kai gaskiya aiki yayi kyau..”take fada tana shekewa da dariya.

Da kallo Alhaji ya bita yana dan mirmishi domin azahirin gaskiya yafara dawowa hayyacinsa da taimakon Mahaifiyarsa data sanya akemai Saukan qur”ani da Sadaka,dauke idonsa yayi akanta yamaida kan zahirah wacce ke kuka wurjanjan dakyar ya iya bude baki yana fadin”Ki yi hakuri..”dagowa kanta zahirah tayi idanunta sunkada sunyi jawur tana so tayi mgana ammh bakinta yamata nauyi,kawai sai ta yunkura tatashi,ta dauki moodu dake tsandara kuka,itama Tuni little dake bayanta ta fara nata kukan,ta shige daki da gudu tana kuka,tana shiga daga ita har yaran suka zube bisa gado suna kuka,zahirah fadi take”Shikenan nakara zama bazawara akaro na biyu..”take fada ranta na kuna,tasani batason Alhaji ammh sanda ya furta ya saketa sai da komai nata ya tsaya cak,dama haka Abun yake duk takamar mace,da izzarta kalmar saki na matukar girgiza ya”ya mata.

Alhaji baima yagana mgana ba,ya tashi yabi bayan Zahirah da kallo yagana tabishi tana maijin dadi aranta lalle aikin boka yayi,tashi tayi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira kawarta zinatu,tana bata lbrin komai,itama ihu ta saka tana fadin”Dole sujema boka godiya domin aikinsa ba irin na sauran bane..”Sunata murna awaya,su azatonsu Asirinsu yaci Alhaji har ya saki zahirah basusan kwanan zencen ba.

Yana shigowa cikin daki zahirah tamike tana mai wani kallo,ajiyar zuciya ya sauke kafin yafara mgana”Zahirah ko alama ban sakeki don na bata miki ba””..To don ka maidani bazawara akaro na biyu ka aikata hakan…”Zahirah ta katseshi da cewa haka,Hannu ya daga mata kafin yace”Ba burina kenan ba zahirah,..”yafada yana juyamata baya kafin yacigaba da cewa”Nasani cewa koda na Aureki bawai don ina sonki bane,na aureki ne,domin kwadayin samun zuru”a daga gareki,kema kuma na san cewa ba sona kikeyi ba,biyayyah ce da kuma hakuri yasa kike zaune dani,na yanke shawaran Sakin ki ne saboda akwai wanda yafinin bukatarki wanda yake chan kwance cikin halin ciwo tunda ya rasaki,kema kuma nasani kullum cikin begenshi kike,domin gangar jikinki kawai ke tare dani ammh hakikanin gaskiya Ruhinki da zuciyarki tana tare dashi..”yafada cikin Raunin murya.

Daskarewa Zahirah tayi tana bin bayan Alhaji da kallo cikin mamaki da zubar hawaye tace”waya fa..da..Maka..”tafada tana rawar murya juyowa yayi yana fadin”kowaye ya fadamin ba sai kin ji ba,zaki rantse min da Allah cewa kullum baki cikin Tunani Tsohon mijinki kuma uban ya”yanki? zaki iya rantse cewa abunda na fada karya ne..”yafada yana kuramata ido.

Ja da baya zahirah tayi tana wani kuka,lokaci daya tana kamkame jiknta take fadin”a..a….”kiyi Shuru kawai Zahirah basai kince komai ba, narigaya dana yanke hukunci Nayi SADAUKARWA..,Zaki zauna anan gidan kici gaba da iddarki har zuwa jini uku,in inada rabon samun zuru”a Atsakani dake,zanyi murna da hakan,in kuma harkika gama jininki uku,ma”ana lokacin kingama iddarki zan maidake gaban iyayyanki,nayi musu godiya bisa hallarcin dasukayi min,kiyi Hakuri Zahirah nayi hakan ne,domin Farincikinki,farincikin kowa naki tare daFarincikin su Little Ummi,Allah yaga zuciyata,ammh inaji ajikina kila ban da rabon ganin kwai na aduniya ne…”yafada lokaci daya hawaye suna kwaranyomai kafin kawai yajuya yafice yana share kwallah.

Yana fita Zahirah takoma bisa gado tafada tana kuka,lokaci daya taja moodu da little ta rumgume tana fadin”Zamu koma gidan Abbanku,zamu koma gidan Abbanku..”take fada tana kuka da dariya lokaci daya hawaye suna zubomata,kamar ko yaran sun sani sai sukayi tsit,suna kallonta kawai,rumgume tayi kamkam tana dariya hade da kuka lokaci daya,Tarasa kukan me takeyi,na mutuwar aurenta ko na murnar ta hallarta ga mu”azzam,tama rasa wani yanayi take ciki,jikinta na rawa ta rarumi wayarta talalubo nombar mahgana tadokamata kira.

Lokacin mahgana na falo tare da bukar suna cin abinci kiran zahirah ya shigo ta daga tana fadin”Zahirah ce,maman yan biyu..”Tafada tana kallon bukar daidai lokacin data dauka,sallama tayi ammh sai zahirah ta katseta da cewa..”Mahgana Alhaji ya sakeni..”Tafada hawaye na ziraromata,saurin mikewa mahgana tayi,hannunta na dafe da kirji tace”Alhaji ya sakeki? mekikayimai Zahirah..? tafada hankalinta tashe goge kwallah zahirah tayi kan tace”Babu abunda nayinai mahgana,da kanshi ya sakeni,sai yau yake fadamin kwana na goma ina cikin idda..”

Dafe kai mahgana tayi tana sallallami,Bukar dake zaune ya mike yana fadin”Ita wa aka saka.?.’Mahgana ta yanke wayar tana fadi asanyaye”Zahirah…”Zaro ido Bukar yayi kafin yace”Shi Alhaji kabirun ya sakarmin ya’..”Yafada yana bayyanar da bacin ransa kai mahgana ta daga tana fadin”eh..,Tama ce yace yau kimanin kwana goma duk tana cikin iddarta ne..”Hulan kansa ya cire yana fadin”Innalillahi wa”inna Alaihirraju”un…”Yake fada yana share zufan dake ketomai,Mahgana ko dakinta takoma farinciki ya isheta tarasa wazata kira tafadamawa bata da nombar Ummi,kawai sai ta kira yagana.

Yagana na zaune tana bama shettima Abinci abaki kiran mahgana ya shigo wayarta hartaji tsoro ta dauka tana fadin”mahgana lafiya kuwa..? naga kira da daddare..? Mahgana na dariya tace”Albishirinki…”Tafada tana dariya,gyara zama yagana tayi tana fadin”Goro fari kal dashi mahgana,domin daga jin dariyarnan taki abun Farinciki ne ya samu..”Da hanzari mahgana tace”kwarai ma kuwa,yanzu zahirah takirani tana fadamin Alhaji dai ya saketa tun kwana goma da suka wuce..”zaro ido yagana tayi tana fadin’Kibari don Allah..”Dariya mahgana ta sakamata tana fadin”wlh Tallahi da gaske nake fada miki..”

Ai yagana batasan sadda ta saki guda ba,tana fadin”,Masha Allahu matarmu ta dawo..”take fada harda hawayen murna kashe wayar mahgana tayi aranta tana kara godema Allah dayaba Alhaji ikon sakin zahirah hankali kwance batare da an kaucema hanya ba.

Shettima dake zaune yabi yagana da kallo kafin yayi mgana ta rigashi da cewa”Allah yayi da rabon zama tsakanin masoyan guda biyu,mijin zahirah ne ya saketa,tun kwana goma dayawuce,kaga kenan ma yanzu haka tana cikin iddarta ne..”Tafada tana bayyanar da murnanta,Washe baki Shettima yayi yana fadin”Alhamdulillah..Allah yasa karshen wahalarsu kenan..”yafada yana jinjina kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button