UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Dr.Sultan Balarabene, Cikakke mazaunin Madina,aiki ne shima ya kawoshi Sudan din,yahadu Da Dr lubna wanda ya kasance abu daya suka karanta wato abunda yashafi zuciya kuma suna yawan aiki tare,Dr Sultan dogo ne fari,kyakyawan gaske mai dauke da manyan idanuwa da dogon hanci,kota ko”ina baida makusa,tun da Allah yasa ya dora idonsa kan Lubna yaji duk duniya ba wacce yake so irinta,tun yana boyewa har ya bayyanamata,ammh Lubna taki bashi dama,bawai don bata sonshi ba,sai don ita tsarinshi kwata kwata baimata ba,infact ma batason Auren balarabe.

   Lokacin daya ga yadda lubna ta rude kan halin da mu”azzam ke ciki yasa yafara dora ayyar tambaya akanta,ammh daya tambayeta meye alakanta dashi,sai tace mai cousin Dinta ne yazo daga Nageria,bata sani bafa karya kawai ta yankamai,ammh abunda yasa yaki yarda da ita ganin ko dan”uwata ko daya bai gani ba,kuma ga yanayin yadda mu”azzam ke tafiyar da ita,sai yafara tunanin wani abu dabam,duk bin diddiginsa lubna ta toshe hanyar da zai Fahimci bawata alaka tsakaninta da mutumin dako Sunanshi bata sani ba.


NAGERIA

    Shirye shirye ne keta gudana takowani bangare,mussaman Alhaji kabiru dayaketa rawan jiki,tuni yafara gyaran shashen da xahira zata zauna,wanda yadaga Hankalin yagana,wanda Tana tambayarsa dalilin gyara yafadamata amaryace zata tare..Bala”i????????Haka yagana tafada domin abun yazomata abazata,ada taso tayimai borine sai kuma tafasa,domin tana son taji wata mai karar kwanan ne take kokarin keta mata gona.

   Lokacin dayake fadamata an Daura aure tarewane amaryan zatayi kadan yarage yagana bata Fadi Asume ba,bata kara tsinkewa da lamarin na Alhaji ba,sai da yake bata lbrin zahirah da dalilin dayasa yake kwadayin Aurenta,kutumar ubanchan inji yagana,wato Mai ya”ya ya auro ko? wato ita bibbiyu ma take haifa,lalle akwai babban tarzoma don wallahi ita bata haihu da Alhaji ba,to billahil azim babu maccen data isa ta haihu dashi,dukiyar Alhaji natane ita kadai,saboda haka koma wata mai karan kwanan ne,tazo itace zata zama ajalinta daga ita har ya”yan nata dayake murnan zuwansu,don taga in ba tafara aikasu lahira bane,Alhaji da uwarsa bazasu barta ta huta ba,..Topha.????


  Tabarayin Zahirah ko bata samu lbrin barin mu”azzam gida ba,sai daga bakin yakura fadar irin tashin hankali da damuwa da zahirah ta shiga bata lokaci ne,Mikewa tayi dafe da kirji little Ummi na kan jikinta ta saketa ba don yakura tayi saurin Riketa ba data fado kasa,hawaye kawai ke kwararamata tana maimata”Ya mu”azzam yatafi fa kikace yakura? yatafi ya bar ummi,wayyo ni zahirah duk adalilinKi Ummi komai ke Faruwa gashi yau babu mu”azzam tare dake,wlh Ina matukar Tsausayama kaina ammh wlh yakura Nafi Tsausayama Ummi matuka,ni nasan son Da Ummi takema ya mu”azzam Rasasa tamkar rasa wani shashe na rayuwarta ne..”.

   tafada bayan ta sulale kasa tana kuka yakura tasharbe hawaye tana jijjiga little Ummi datake kananun kuka,tace”Abun ba dadin ji zahirah,Wlh ance duk mai imani yaga halin da Suhaima ke ciki sai ya zubarmata da hawaye,ina amfanin muguwar gaba,wacce batada tushe ballatana makana,yau duk inda tayi hakuri, wlh da duk haka bata faru ba,an bata goma ko daya bata gyaru ba..”dagowa Zahirah tayi cikin hawaye tace”yanzu babu wandan yasan lbrin inda yake,baya da lafiya yakura inajin Tsoro,inajin tsoro kada wani abu ya sameshi,wlh ina sonshi bani son Rashashi gabadaya yakura..”Tafada tana dafe kanta dataji ya sara mata,lallashinta yakura tahauyi da cewa”hakuri zakiyi kinga ko mahaifinki baisan na fadamiki ba nakasa hakuri ne nafada miki ammh ko baffanki ai dalilin ciwonsa kenan,rashin sanin takamamman inda mu”azzam din yake,shikanshi abokin nasa yace ya bincika ko”ina ammh babu lbrinsa yaface yayi nisa da garin ne gabadaya.

  Dafe kumatu Zahirah tayi tana fadin”Hasbunallahu wani’imal wakil,Allah mun godemaka daga wannan Sai wannan”Tafada tana share kwallah kan tamika hannu ta amshi littae Ummi ta ciro nono tafara bata,tana kallonta yadda take tsotsonta da zafi zafi,alamar yunwa takeji Runtse ido,Zahirah tayi wasu hawaye suka zubomata ta furta cikin karayan zuciya”Allah ya bayyanaka ya mu”azzam,duk inda kake ka tuna dani da ya”yanka muna kewaraka bayan mutuwar sonka zai sama abincinmu son ganinka kuma zai zama abun Fata agaremu har karshen Rayuwarmu,Allah ya karemun kai ya mu”azzam aduk inda kake..”Tafada hawayenta na diga bisa Fuskar little Ummi,kamar wacce ko kamar tasan me uwar ke cewa,tasaki nono ta zuramata ido,ana haka sai moodu ya farka shida da kuka,Yakura ne tamiko mata shi tahadasu Ta rumgume tana kuka.

  Yakura dake tsaye tana kallon ikon Allah tace”Kibasu abincinsu,kibar kukanan zahirah..”idanunta na kulle tana hawaye tace”Ba Nono sukema Kuka ba yakura,suma sun ji ajikinsu sunyi maraici,maraicin uba nagartattace,basu da masaniyar samun wani makwafinsa suma suna kukan Rashin mahaifine,nikuma ina kuka RASHIN MASOYI NE..”Tafada cikin wani yanayi..

  Yakura dole tasakai tafice daga dakin saboda yadda tsausayin zahirah ya cikamata ciki,falo takoma suna mgana da mahghana akan tarewar zahirah jibi,wanda take fadamata irin dagan datakeyi da zahirah kan kin cin komai aka bata na gyara jiki,ko na jegon ma bayan tagama kin yi tayi,mahgana tace”Da an mtsamata sai tasaka kuka,wai wazatama gyara,babu ya mu”azzam dinta,ita wlh babu wanda zatama gyara..”Ki jimin yarinya to Ai hakuri zatayi da mu”azzam din yamata nisa,in ma zata saki jiko ta gyara toh,ta gyara don gidan kishiyata zata,wannan karon bata uwar miji bace,ta kishiyace.

  Hakuri kawai yakura ke bata,ko ita haushin ma mahgana taji,to miye nawani bata kayan gyara,Takaicima yahanata zama dole tayi mata sallama ko dakin zahirah bata koma ba, ta fice daga gidan Aranta tana jin kishin Auren nan,duk da saki uku ne,ammh tanajin babu dadi,ko don mu”azzam dayake mutuwar son yarinyar,ammh yazasuyi wannan karon basu da tacewa,don iya alkunya bukar yayi musu shi,wannan karan kuma kiri kiri yake nuna shi ke iko kan yarsa.

    Ana gobe tarewan sai ga dangin Alhaji kabirun wa”inda suka zo daga kano sunzo kawo kayan Akwatu,guda biyar shake da kayan arziki,ankarbesu hannu bibbiyu cikin mutumci da karramawa,sunci sunsha dakuma zasu tafi suka wuce da abun arziki niki niki,suka tafi suna fadin kabiru yagama sa”a duk da sun so ganin amaryan ammh zahirah ta rufe kofar dakinta,tana ciki tana rafzan kuka,tana auna yadda zata rayu dawani Namiji ba ya mu”azzam dinta ba, gaskiya da wuya ta iya yimai biyayyah tsakani har ga Allah, babu wani da Namijin dake burgeta kamar ya mu”azzam shine na farko kuma na karshe,so zata yarda da Auren ne,kawai don bahna dinta ammh har abada zuciyarta yana ga Shi din dai IBRAHIM MU”AZZAM.

Ashe Tun kwana biyu da suka wuce  inna Ashe da mahgana sukaje sukamata jere agidan Alhajin,wanda ko da sukaje yaganar batanan an tafi yawon bin bokaye ba zama,su kadai sukayi jerensu suna yaba tsarin gidan nata,suna fadin Nan ma zahirah tayi sa”a Ammh Allah yasa kada tafadama mtsalar kishiya bayan ta baro ta UWAR MIJI.

  Kaya sabbi Bukar yakara yima zahirah komai sabo,don ya nuna bajintarsa,Tabbas yana bala”in sonta komai ya samu wa ita yake karewa,babban burinsa yaga yawanke duk damuwar dake ranta,yazama tazauna cikinn Farinciki kamar yadda take ada,itako zahirah ko daya ba”a burgeta ba,kallon kowa kawai take,ita ta kanta kawai take da ya”yanta da kuma kwana sallar datakeyi na Allah ya tsare mata mijinta aduk inda yake,..Kiji karfin hali irin na zahirah,ga mijin ki chan,,Alhaji kabiru Nepa????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button