UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Da wuri ta kwanta saboda gobe school,shiyasa koda mu”azzam yadawo tuni ta dade da barci shiyasa bai tasheta ba shima ya shige shashensa yayi abunda zaiyi ya kwanta,itako Ummi rantane duk ba dadi shiyasa ko fitowa batayi ba.


Washegarima dai bata chanza zani ba ,da wuri ta shirya Shikanshi mu”azzam din yau fuskarsa babu Annuri gaisuwanta kawai ya amsa yace taje ta karya da hanzari,ganin yaki karyawa yasa ta kallesa taga yahade rai sai yajan tsaki yakeyi sai taji babu dadi shiyasa kadan tasha tea din Wainar kwan ne ma Karime ta sakama a food flulas,suka fice Ko amotar ko mgana bai mata ba, illa kawai tambayanta dayayi ya yanayin karatun tace mai Alhamdulillah,ganin shi cikin damuwa sai kawai taji ta damu sosai shiyasa suna kaita har haraban mkrantan bayan ta fito sai ta dan tsaya rike da murfin motan tana kallonsa,kallonta yayi yana fadin”Any problem..”Fuskarshi babu Annuri,gyara zaman jakarta tayi tana wani kwabe fuska tace”Don Allah yaya Mu”azzam kayi hakuri..”Tafada idonta na kansa,kur yayi mata da ido kafin ya murmusa yace”For what..’cike da yarinta tace’to naga kana ta fushi dani ko kallona baka san yi..”Baki ya rike cike da mamakinta yadda ta iya gane yana cikin damuwa,kallonta yayi kafin ya kada kai yana fadin”Ni bake kika batamin rai ba,kuma dawani idon kika ga ban kalleki ba.”Yafada yana leko fuskarta Dariya tayi tana rufe fuska shima mirmishin yayi yana fadin”Ngd tunda dai har andamu dani,kuma daga yau zanta kura miki ido tunda shi kike so,shikenan ko”rufe ido tayi da tafin hannunta tana dariya,hannu yadagamata yana fadin”Oya go to class gashi can an buga bell,take care sai na dawo ko”Kai ta gyada tana dagamai hannu bayan ta rufemai murfin mota tana tsaye agun har Motarsa ta fice daga haraban mkrantan.

  Ke….”Taji ance daga bayanta saurin juyowa tayi saboda yadda ta tsorata kawai sai taci karo da Asma”u ajiyar zuciya ta sauke tana fadin”Wai wlh kin tsorata ni..”Dariya Asma”u tayi tana riko hannunta tace”Am srry Besty na tsorata ki ko? tun dazu nake kallonki sanda aka kawoki kin tsaya kina mgana hala da mum dinki kuke magana? tafada tana kallonta.

   Mirmishi kawai zahirah tayi kafin tace”a’a Yayana ne…”tafada kanta tsaye domin bazata iya fadama Asma”u miye hadinta da ya mu”azzam ba daga haduwa jiya jiya,Asma”u tace”wow..Kina da broda ashe niko kinga Sister gareni yayata wacce nake bi,mu biyu kachal Mami da Abbi suka haifa..”Tafada tana yalwata fara”anta Allah sarki zahirah ta furta kawai,suna tafe zasu aji Asma”u na cigaba da bawa Zahirah tarihinta ko ajikinta kamar sun shekara tare.

  WACECE ASMA”U GADDAFI NURA

    Yace ga minister of Foreign Affairs(ministan huldar Najeria da kasashen waje) Alhaji Gaddafi Nura da Hajiya Umaimah,su biyu kadai iyayansu suka haifa aduniya ita da yayarta Hidaya,wacce ke aure alagos tana Auren wani Captain din Soja,su asalin iyayansu fulanin Yola ne zama ne dakuma arziki ya kirasu zuwa Abuja.

  Duk da sun kasance sun fito gidan Arziki hakan baisa tarbiyansu ta lalace ba suna da gata na hakika,domin duk burin iyayansu yana kansu ne kada ma Asma”un taji lbri,Asma”u yarinyace wacce ashekaru bazata wuce 19 ba ammh kana kallonta zaka ga tsantsan wayewa da ilimi,doguwace fara tas mai dauke da dogowar Fuska,tana da Faram faram da jama”a kuma akwaita da Saurin sabo,gata da Surutu,bata da girman kai balle nuna ko ita watace babu ruwanta kowa natane,tunjiya da”aka kawo Zahirah taji ta burgeta sosai hartaji tana so ta kulla kawance da ita.

Koda aka tashi break tare sukaci abinda Zahirah tazo musu dashi,bayan itama Asma”un tazo da Arish da kwai,Abunsu gwanin ban sha”awa,duk rashin sakin jikin zahirah sai da tasaki saboda Asma”u tayi bata da mtsala sam,gashi tana taimakonta ta bangaren karatu domin kaf ajin ba wanda yakamo kafarta akokari,ta ko”ina yarinyar ta hada komai,tuni,sauran yan class din suka fara jin haushin Zahirah na ganin daga zuwanta ta samu daman kawance da Yar gidan minister ammh su dasuke tare babu wanda ta taba bawa Fuska.

MAID

   Mutanen Maiduguri,tunda suka koma da lbrin dacen Da Zahirah tayi hankalin kowa ya kwanta ammh banda Na shettima da yakura,kullum garin Allah ya waye har duhu ya shiga basa cire ran ganin dawowar zahirah kullum cikin zullumi suke kamar ma, shettima yaji lbri,koda yake yana kokarin nuna komai ba komai bane,ammh yakura datake tare dashi tafi kowa sanin halinsa,shiyasa wani lokacin yakan bata tsausayi domin tako ina maraici ya lullubesa ga ba uwa ba uba,babu yan”uwa duka sun kwanta dama,ga babu wanda zaka kalla kace nakane ko zakaji sanyin aranka,tanaji ajikinta kila Shi shettima nashi sakayyar kenan da Allah ya hanasa haihuwa,ya nuna masa wanda dai suka tsana yanzu duk,duniya shine nasu kuma sanyin idaniyarsu.

Yakura kullum cikin yima zahirah addu”an zaman lafiya take da hakuri da juriya,duk da bayan auren sunyi mgana da Mu”azzam din sau biyu ta wayar bukar,koda ta tambayeshi zahirah sai yace tana gida,shikuma yana office,ammh ya tabbatar mata da cewa komai lafiya bawani mtsala,duk  da,hankalinta bai kwanta ba ammh kaso hamsin na damuwar tata yatafi,ita dai yanzu tabarma sarki Allah komai don taga damuwar ma ba magani bace.

Abagaren bukar kuwa,kewar na zahirah kadan ce ke taso mai,saboda shi yana nan albrin da mahgana ta fadamai,wani lokacin yaji kamar yakira mu”azzam yace yahadasa da Zahirah,in su Alee suka saka kukan ina yahna dinsu,ammh sai yaji yakasa amtsayinshi na mahaifi gareta hakan baida ce ba,shikuma mu”azzam duk sanda sukayi waya sai dai,yace tana gaishesu shi yana wajen aiki ne,baita ba cewa gata ba,shikuma bukar kunyace da Nauyi yahanasa mgana,ammh azahirin gaskiya yana bukatar Jin muryan yarsa ko hankalinsa zai kwanta.

  Akwanaki ma yan”uwansa suka kafamai tsiya wlh sai sunje Abuja sunga dakin zahirah tunda dai basu samu zuwa da biki ba,dakyar ya lallashesu cewa karsu damu shi da kanshi zai kaisu,su bari adan kwana biyu,harda mahgana amasu lallaban kada yabarsu sutafi,saboda tana gudun karsuje suga halin da ake ciki suxo sufadama dan”Uwansu su tadamai hankali yace ta munafuncesa,kuma ta sani Ummi wlh babu ruwanta Ubansu zata ci, in ma ta barsu sun kwanan mata a gida,Kenan.


After 1 week

Abuja

Yau kimanin Sati daya kenan da fara zuwan zahirah mkranta,ammh in ka ganta awannan kwanakin sai kayi mamaki,domin zahirah takara wayewa tafara fahimtar yanzu tana cikin garin Abuja ne,Haduwarta da Asma”u Gaddafi Nura Alheri ne gareta domin itace take kara koyamata wasu abubuwan na fanni mkranta,yanzu kawancesu yayi karfi domin tuni zahirah tasaki jiki da besty nata wacce ke matukar kaunarta don Allah,wanda saboda son datake mata har sai da Maminta hajiya Umaima tazo har mkrantan domin taga Zahirah wacce kullum Asma”u takoma gida lbrin kenan,Mami Besty ta kaza,besty ta kaza,soyayyahce wanda Allah ke hadawa,ba shakka Mami tayaba da natsuwar ta zahirah shiyasa hankalinta ya kwanta da kawancen nasu,rumgumeta tayi tana ta samata albarka bayan tayi musu fadan su maida hankali akaratunsu,zahirah taji wani farinciki,yakamata domin lokaci daya taji mami ta burgeta matuka,duk ita tataso bata son dadin mahaifiya ba,abun ya burgeta yadda taga Asma”u nama maminta shagwaba ita kuma tana biyemata,saboda tsausayin kanta har sai da hawaye suka zubomata ammh tayi saurin sharewa,Asma”u taganta shiyasa Mami na tafiya ta tsareta da tambayan meyasata kuka,sanin Halin Asma”u danaci yasa tace mata ta tuna da mamanta ne shiyasa,to sai anan ne Zahirah kefadama Asma”u mahaifiyarta ta rasu,ita din yar maiduguri ne,ammh tana zaune gun goggonta ne anan Abuja,haka kurum taji bazata iya fadan cewa aure ne yazo da ita nan ba,kozata bada lbri ba yanzu ba, saboda yadda takeda bala”in zurfin ciki bako da yaushe take sakin baki tana bawa Asma”u lbri ba,duk da har yau batasan cewa ita Asma”u diyar minister ce ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button