UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Itako Zahirah tana cikin tiolet ko”ina na jikinta na rawa tana jin Fitansu shine ta sababo ta fito ta dauki jakarta kenan takarajin motsin dawowar Ummi Shine takara rumtuma tiolet din aguje,tana jin sanda Ummi ta shigo tana bude buden wardrope,fitsari sai daya cikamata mata mara dataji,takunta akusa da bayin,kamkame jikinta tayi tana toshe bakinta da hannunta saboda kada kukan datake boyewa ya bayyana,cikin ikon Allah tafice bata duba bayin ba,ajiyar zuciya ta sauke kafin tahau share hawayenta.

Shiko Mu”azzam suna fita yasa ushe pakawa,sai da yadan bata lokaci kana ya fito daga motan yadawo gidan,sai da yaleka falon yaga ba Ummi kana yayi zuruf ya shige dakinshi,sauri sauri ya shiga ciki ya burma tiolet din wanda zahirah sai da taja baya ta zata ummi ce,sai taga mu”azzam,hannun ya sanya abakinshi yana fadin”Shiii…” da hannu ya yafitota ta kariso garesa yakamo hannunta suna tafiya suna sanda,kamar wasu marasa gaskiya sai da yaleko falo baiga Ummi ba,kuma ya duba samanta bata kana suka fito suna sanda,suna gabda ficewa ne sukaji takun Ummi tana kiran Uwani,ai daga mu”azzam din har zahirah a tamanin suka fice waje,basu tsaya ko”ina ba sai da suka danganta da waje,Allah yasa bakowa aharaban gidan harta sani,kila ya zagaya ne,da sunyi abun kunya.

Sai da suka shiga mota ushe yaja suka wuce kana suka kalli juna suna sakin ajiyar zuciya atare lokaci daya suna kuma kwashe da dariya harda tafawa,ushe dake gaba sai da yadan waiwayo yana mamakin oga da kansa harda kashewa,lalle duniya tama yallabai Dadi.

Kuyi hakuri da yadda kuke samu ba yawa,am mana haihuwa ne,ASMA”U M YUSUF( Janaf A2) ta sauka tasamu bby girl Halimatus sa”adiya(Ihsin bby)Muna bukatar addu”arku daga bakunan ku masu albarka

Comment
Share
Vote

#Intelligent writer”s#
#Uwar mijina..#
#JANAF FANS#❤❤
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

  *Alkalamin:JANAF*
  *Wattpad:Janafnancy*

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED

  *NO 20*

Har suka kai mkrantar su zahirah suna ta dariyan gudun da suka kwasa sai sun tuna sukara tintsire da dariya,mu”azzam yace”Ya”yan zamani kenan,tabbas ko taga yayan zamani wa”inda suka fita wayau da dubara.

Har cikin haraban mkrantar suka kaita kana Ushe yajuya da yallabai,kamar kullum Asma”u na kofar ajinsu tana jiranta Rumgume juna sukayi suna murnan ganin juna,wanda cikin kwanakin na Asma”u na mamakin kibar da zahirah ke mulkawa,ga haske datake karawa,sai ta danganta hakan,da hutune kawai tasamu da chajin manshafawa,ashe bata sani ba kawartata tajin abunda ita bata taba ji bane,ma”ana Da Namiji.

Tabbas Zahirah da mu”azzam sun zage sun Nuna ma Ummi in ita Uwar zamani ne to,suma ya”yan zamani ne masu amfani da kwakwalwarsu kansu wajen aikata abu,Tuni suke kife Ummi ta baibai Tunda dai tana takura musu da rana wani lokacin daga mkranta yake zuwa ya dauketa suwuce wani gidansa dake jabi wanda ko Ummi batasan da gidan ba,don bai dade da siyan gidan ba,suje sai la”asar kana ya maidota gida ya ijiyeta bakin get yakoma,su ushe suna ganin Abunda kefaruwa,suma dadi sukeji ganin yallabai cikin walwalarsa,wani lokacin kuma su karime ke musu gadin Ummi in ya shiga dakin Zahirah,kai ta ko”ina suna da masu lura da ita,tana cikin gidan suke kwana daki daya manne da juna ammh bata sani ba,kuma bata taba lura ba saboda da taku sukeyi,zahirah tuni itama mu”azzam yafara ciremata tsoron Ummi aranta,itama tasan hanyar layance ma Ummi sak wani lokacin Ummi na falo zata sababa ta shige dakin Mu”azzam duk bata lura ba,akwai kuma ranar data dako sammako ranar kuma zahirah adakin mu”azzam ta kwana jin shigowarta kawai sukayi lokacin zahirah na bakin madubi itada Mu”azzam sun fito wanka bayan sungama farantama juna rai,tana tsaye daga ita sai towel tana ma kansa cumbing suna hira sai shigowar Ummi sukaji aiko da hanzari Zahirah tashige cikin wardrope tana makyarkyata,Ummi data ga wulgawar mutum kamar amafarki tace ma mu”azzam waye taga kamar yayi wajen wardrope basarwa yayi yace mata shine fa,don babu kowa adakin data dage itafa taga kamar mutum ,mutum din kamar mace don taga bakin gashi bari ta duba tagani ganin da gaske take sai ta duba,kawai sai ya duke mata yana fadin wayyo cikinsa da rawan jiki tayo kansa tana masa sannu,to ranar da ciwo ya cecesa ammh fa zahirah ta zauni cikin wardrope din don sai da ummi tadade adakin na Mu”azzam kan takoma dakinta.

Aiko zahirah tasha dariya wajen mu”azzam sanda ta fito duk ta hada zufa,ita kanta dariyan take sunayi suna kyalkyatawa,suna hada jiki kamar wasu yara basu ma tunanin Ummi ta kara shigowa ta kamasu.

After 4 month

Abubuwa dadama sunfaru cikin wadannan watanin ciki harda Kamallah jarabawan su zahirah na Ss1 suka fada SS2,alokacin duk wanda yasan zahirah indan yaganta bazai taba shaidata ba saboda yadda tayi kiba ta cika sosai tazama mace shikanshi mu”azzam mamakin girmanta yake saboda sanin sadda aka kawota kamar kara,ba laifi yanzu takanyi waya da gida chan maiduguri ta wayar mu”azzam harta da baffa da yakura suna yawan mgana,kullum kuma yakura ta tambayeta game da zamansu da Ummi cewa take babu komai saboda mu”azzam bazata so ta karya alqawarin dake tsakaninsu ba,kuma ita bata da burin tadama iyayanta hankali,shiyasa kullum Zaman lafiya take shaida musu da alkahiri ya mu”azzam gareta,domin aboyen nan babu abunda baya mata baya tauyeta duk wani hakkinsa yana kokarin saukewa,Babu abunda zatacemai sai godiya tareda godema ma Allah daya mallakamata shi a matsayin miji gareta.

Game da Ummi kuwa,yanzu bata wani jin tsoronta kamar da don yanzu bama kasafai suke haduwa, ba don indai Ummi na falo bata fitowa sai ta tabbatar da batanan kana take fitowa,kuma itakanta Ummi bata nemanta sai dai in tsautsayi ya ratsa sun hadu to fa sai tasha zagi da dundu harda Rankwashi,shiyasa duk abunda zai hadasu bata yarda dashi,domin yanzu fa ba da bane,itama tafara sanin meye duniya,domin Kawarta Asma”u tuni ta koyamata karance karancen nan na novels din Hausa,da ta tambayi mu”azzam bai hanata ba da kanshi ya jido mata masu yawa tana ta karantawa,shike sa ajita shuru kamar batanan,kuma Alhamdulillah yana ganin riban karatun don yanzu zahirah ta rage jin kunyarsa zagewa take su tsotsi juna son ransu kamar wanda basa gajiya da,juna,kullum abu daya kamar cin kwan makauniya,bangaren kwalliya kuwa tuni ta kware awannan Fanni duk ta dalilin kawartata Asma”u domin ita da kanta zata zabo mata mayuka masu gyara jiki da Taushin fata ta kawo mata,shiyasa lokaci daya zahirah tafara amsa kanta ajerin classic bby,duk inda wata mace mai ji da kyau da kudi,da ilimi zata to itama zata jera dasu,kuma har yau din nan bata taba fadama Asma”u ita matar aure ce bace tace haryanzu lokaci baiyi ba.

Ta bangaren mu”azzam kuwa ya rigaya da yarda cewa yakamu da mtsanancin soyayyar zahirah wacce yake ji inbabu ita bazai taba iya rayuwa ba,ya shaku da ita har baisan sadda sonta yayi zurfi cikin ransa,kulawarta akansa da yadda take kokarin farantamai kadai ke kara masa sonta aranshi,ya rigaya daya bata amanar kanshi da zuciyarshi har yanaji aransa in babu ita to rayuwarsa tana cikin wani hali.

Ummi kuwa ita ganinta tana lura dakomai ta bake gaba ta bake baya,batasan cewa Mu”azzam na chan na mata barna ba,tana zaune bude da baki ita adole tana lura da komai kullum kuma cikin lissafin yaushe ne zahirah zata gama kaddararran karatun nata mu”azzam ya saketa ta kama gabanta,kullum ta tambayi mu”azzam bai wani bi takanta sai dai yace akwai sauran lokaci har yanzu,bata gama karatun ba,da zarar tagama bashi yace ba,to ,zai sallameta takara gaba,to dahaka fa yake linketa ta baibai tana hura hanci,ashe sun maidata sakarya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button