UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Hajiya baraka ita tatafi Da Suhaima gidanta da niyar riketa na har Abada Su Shettima bisa Umarnin kotu suka bisu sukaga mazauninsu..Hajiya baraka tana matukar tsausayin Suhaima shiyasa asatin dasuka dawo ta sanya mu”azzam mkranta inda Shureim yake zuwa tunda daman zasu zo tsara shima din yaro ne..Hazakarsa da kuma yadda yaron keda kaifin basira yasa aka ijiyesa primary 2 cikin ikon Allah kan kace kwabo mu”azzam yabama kowa mamaki domin Kan yahada shekara amkrantan kowa yasan dashi saboda yadda Allah yayi masa baiwa kwakwalwa.

    Lokacin Da mu”azzam yakammallah Primary shi Shureim yana jss3 ne shima kai tsaye yafada shashin yacigaba da karatu..Itakuwa Suhaima hankalinta ya kwanta tasamu natsuwar zuciya,Hajiya baraka ba yadda batayi da ita kan takoma mkranta ba ammh ina Suhaima tace ita ayanzu cigaban Rayuwar danta yafiye mata komai Saboda Haka Shidai yasamu ilimin ita nata mai Sauki ne jin Haka yasa takyaleta..Mu”azzam duk Sati Hajiya baraka ke shiryashi shida Shuraim tasaka direba yakaisu gidansu Shettima tun Sunakin kulasa suna banza dashi Saboda Abunda Suhaima tayi musu ammh yau da gobe har suka saki suka rumguma jikinsu duk Satin da baizo ba yakura da Shettima shiga damuwa suke sakamakom basu da ma wanda zasu gani Zuciyansu Ta sanyaya.

Lokacin Da Shureim yakammalla Secondary kai Tsaye hajiya baraka tasamamai gurbin karatu akasar Malesia yatafi inda zai karanta likita..Wanda tafiyansa ta raunana mu”azzam wanda duk duniya shuraim ne abokinsa kuma dan”uwansa ammmh yanayin karatu yau gashi sun Rabu wanda ada komai tare sukeyi,Hakan ne yasa mu”azzam yadawo so cool wanda ko ada Shureim din ne kesakasa .mgana Saboda dama chan ba mgananne bane.

   Shima mu”azzam din cikin lokaci yakammalla nasa wanda shima Hajiya barakan taso Turashi inda Dan”uwansa yatafi ammh mu”azzam yanuna irin karatunta yakeda sha”awa wannan lbri yama Hajiya baraka dadi matuka domin tama Shuraim sha”awar Karatun lauya ammh yanuna baya Ra”ayi dole ta Rabu dashi.

YANZU SALON LBRIN YAFARA..KADA KU GAJI KUDAI CIGABA DABIN JANAF..KOMAI ZAI WARWARE

Comment
Share
Vote

       AMULA BAE????
INTELLIGENT WRITERS ASSO????

???? UWAR MIJINAH..!????
        (Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)

       ALKALAMIN:JANAF????
        WATTPAD:JANAFNANCY

DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF

Failure is d apportunity to begin again more..INTELLIGENTLY.,Assalamu Alaikum janaf

HAPPY JUMMA”AT MUBARAK

FRIDAY 12/07/2019
6:00am

NOT EDITED

NO 5

   “”””Kai tsaye Tanema masa Addmission Alegal dake kano,bayan shekara  uku yakammallah karatunshi yadawo gida,bayan dawowarsa ya nemi Addmission a B .U .K Cikin sa”a suka bashi Direct  faculty of low old site yana kammallah karatunsa  na law ya wuce law sch yana gaf da kammallawane, aka aiko daga daga federal court Abuja na bukatar sabbin lauyoyi yara kanana masu jini ajika, da suke kammallah karatunsa awannan shekaran, don haka  suna kammallahwa akayi posting dinsu Sunan mu”azzam ne awanda aka tura domin ya samu kyakyawan Sakamako.

  Kafim faruwan Wannan Abubuwa da dama sunfaru ciki harda Rasuwar Fadi..Wacce ta rasu bayan ta haifi yarta mace ko ganin kalan yarinyar batayi ba Allah yadauki rayuwarta…Hakika Lokacin da lbrin mutuwar ya iske Suhaima jikinta yayi sanyi matuka ammh duk da haka hajiya baraka tayi tayi suje gaisuwa Suhaima tace atafau bazata ba..Domin ita ko sunan Fadi aka ambata ranta baya mata dadi..Lokacin mu”azzam yana Kano akayi Rasuwar sai da yadawo yaji lbrin shima ya girgiza duk da Fadi bawani mugun saninta yayi ba don acewarsa bata da fara”a..Shettima maraici ya lullubesa ba uwa ba uba..Kuma ba babu yan”uwa moodu yatafi ya barshi..Ga Fadi yau bata agidan duniya..Yayi kuka kamar ransa zai Fita babu mai rarrashinsa..Ahaka Bahgana yasama Yarinya Suna taci Sunan ZAHIIRAH wacce tataso cikin gata da tsausayi mai girma..saboda tazama baiwa ce daga Allah sai da uwarta ta shekara ashirin da biyar da Aure kana tahaifeta wanda har sun fidda rai ga haihuwa..,Sai gashi wanda tunda tasamu cikin bata kara lafiya har Ta haifeta kuma ta sanadin Allah yayimata Rasuwa..Yakura ita ta shayar da zaniirah hartakai shekara hudu Ahannunsu lokacin Da Abubakar bahgana yayi Aure da Halimatus Sadiya..Sai yanuna yana son karban Zaniirah tadawo gunsa saboda yadda yarinyar tashiga ran kowa..To babu yarda Shettima zaiyi yafi shi iko daita..Sunaji suna gani Zaniirah tabar hannunsu takoma hannun mahaifinta ya sanyata makaranta ammh tana zuwanmusu wekeed….

    Shekaranta Tara Aduniya Halima ta haihu yan biyu Wanda suka ci suna idris Da Aleyu..Tun Tasowar Zannirah aka Fahimci yarinyar dabam ce kwatakwata bata da hayaniya bata sa karkashi da dafarima sunzata sikila ce sai da aka kaita Asibiti suka tabbatar da cewa lafiyarta kalau..Kawai halitarta ce..sai Zaniirah ta wuni adaki ko mgana batayima kowa ko mgana kake mata in kaci Sa”a,ne zata maka mirmishi har hakoranta su bayyana,komai nata cikin Sanyi take gudanarwa Mahgana tana iya bakin kokarinta akan Zaniirah kamar yadda mahaifinta ke kokari akanta..Saboda girmamawan Bare bari yasa Suke kiranta YAHNA ma”ana Anty kenan..

**  ******   *****

Dr Shureim Wanda ke matsayin likitan akwakwal a babban Asibitin ABU Chika dake zaria..Shekaru takwas ya kwashe akasar malesia kafin yadawo gida Nageria..yana dawowa ba dadewa, yafara aiki da ABU Chika..Tafiya yake yana Dawowa weeked lokacin Mu”azzam na law school..Hajiya baraka tafara manyanta wacce Su mu”azzam ke kira Hajiyarmu,Suhaima wacce tazama babbar mace sosai takara wayewa,..Shekarar Da Mu”azzam yafara aiki da federal court..Shekarar farko ya gina  wani tamfatetsen gida A MAITAMA DISTRICT wanda yaji komai na alatun Rayuwa..Shima ashekaran Shureim ya tamfatsa nashi azaria cikin GRA..shekara na kara zagayowa suka daga dasu da iyayan nasu suka lula kasa mai tsarki…Suka sauke farali..Mu”azzam yaso yahada harda Baffa Shettima ammh tunawa dayayi wlh Sai dai Ummi tahakura da zuwan Saboda zencen wani dangin sa yanzu Ransa zai baci..Duk Hanasan datake bai gujesu ba yana zuwa inda suke wanda Suhaima bata da yarda ta iyane kawai.

  Mu”azzam baida aboki baida Amini face Shuraim wanda suka tashi tare sukayi wayau Tare…Mu”azzam Miskili ne nakarshe baya da haniya shima din ba magananne bane..Yana da zuciya ammh yana da hakuri, yana da riko da addini,,baya dawani aiki aduniya bayan Biyayyah ga Umminsa komai tace dashi yake aiko baya iya tsallake umarninta..mtsalanshi da ita danginshi shine ke damunsa domin ko taimaka musu zaiyi sai dai in aboye ammh Ummi bata da makiyi duk Duniya irin Shettima wanda yanzu Nadamar Duniya ta tsufa suka dabaibaye..Yayi nadama ammh baida halin gyarawa don kullum sukayi mu”azzam yazo yafadamai yafadama Mahaifiyarsa Ta yafemasa..Ko yakura dasukayi zaman mutumci Da Suhaima ta yanke alaqa da ita saboda matar Shettima ne ita…

  Lokaci Daya mu”azzam da Shureim sukayi shawaran daukan iyayansu zuwa inda suke aiki..Lokacin dayajema Sheettima Sallama yana fadamsa zai dauki Ummi sukoma Abuja da zama saboda ragema kansa zirga zirga na wahalan hanya..Haka Shettima ke kuka ya rumgume Mu”azzam yana fadin kada yabari mahaifiyarshi ta rabasu kada ya gujesa shikadai yake gani yaji dadi..Shikanshi moodun Sai da ya zubar da kwallah Saboda tsausayinsu haka ya jibge musu kayan Abinci da kudi kana yatafi..Wanda yakura sai da tafadama Shettima Tana Fadin” Wannan Ranar take jiyemaka Shettima gashi tazo maka..Babu kuma wanda zai iya magance maka ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button