UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

……….koda ganin su karime tsattsaye yason za”a Rina Dama..sannu da dawowa gabadayansu suka durkusa suna mai Da hannu ya amsa kafin yawuce yafara Haura step din cikin Kuzari da jarumta, Asaman dakuna uku ne ajere na tsakiyan ya tsaya ya sanya hannu yana kwankwasawa cikin karamar murya yake fadin”Ummi na..”Kira yake tareda kwankwasa ammh tayi mai biris domin yasan tanajinsa ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lafe jikin kofa yana Fadin cikin Raunin Murya”Plz Ummi na..Don Allah kimin aikin gafara,Nazo nafadamiki na tarar dake baki Tashi ba kuma banison katse miki barci am Sorry plz forgive me”Yafada yana hada Hannuwa kamar ya fashe da kuka yadade jikin kofa yana magiya sanin dayayi bazata bude ba yasa ya ja baya bayan ya sanya duka hannuwansa cikin aljuhu ya juyo yafara saukowa daga Step din kamar zai kifa saboda bacin Rai tsakiyar falon ya tsaya yana sakin Ajiyar zuciya karime tayi hanzari Nufar Fridge tadaukomai Ruwan Swan mai sanyi Ta tsiyayamai akofi Ta nufoshi dashi tana Fadin”Ranka ya dade sha Ruwa mai sanyi ko zuciyarka Zata sanyaya”Dago daradaran Idanunsa yayi ya sauke kanta kafin yadaga mata hannu kawai yace”Nagode..Kuje ku kwanta Allah tashemu lafiya”Ba yadda suka iya dole kowanne ya wuce makwancinsa zuciyarsa babu Dadi.

   Kan Daya daga cikin Kujeran  yakoma yazauna hannunsa dafe da kansa yanajin yana wani saramai…Yadade haka kafin yakoma ya jingina da cussion din kujeran yana sakin ajiyar zuciya,cikin kasan zuciyarsa yana jin kamar Wani al”amarune zai Faru matukar Ummi taji Abunda Baffa yazo mai Dashi..Yana nan kwance yana Tunane har barci barawo yadaukesa dayake sun tsaya bisa hanya sunyi sallah Sunci Abinci.
     

Toya kuka ga salon..Karfin gwiwanku shine zaisa na cigaba drop ur Comment in nagamsu sai kuga update

Comment
Share
Vote

#Intelligent writer’s#
#Janaf fans#
#HAFMEELART#
#Uwar mijina#
INTELLIGENT WRITERS ASSO

    ???? UWAR MIJINAH..????
          (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)

      ALKALAMIN:JANAF????
      WATTPAD:JANAFNANCY

Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF

Masha Allahu..Hakika jiya naga Ruwan masoya ta ko”ina..,naji dadi matuka sosai da sosai..Uwar mijina lbrin Shi mai fitar da amo ne,wanda nikaina yake mukurkusana..Ku himmatune wajen karatu da comment nikuma zan Himmatu wajen faranta muku,tanque dearest For u luv,support,and care..Assalamu Alaikum..Janaf????

NO.2

MEIDUGURI

    GRA

  “”””School Bus ce maidauke Da Sunan mkranta kamar Haka… IL”KALAMIK Wacce ke Barrat police barrak Daidai Shiga Maiduguri makaranta take..Motar mkaranta ta jido dalibai makil tana kai su gidajensu hakan ne Ya faru Da ZAHIIRAH wacce aka Sauketa a kofar makaken gidansu Dake GRA.

     Wata yar budurwa nagani Ta fito daga sch bus,din cikin Sanyi da Natsuwa dogowa ce sambal kallon farko zaku iya kiranta da one Saboda Rashin kibanta..Baka ce ammh ba chan ba tana dan Fadin Fuskar mai dauke da zanen Bare bare bibbiyu akumatun ta kanana Idanunta, bamasu girba bane sai Hancinta dayake dan matsakaici Lebenta, yanada dan Fadi da Tudu kadan wanda yake karamata kyau ashekaru bazata wuce 17 bakwai ba saboda a kallon Farko zaku iya hango tsantsan kuruciya tare Da ita ..Sanye take cikin Uniform dinta bayanta goye da sch bag dinta wacce kamar tana Rinjayanta saboda Nauyinta yan Sch din Suna dagamata Hannu itama cikin Sanyinta da alama halittarta ce take maida musu da martani har Suka bace ma ganinta… ZAHIIRAH ABUBARKAR BAHGANA kenan Yarinya diya ta dubu gun mahaifintaa yargatace ta karshe wacce duka bangarori biyu ke ji da ita duk da ta kasance MARAINIYA

    Cikin Natsuwa da Sanyi jiki ta tura get din Nasu tashiga kai tsaye kofar da zata sadata da falon Ta nufi tana doka sallamanta cikin karamar muryanta Tana Shiga Falon yan kanneta Idris Da Aleeyu wanda suke cema Alee yan biyu Twice..Suka taso da gudunsu Suna Fadin”Oyoyo YAHNA lokaci daya suka fada jikinta wanda saura kiris sukadata tayi saurin Fadawa kan kujera tana rike dasu fuskarta na bayyana da Annuri har Saida kumatunta guda biyu suka lotsa dimple dinta suka bayyana..Wow..Na furta saboda ganin yadda Komai yadace da Fuskar Zahiirah.

  Halimatus Sadiya wacce Suke kira da(Mahgana) wato mama karama kenan ta fito daga kichin tana Dariya take fadin”Kayyah zaku karya Yahna din Naku ne kuma dama gata ga yadda take”Kamar takara zugasu suka hau kan jiknta suna kara tumurmusa da ihu Mahgana ta rike baki kan tace”Ke kuma ki tashi kada su halaka ki dama suna fama da karfi kamar dawakai”Tafada tana dan mirmishi itama Fuskarta dauke da zanen bare bare guda biyu a fuskarta..dakyar Zahiirah ta yakice Su Alee bayan Mahgana ta jasu da karfi dakyar suka barta taja jakarta tashige dakinta cikin sanyin ta kamar wata mara lafiya.

  Ko acire kayan nata ma cikin Rashin kuxari takeyi da sanyin jiki..Tana gama cirewa tafada Toilet din yin wanka chan ma haka ta bata dukkan lokacinta kuma kada kuce bada hanzari take ba A”A cikin kuzari take komai ammh Halittarce haka bata iya yin komai cikin hanzari mutane dadama suna mata kallon mai sikila ce saboda yadda take gudanar da Rayuwarta…Lokacin Data Fito taji muryan Abbanta.. (BAHNA) Yashigo gidan taji kiriniyan su Alee.

    Cikin sauri ta shirya cikin lifayanta wanda tayane dukkan jikinta zumudi take tagama shiryawa tafito kada ta iske Bahna yafita kuma yasan yamata alqawarin zuwa gidan Baffa Shettima..Duk Saurinta koda Tafito ta iske har sun kammallah cin Abinci Tana fitowa Mahgana ta sakamata ido tana Dariya kwabe fuska tayi kan ta karisa tana gaida mahaifin nata hannu ya mikata alaman Tazo cikin sanyinta takarisa kusa dashi Alee ya ijiye yadauketa cak yadora bisa cinyarahi yana Fadin”Uhmm Zahiirah Fadamin Me Bahna yayi kuma”Yafada yana shafa kanta kamar karamar yarinya.

   Durkuar dakai tayi cikin jin kunya duk ta saba Da Bahna dinta tun tana yarinya haka yake mata ko yanzu ma ba abunda ya sauya zani domin Shifahar yanzu kallon Yarinya yake mata..Mahgana ce tace'”kaine da Laifi mana kamanta yau da Safe kanka Fita kamata alqawari kaida kanka zaka kaita gidan Baffa Shettima”Jin haka yasa ya rike baki yana kallonta kan yace yana mikar da ita tsaye”Afuwan Yahna..Muje ai na manta yau da gobe harda jibi ba”a bukatarmu gidan Baffa ake so ko?”Yafada yana gyara babban Rigansa dake jikinsa ita tana gefe mirmishi kawai take saki tunda tadawo gidan kalma ko Daya ba wanda yaji abakinta sai Da mirmishi kawai kuma ba wanda yadamu saboda Sanin Halin zahiirah na Rashin mgana wanda da fari har Taimako anfara Neman mata ana zaton Aljanu sun Shafeta ammh sai aka Fahimci haka Allah yayi ta.

    Ganin Haka yasa Su Alee suka saka kukan Sai sunje ba musu Ya sunkuce Alee itakuma ta dauki Idris sukama mahgana sallama suka Fice kai tsaye motarsa kirar matrix ya nufa ya bude ma Zahiirah gidan gaba tashiga kan ya zagaya yashiga mazaunin Direba yazauna Alee na kan cinyarsa ya tada motar suka fice daga gidan.

   Afamafari suka yada zango kofar wani dan madaidaicin gida mai kyau Da tsari Tunkan Bahna yagama paka motar Zahiirah tafice da gudu tabar Idris wanda zafin Fitan datayi yasa ya fashe dakuka Girgiza kai kawai Bahna yayi yana sakin mirmiahi lokaci daya domin inda Sabo yaci ya saba Da zahiirah kullum tazo gidan Baffa to haka take yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button