UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

****  *****  ******  *****

  MAID

  Achan kuwa Tuni duk wani Shirye shirye ya kamkama Zahirah batasan komai ba itadai Bahna dinta yace ta tattaro kayanta zata koma gun yakura da zama murna kamar zai kasheta jiki na rawa ta hada ya dauketa yakaita gun yakura.itakuwa batare da tsayawa wasa ba ta shiga gyara yarta tata Zahirah yarinyace,shiyasa bata fahimci komai ba,ammh abun yana bata mamaki komai aka bata tasha wanka ma bada ruwan banza take ba hakama tsarki..Turaren tsugunno ko har tagaji dashi kuma Abunda yafi dauremata kai tadaina zuwa mkranta data tambayi baffa sai cemata yayi “Kada tadamu xata koma mkranta ammh ba anan garin ba”To miskilancinta yahanata kara magana..Uwa uba ga Nasihohin da yakura kullum dare take doramata kan tayi hakuri da duk Rayuwar data tsinci kanta karta bari a fahimci Rauninta, zahirah yarinyace miskila wacce mgana ba damunta yayi ko ta tambayi yakura amsa daya take bata”Mtsayinki ne zai karu yahna”daganan bata kara cemata komai Itakuma bakinta na mata Nauyin kara tambaya.

  Ayayinda biki yarage Saura one week duk wanda ya kamata yaji sai yaji don Bukar ya shiryama Abun gayyah yayi sosai shida mahgana Wanda mutane dadama Sunyi mamakin wai Mu”azzam dan Suhaima wanda ba”arabu ta dadi ba za”a kuma kulla auratayyah wasu dadama sun kasa gasgassta abun wasu kuma so suke suji yadda wannan al”amari zai Faru Shikuwa Shettima ya dole kunnensa Ruf burinsa kadai yake Muradin cikawa.

•°•°•°•°•°•°••°•°•°•

   “”””Kokarin daura tie yake lokacin da wayar ta shigo masa Sai da gabansa yafadi dayaga, sunan BUKAR MAID Ya fito baro baro..Gabansa ya fadi har sai da wayar ya yanke yarasa Abunyi kafin ya nemo mafita wayar ta sake daukan kuwa..Cikin mutuwan jiki ya daga kiran kokafin yayi mgana yaji muryan Baffa na kwarara sallama cikin mutuwan jiki ya amsa bayan ya gaisheshi.

  Baffa Shettima yace”Daman dalilin kira na karin Tuni ne Rana ita yau ne za”a daura Auren kada ka sha”afa don Allah kada kabani kunya dana”Yafada cikin karyewar murya Cikin daburcewa mu”azzam yace”Bazan baka kunya ba baffa ammh bazata tare ba ko? Saboda akwai shirye shiryen danake son gudanarwa”Bude bakin baffa sai cewa yayi “Kada kadamu da wannan Ai zahirah kanwarka ce..Babu abunda zaka wahalar da kanka ko dakin dakake kwana ka ijiyeta babu damuwa komai sai yazo daga baya..Ammh kamim alfarmar ana daura aure zaka taho da matarka nan”jikin Mu”azzam yadau rawa zufa tana yankomai yanaji baffa nata hello hello ammh kuma ya kasa mgana dakyar ya iya cewa”Shikenan Baffa Umarninka shine nawa…Allah ya kaimu’Yafada kamar zai saka ihu.

   MU”AZZAM….! yaji muryan Ummi takirasa daga baya cikin muryan fushi da tsantsan bacin rai, a firgice ya waigo yana kallon Ummi wacce ke tsaye kikam akofar dakin nasa Fuskarta babu Annuri tana Fitar huci cikinn Fushi da bacin Rai…Ai Tuni mu”azzam yaji kansa na juyawa jikinsa yahau rawa babu Tamtama Ummi tagama jin komai yau karyansa takare.
 

   Abunda baisani ba tun sanda yafara waya Ummi na tsaye awurin tagaji da jiransa yaxo suyi breakfast ne yasa ta biyo sawunsa hankalinsa yayi gabane shiyasa baiji karan bude kofarta ba dukkan Abunda yafada a kunnenta.

Takowa take cikin Fushi tana karisawa kusa dashi tace”Mu’azzam minaji kana fadi..Naji kana fadin in an daura aure matar bazata tare ba? kuma naji kana ambatan Baffa wani Baffan?'”Tafada cikin Tsawa tana zaremai ido jikinsa na rawa yaja baya yana Fadin”A”a Ummi tsaya kiji kada ki daga hankalinki don Allah”Tsareshi tayi ido wanda suka kada kafin tace”Zaka fadamin ko sai naci UBANKA YANZU ANAN”Tafada kamar zata dakesa.

Bai da Zabi illa zubewa dayayi agabanta yana fadin”Ki yafemin Ummi rashin gayaminkin dabanyi ba..Bani son Tashin hankalinki ne narasa mafita Ummi”Yafada kamar zaiyi kuka hannu tadagamai kafin tace”go to d point Mu”azzam wani Baffan kuma wata matar naji kana mgana akai”Tafada cikin Tsawa runtse ido yayi kafin yace”Zuwan danayi maiduguri baffa yakirani yana bani UMARNIN auren Diyar marigayiya Inna Fadi ta da rasu ta bar… ” TAS..”TAS…”TAS.. kakejin Karan tafika ta ko’ina haka Ummi ke zuba su bisa Fuskar mu”azzam Tana kuka take fadin

” IBRAHIM nizaka ci amana…Nizaka Tozarta to wlh baka isa ba, zoka Ficemin daga gida kaje bani bukatarka wlh na barma Shettima kai, daman Burinsa kenan..Zoka fice Ibrahim bani kaunar ganinka zo ka Ficemin..”

tafada cikin wani yanayi Kafin tajuya Tafara tafiya tana kuka jiri ne ya kwasheta kafin kace me ta zube kasa warwas kamar gawa cikin wani irin Rudewa Mu’azzam ya mike lokaci daya yana kwallah kara da fadin

   UMMI NA…”yafada cikin Sauti wanda,duk wanda ke gidan sai da yaji wannan Sautin.

hohoho..Anzo gunfa janaf fans…Akwai badakala mai ban mamaki da tsausayi da Nadama..Kubiyoni ni zan warware muku ZARE DA ABAWA

#TEAM ZAHIIRAH# Kutanadi Botiki na taran hawaye????

#TEAM MU”AZZAM# kuma ku Shirya shiga cikin kuncin rayuwa,garari tareda fadawa tarko mai wuyar fita????

#TEAM UMMI# Ku kuma ku daura damarar daukan Fansa,ba mutumci yasin no respect????

Comment
Share
Vote

#intelligent writer’s#
#Uwar mijina…!#
#Janaf#
#One love#
[18/08, 14:17] 80k: INTELLIGENT WRITERS ASSO????

???? UWAR MIJINAH..!????
        (Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)

       ALKALAMIN:JANAF????
        WATTPAD:JANAFNANCY

DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF

NOT EDITED

NO.8

    ”””””’Lami da Uwani Dake kichen suna kokarin hada breakfast sukaji wannan ihun tare da kiran Sunan Ummi,cikin Dimautuwa suka fito falo nan sukaci karo da karime itama ta rumtumo zata shigo kichin din hannunta dafe da kirji take fadin”Lami kunji abunda naji kuwa?’Tafada tana haki.

Lami bata samu zarafin mgana ba ,sai ga Sani maigadi da Falalu mai bawa fulawa ruwa da ushe suma sun Rumtomo zuwa falon Suna tambayan lafiya ihun me sukaji haka”Karime ta nuna Saman Hajiya tana fadin”Wlh bamu Sani ba ammh kamar daga bangaren Hajiya ne fa”Basu samu zarafin mgana ba suka ga Yallabai ya fito cikin tashin Hankalin hannunsa dauke da Ummi wacce ke halinn rai da Mutuwa.

Cikin sarsarfa yake saukowa yana Fadin”Bring d car plz”Yafada cikin tashin Hankali ganin haka yasa ushe rumtumawa waje ya bude motar yallabai wanda ya fito da ita 607 kirar Piogion ,su karime ko hannu suka daura akai suna fadin”Mun bani hajiya innalillahi wa”inna Alaihirraju”un”Haka suketa maimatawa har mu”azzam ya fice da sauri.

  Kokafin sufito tuni har yasakata a mota ushe yaja sani ya budemusu get sun fice cikin hanzari..Lami da karime jikinsa babu inda baya Rawa Uwani tace’Mun bani meyafaru da hajiya ne’tafada kamar zatayi kuka babu wanda ya iya cewa komai sai ma karisa da sukayi gun sani maigadi wanda ke zaune da falalu suma suna janjanta Abun haka sukayi tsaye tsuru tsuru babu mai iya cewa komai kuma sun kasa komawa sucigaba da aikin gabansu.

  Cikin Abunda baifi minti sha biyar ba suka bayyana acikin babban asibintin nan SPECIALIST HOSPITAL ABUJA Ushe ne yayi saurin fita ya rumtuma cikin asibitin yana kiran Nurses suma cikin rudewa suka dauko abun daukan mara lafiya suka biyoshi ammh kafin kace me har sunci karo da Mu”azzam ya dauko Ummi ahannunsa,cikin Tashin hankali yake kwalama Doctor kira..Dr Abduljabar ne ke kan Duty ranar kuma daman Asibitin nan asibitinsu nan suke da fayel tun bayan dawowarsu Abujan da azama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button