UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Yafada yana sharbe hawayensa,Ba Abbie ba hatta mu”azzam kuka yake ka shirban,lubna ma,kukan take mooh kuwa,shima ya dukar dakai yana sharan kwallah,haka mom wacce itafi kowa sanin yadda mijinta ke kwana cikin damuwa,jinjina kai Abbie yayi kafin yace”kaji dalilina da abunda ya faru,ina Suhaima?miya kawoka Sudan? kuma aka ganka cikin mayuwacin hali?

  Abbie yafada yana kallon Mu”azzam din,Dukar dakai mu”azzam yayi lokaci daya hawaye suka kwaranyomai Tsuramai ido lubna tayi takosa taji kadan daga lbrinsa dakyar ya bude baki yace”Sunana Ibrahim Mu”azzam,….Tiryan Tiryan yafara basu lbrin rayuwarsu tundaga farko har karshe bai boye musu komai ba,tundaga cikinsa har haihuwansa da yadda Ummi takai su shettima kotu da rayuwarsu agun hajiya baraka,da yadda rayuwa ta sauyamusu da komawarsu Abuja da hadin Auren da shettima yamai da rayuwarsa da zahirah da yadda Ummi ta datse Rayuwarsa ta hanyar rabasa da zahirah da kwaciyar dayayi a asibiti da barinsa gida zuwa yanzu dayake zaune agabansu sai daya fadamusu kafin ya karishe da cewa,”Hakika itakanta Ummi kullum cikin Tunatar dani take game dakai,tana fadamin cewa yakamata na nemeka,nine ban maida kai ga mganarta ba har zuwa yau danake mgana agabanka ammh itakanta Ummi bata manta dakai ba”

  Shuru falon yayi,tuni lubna ke rusa kuka,tun sanda Mu”azzam yafara bada lbrinsa,dama ita macece mai tsausayi ,mom share hawaye na tsausayin mu”azzam din,shiko mooh kusa dashi ya matso ya dafa kafadansa yana dan damkewa kadan kadan alamar lallashi,Abbie kuwa shuru yayi kamar ruwa yacisa kafin yace”Ashhh..Suhaima bata kyauta ba sam,ai ba”a rama cuta da cuta,da alheri ake ramawa,kuma tunda suka gane sunyi kuskure sun roketa gafara meyasa bata yafe musu ba,?Yanzu gashi duk yakin datayi daga karshe ita akazo aka cita da yaki,banji dadi ba sam,gashi ta sanyanka cikin mawuyacin halin wanda intasamu lbri Sai taji dama tunfarko bata aikata haka ba”

  Yafada cikin damuwa kafin ya dafa mu”azzam yana fadin”Bakomai Son,anytin will be alright,kayi hakuri kacire damuwa aranka ka rumgumi kaddaranka,kana tare da Abbankane bazai kara bari kayi kuka ba kaji ko’gyada maasa kai mu”azzam yayi yana sharen kwallah ajiyar zuciya Abbie ya sauke kan yace”Mooh take him to ur bedroom,yayi wanka ya chanxa kaya am make sure kabashi clipper ya aske wannan Sumar data rufe masa Fuska”yafada da sigar zolaya.

  Dan murmusawa mu”azzam yayi kafin ya mike riko hannunsa mooh yayi yana fadin”welcome bro..Naji dadin ganinka da haduwa dakai amtsayin dan”uwana,tunda nake nikadai nake rayuwa dagani sai wannan rigimammiyar yarinyar”yafada yana nuna lubna wanda ta makamai harara tana share hawaye.

Mirmishi mu”azzam yayi mai kayatarwa,yana kallon lubna wacce take kallonsa tana wani lumshe ido,dauke kai yayi yana kallon mooh kafin ya damke hannunsa yace”am hppy to bro..”yafada shima fuskarsa na nuna farincikin dayake ciki,hanunsu na sarke suka wuce zuwa shashen mooh din wanda Abbie da mom suka bisu da kallon sha”awa,itako lubna kallonsu take tanajin wani yanayi atare da ita.
 

  Suna zuwa dakin mooh bedroom ne mai dauke da tiolet,mooh din da kanshi yahadamai Ruwanka ya shiga yayi,yau ne rana ta farko daya yi wanka cikin natsuwa haryaji yaji dadin jikinsa yana fitowa mooh ya rigaya daya Fitomai da kayansa,riga da wando ne,black and white na kamfanin Armani,abun dariya mooh da kansa ya zaunar dashi gaban dressing mirror yajona clipper din ajikin wuta yana askema mu”azzam din gashin daya cikamai kai da Fuskarsa gabadaya mirmishi kawai mu”azzam keyi yana kallon mooh ta madubi yanaji wani bamgare daga damuwarsa ta ragu ko bakomai he met anoder Family,ya Family domin Abbie khamis yana madadin Abbansane.

  yana gamamai sai gashi ya fito ras dashi,kyansa da zatinsa tare haibansa kuka bayyana,sai dai yar ramar dayayi kawai na ciwo,kallon kansa yayi yana shafa kansa,Rabonsa da zama irin haka tun agida kafin Ummu tayi yanke duk wani jin dadinsa na rayuwa sai yau,Shima mooh din wanka yayi yasa irin kayan Mu”azzam din sai dai diffirent clour ne,hannunsu na cikin na juna suka sake fitowa falon suka iske mom na jera abinci bisa makeken Tebir din cin abinci mai kama da na villan gidan gwannati????

  Mom tabisu da kallo sha”awa aranta jin dadin ganin zaratan mazan masu kwarjini da tsari,sannu da aiki mu”azzam ya mata,ta amsa tana kallonsa tana washe baki alamar tana cikin Farinciki,Abbie ne shima ya fito ganinsu haka shima yasashi Farinciki sosai,Rumgumesu yayi dukkansu yana ma Allah godiya,yana dagowa yaci karo da lubna tana tsaye tana kallonsu cike da burgewa waremata hannu yayi yana fadin”oya come and join us Dota..” 

Da Sauri ta kariso ta gefen mooh ta tsaya bayan ta sanya hannu inda Abbie yadafa bayan mu”azzam,tana kuma kallon bayan mu”azzam din,sakin su Abbie yayi yana fadin”welcome to happy Family my Son..”yafada cikin murna mu”azzam yace”Tanque Abbie..Nagode ma Allah da yasa ina da rabon haduwa daku,haduwa da Family dina wanda sukamin nisa”jinjina kai Abbie yayi yana fadin”kadaina godemin Son iz my Duty so muje muci abinci ko?

yafada yana kallonsu kada kai sukayi suna mirmishi gaba yayi suna binsa abaya,lubna kuwa duk motsin Mu”azzam a idonta,kamar ya sani ya waiwayo karaf ko suka hada ido mirmishi ya sakarmata for d First time,sandarewa lubna tayi saboda yadda mirmishin ya daketa lokaci daya wucewa yayi yabarta itako dakyar ta karisa taja kujera ta zauna jikinta amace.

  Kowa nacin abinci ammh gabadaya attention din lubna naga Mu”azzam,wanda ko shi baima san wainar datake toyaba,bai wani ci abincin dayawa ba ya tashi,mooh yabisa suka koma falo suna hira,sai tamaida kunnanta kansu,tanaji yana fadama mooh shi lauya ne yana aiki a hight Supreme court Abuja,a inda shi mooh din kefadamai Shi Quantity Suver,yakaranta A jam’ar Malesia ayanzu haka yana aiki da gwannatin kasar sudan wajen shimfida kwalta,sunata dai hiransu mu”azzam ya saki jiki yana ba mooh lbrin yanayin aikinsu A Nigeria shima yana bashi nashi,ahaka Abbie yazo ya samesu wanda shima sama sama yaci abinci hankalinshi na gunsu tsakiyarsu ya zauna,shima aka shiga hiran dashi.

  Tagumi lubna ta buga tanajin yadda zuciyanta ke bugawa duk bayan kowani dakika matukar ta kalli mu”azzam,mom dake gefe ta kura mata ido tana mamakin meya same Lubna yau,ganin bata da wannan amsan ya sata ta mata banza taciga da cin abincinta.


NAGERIA

  Motar su Zahirah na tashi Ummi tayi Wuf ta fito,tana fitowa ba wanda ya ganta Waje ta fito ta iske ushe cikin mota batai wata wata ba,ta bude baya ta shiga tana fadin”Ushe mu koma Famfari..”jin mganarta kawai yayi asama kamar zaiyi mgana  sai dai ya fasa yaja motar suka Fice daga unguwar.

   Hon Suka zuba abakin makeken gidan da hanzari megadi yazo ya bude musu get motocin suka sulala ciki,Ashe ce kan gaban Fitowa tana sakin guda,itama mahgana ba”a barta abaya ba,tuni suka rikita gidan,chan wata yar yayan bukar ta fito da Turaren Wuta tana hurama Amarya wacce Yakura ta fito daga ita daga mota.

Gaba su Ashe sukayi suna sakin guda da tafi lokacin da suka nufi kofar da zata sadasu da babbar tagamemom falon Zahirah dake rike hannun yakura jitake kamar ana janta gudan ko da su Ashe suke kamar ta mutu takeji banda Tsiyayar hawaye bata komai cikin katon lifayan da aka nadeta dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button