UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ko mganar shan kayan gyara mahgana da Innarta Ashe ta hadata, aiko ta sameta tayita mata fada kamar ta daketa,takuma kasa ta tsare sai da cinye kazan da”aka yimata na jego wacce ba”ayi mata ba,sai Fefesun yan shilla,da Hadin gumba wacce ake sha da madara,halin na yan Maiduguri ne domin mahgana tayi su da kanta hakanan don babu yarda zahirah ta iya take sha tana kuka,tana gamawa aka kawo turaren tsugunnne,shima Ashe ta karbe yaran tana fadin”Maza tsugunna,ana nuna miki hanya kina wani kukan iskaci,yo Shi mu”azzam din dakikema kwakwa,bafa zaki koma gidansa ba yarinya tun wuri ki dainama kuka,don gidan Alhaji nan ne gidan zamanki na har abada,ke ko Zuciya baki dashi,uwarsa tasaka yayi miki sakin wulakanci,ammh don jaraba da sakarci kina nan kina kulafuncinsa,kina ta halaka kanshi da yaransa.”

  Tafada harda dungurin zahirah akai suko yaran da harara ta bisu tana dungurar dasu bisa gado tace”Ku koyi zama ku kadai don uwartaku gidan mijinta zata,taje itama tasamu ladan Aure,bawai a iya renonku zata kare ba,Shegun ya”ya masu kama da tsinanniyar kakarsu,ni yaya yakin mun ne,tuni nace ya kawo munsu na dinga dirkamusu madara Allah ke rayawa,ke kuma abarki kici amarcinki “
kona sati uku ne..

Zumbura baki Zahirah tana kuka tace”Ni.wlh bamai rabani da ya”yana,tunda bawani ya haifamin ba,kuma aure ai bance ina so ba,Takurani akayi,kuma wlh tallahi ni babu amarcin da zanci ba zan ci Amanar ya mu”azzam ba..”tafada tana rufzan kuka wiwi..

baki Ashe ta rike kan tayi shewa tace”Ayyiriri Ayyiriri nanaye..Ohni Aishatu yau naga duniya,yo kada Allah yasa kici amanarsa don ubanki,ke in bakici nashi ba yaci naki ai,ke Soyayyah ko?to Soyayyar taci kazan kazanta,sakarya kawai,kinji in kinje ki hanasa kanki,yako turmusheki ya amsa abunsa,tunda kudi ya biya,kuma karki zauna kiyi abunda yadace ni dake shege ka fasa..”Ashe tafadi haka kan Tafice tana masifa ita kadai,Itako zahirah tana tsuguuno kan kaskon Tana hawaye ita kadai,Su little Ummi ko sunyi tsit suna raba ido sukansu sunsan Ashe ba dama.


   Wanan Zuwan da Shettima yayi da shirin zuwa maiduguri yayi, kara zuwa duba jikin Baffa,dakuma duka yan biyu,domin shine makwafin ubansu,dole Ya kula dasu,hajiya najin haka tace itama zata tunda baxai kwana ba sai su dawo,Ummi dake zaune tana jinsu ta daga ido tana kallon hajiya.Wacce ta waigo ta kalleta kan tace”Suhaima ya akayi ne?tafada tana karisawa kusa da ita,dom yau kwana uku kenan Ummi batayi ma kowa mgana ba,ko mgana kake mata sai dai kallo tana tsiyayyan hawaye.

  muskutawa tayi tana fadin”Za..Zan..zani yaya…”Tafada murya na rawa..Shureim da Hajiya suka zaro ido suka ce”ina..? atare cikin mamaki,sadda kai tayi kan tace “inda zaku..”gyara tsayuwa hajiya tayi tana hamdala aranta kan tace” MAIDUGURI ZAMU FA..

Ummi tadago kanta hawaye suna gangarowa tace”eh cham zani nima yaya,na Sauke nima Nauyin dake kaina,ko abunda ya tsayamin shekara da Shekaru ya wucemun na huta nima…”Tafada tana mai Fashewa da kuka.

Comment,share and vote

Nice dai taku jamilaomar, ba Nagudu bace????ba kuma kuma jut bace,JANAF NIKE. 
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

Congratulation My Anty SIS NAJATEE..,4 ur completing ur Amarxing,special,adorable,fabulous,Fantastics and Educated Novel ZAB’IN RAINA…,Ina rokon Allah yayafemiki kurakuran dake ciki,mukuma yabamu ikon amfana da darussan dake ciki,Kisani ki kara sani UR’S KANWA Love u back and moon????✌

NOT EDITED????

            NO 31

   Tun da suka dau hanya Ummi ke rafzan kuka,tsakanin Hajiya da Shureim babu wanda yayi yunkurin lallashinta, domin ya chanchanta data kokan,Ushe ne ke tukasu yayinda Shureim ke muhallin gaba,sukuma hajiya da Ummi na gidan baya,gidan su karime kadai aka bari,bayan hajiya taja kunnansu duk da tasan cewa basu da wata mtsala.

    Dayake Sun taso da wuri wajejen la”asar suka isa maiduguri,Ummi dagowa tayi tana karema garin na maiduguri kallon rabonta da garin Shekaru ashirin da wani abu,duk da garin yadan chanzamata baisa takasa gane wasu wurareba,duk da ansamu chanje chanje dakuma cigaba daga gwamnatocin dasuka gabata.

   Tsayuwar motar kofar gidan Shettima shiyakara rikita Ummi,tacikin motan take karema gidan kallo,duk da gidan yasamu gyara,ba kamar yadda ta sanshi ba,bai hanata Tunawa da abubuwa dadama ba,ciki harda sanda mai taxi ya saukesu ita da moodu da khamis suna gaba tana binsu abaya lokaci daya tasanya hannu tana toshe bakinta saboda kukan daya tahomata kallonta hajiya tayi bayan tafito daga motar tace.

  “Ki Fito Suhaima,nasani zaki Tuna wasu abubuwan,ammh ya mutum zaiyi Rayuwar kenan dama,abunda yabaka dariya watarana shi zai saka kuka..”

  jin haka yasa Ummi yin karfin halin Fitowa tana gyara,Zaman vail din dake jikinta,Shureim dake tsaye yana jiransu shikanshi Ummi ta bashi Tsausayi matuka,ganin yadda Ummi ke bin gidan da kallo tana tsiyayyar hawaye yasa Hajiya zuwa takama hannuta kawai Ta nufi cikin gidan da ita,shiko Ushe umarni Shureim yabasa daya bude booth ya debo kayan abincinsa dake ciki ya shigo dasu.

Yakura tana kichen taji sallamar kamar ta hajiya baraka,Jug ne a hannunta ta diboma baffa ruwa zata bashi magani,ta fito tana fadin”Muryan wa nakeji kamar ta Hajiya bara…”kalamanta sun makalene sakamakom tozali datayi da Ummi wacce ke tsaye tana tsiyayyar hawaye,jug din dake hannun yakura ya subuce yafadi cikin mamaki da al”ajabi ta furta.

  “Su..hai..Ma..”Tafada cikin Rawan baki Da gudu Ummi tasaki hannun Hajiya ta ruga ta isa ga yakura tafada jikinta tana fadin”Nice yakura,kinganni ko,Don Allah ki yafeni Yakura,ba laifi na bane laifin Zuciyatace,dakuma shedan wanda yake tusamin akidar tsanarku wacce bata da tushe ballanta makana,ki yafeni don Allah”

  Yakura data ke ji kamar mafarki take da Sauri Ta rike Ummi tana fadin”Suhaima kece dakanki,kice kike fadin a yafemiki lalle Allah abun godiya..Allah mun gode maka Alhamdulillah..”Tafada hawaye suna zubomata kan takara rumgume Suhaimar suna kukan Tare.

   
Hajiya tace ganin koken nasu yaki karewa”To mu karisa daga ciki mana,kuka ai yakare,tunda Kin gane gaskiya kuma kinyi nadama..”yakura tace”Tabbas dama mu kullum Fatanmu da addu”anmu gareki kenan”Hannun Ummi taja tana cema su hajiya bismillanku,Shureim sannu da kokari.

  Suna shiga dakin Baffa na zaune bisa katifarsa wacce aka Shimfidamai Atsakar daki dayake jikin yafara sauki,yakan iyama zama a jinginamai da Filulluka,Da murna da Farinciki yakura ke fadin”Mallam tashi yau addu”arka ta cika ga Suhaima tazo gidanka yau”

  Tafada tana jawo Ummi zuwa gaban katifar, jin Abunda Yakura kefadane,yasa Baffa dan zaro ido bakinsa na rawa yake Furta’Su..hai..Ma..Ki yafemun don Allah,wlh hakiinki ke bibiyana haryanzu’ya kareshe hawaye suna bin kuncinsa.

   Ummi ta durkushe gaban Shettima tana fadin”a”a bakai zaka nemi yafiyata ba,nixan nema,yafi kuwa saunawa zaka roka baffa,kullum ciikin aikomin da sakon na yafemaka kakeyi,nikuma na hau dogin zuciya da turban shedan,wanda bai kai ni da komai ba Sai Nadama,Alhalin na manta Allah kadai ke tsara abu kuma yatafi ayyada yaso,Yau dai gani Durkushe agabanka ina mai neman Afuwarka,don Allah kayiman aikin gafara”Tafada tana fashewa da kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button