UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda Akayi bakwai yagana ta dawo bata lura da abunda yafaru ba,domin ta dawo hankalinta atashe domin kafin uwarta ta rasu ta fadama sauran yan”uwan yagana akwai takardun gidanta dana filinta hannun yagana,tobayan anyi bakwai babban wansu yatarasu yana umartan yagana data kawo wa”innan kaddarorin don sun shiga cikin na magada,hankalinta ya tashi ainun domin fa basu,ta saidasu tuni tayi yawon bin bokayeta dashi lokacin da zahirah zata tare,babban tashin hankalnta ina zata samo su,koda gwalagwalanta tuni ta saida su bata ijiye komai ba,sai tsiya da kayan asiri balle tadaga ta saida,da wannan Tashin hankali tadawo gida shiyasa batabi takan ma Alhaji ba koda yazomata da mganar raba kwana,kallonsa kawai tayi aranta tana ayyana yadda zata tursasa Alhaji ya siyamata gida da fili cikin kwana uku kachal,shiyasa tace mai yaje dakin amaryan yayi kwana ukunsa na al”ada ta amince kafin azo araba girki,jiki na rawa ya dinga mata godiya itako tarko ta dana mai,yabata kudi kuma tasaka ya saki shegiyar yarinyar dole,jira takeyi ta fita daga wannan hargitsin,domin bazata kashe kudi abanza ba.


Sudan

Duk wani shirye shirye na tahowarsu ya kamkama,domin Tuni visar su ta fito mu”azzam ko yaji sauki sosai domin kwana hudu yayi a asibiti ya dawo gida lubna na cigaba da kula dashi,ba laifi ya samu lafiya sai dai ramar dayayi sosai yayi baki kamar ba brr.Mu”azzam ba,yanzu babu kwanji babu ado ballatana kwalliya yamaida rayuwarsa babu wata kawa abun burgewa.

Ana gobe tahowarsu ya saka Abbie yakaisa,har gidan marayun da Umminsa tayi rayuwa,gidan ya chanza sosai ansamu cigaba ta fannoni da dama,Kuka wurjanjan mu”azzam yakeyi na tsausayin Ummanshi,lokaci daya yaji kewa tare da kosawa ya saka idanunsa ana Ummi,wlh tallahi yayi kewarta so ba adadi,Abbie ya basu kyautar kudi sosai har na miliyan biyar kafin su baro wajen duk da basu ganesa ba,domin an chanza masu kula da wajen,yana kyautata zaton kilama basa raye,shiko mu”azzam ya gudurta aransa yana komawa zai kawo Ummi tazo taga inda ta rayuwa,domin tunda ta fita gidan bata kara komawa ba.

Washegari jirgin karfe 10:00am na safe ya daga dasu mu”azzam da Abbie da mooh da mom,da lubna zuwa kasar Nageria suna fisrt class ne,ayayin da Mooh da mu”azzam ke zaune kusa da juna,Lubna suna gefe ita da mom,sai Abbie dake kujeran gabansu shi dawani bakin mutum dan Africa ne daga ganinshi,tunda jirgin yadaga yafara tafiya asararin samaniya abubuwa dama dama,suka shiga dawoma mu”azzam kamar yanzu suke faruwa,nan da nan jikinsa yafara rawa idanuwansa sun kala sunyi jawur jijiyoyin kansa sun mike,Da kallo Lubna tabishi ta girgizamai kai cikin tsausayawa,ita kadai ne ta lura da halin dayake ciki,saboda daman duk motsinshi na kantane,ko rayuwarta bata mata kaffa kaffa kamar yadda take da tashi,kauda kai yayi kafin yamaida kanshi ya jingina jikin kujera yana lumshe ido.

Godiya ta mussaman,gareku Janaf Novell Fans 1&2 tare da Uwar mijina Fans 1,2&3 hakika jiya naga soyayya wacce ta tsayamin rai ,bantaba tsammanin haka uwarmiji ,yasamu karbuwa awajen ku ba naga sharhi masu tsuma zuciya,akwai wa”inda sukayi sharhi tamkar suna rubutu Novel,godiyata agareku bazata fadu ba,ammh kusani cewa wlh tallahi ni Jamilajanafty ina mayen sonku har cikin raina,ina rokon Allah yabarni da ku,har karshen rayuwa,nagd ngd….Allah yabar zumunci Ameen

Comment,share and vote

     *Janaftyjamila*

UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

Shatu????Shatu????Shatu????,where are u? come Closer,cuz shafin gabadayansa mallakinki ne,kin chanchanta,kuma kinkai dukkan mtsayi,Karamcinki gareni maigirma ne,haka kirkinki gareni sai dai nace Masha Allah,ina matukar godiya da Allah yahadani dake amtsayin masoyiyata ta hakika,Na yaba kuma ngd,Allah ya iya miki Abunda kika gaza,Nagode da kulawanki gareni Rabbi ya saka miki da gidan Aljannah mafi Soyuwa FIRDAUSI????????

YASIN NAYI EDITING????

            NO 37

        “”Awa6 suka shafe asama kafin jirgin daya,kwasosu daga Sudan yayi dirar mikiya, dasu Ababban Filin jirgin na Abuja.

   Daganan Tashan Tasi suka dauka harzuwa maitama District,kofar gidan mu”azzam mai motar ya taka birki,da wani rin yanayi mu”azzam ya fito daga cikin motan yana bin gidansa da kallo,wanda ya barsa tsawon watannin Shidda da wani abu,idanunsa suka kawo kwallah yayi Saurin maidasu,Mooh shiya sallami mai tasin bayan ya sauke musu jakukkunansu,Abbie ne ya karisa ga get din yana kwankwasawa.

  Sani da Falalu sai Ushe dake zaune kan wani benci,sun tsuge da lbrai basu ma ji Buga kofar ba,sai da Abbie yasake bugawa kana sukaji da hanzari Sani ya mike ya isa ga get din ya bude bayan ya leko da kansa,ganin Abbie khamis tare da baki ya sashi washe baki yana fadin”Yallabai yanzu kuke tafe? yafada yana bude musu kofan sam bai lura da mu”azzam ba,don shine na karshen Shigowa bayan Abbie da mooh sai mom sai lubna sai shi na karshe.

  Cikin washe baki Abbie yace”wlh kuwa sani,yanzu muke tafe dani da iyalaina..”Cikin fara”a Sani yace”masha Allah,lalle hajiya zata ji dadin ganinku,sannunku da zuwa”Yafada yana kallonsu mom,Mu”azzam ko na bayan mooh ya labe Yana jin yadda jikinsa ke rawa kamar baitaba rayuwa agidan ba,kasa boye kansa yayi kawai sai ya fito daga bayan mooh din idonsa na kan sani dayake kokarin maida kofar ya rufe.

   Yana rufe get din ya waigo yana fadin”Sai ku…”Sauran mganar ta makalene sanda yayi arba da yallabai,cikin rawan jiki sani yaja baya bakinsa na rawa yake Nunashi yana fadin”ya…lla..bai..Ko ba shi bane.?.”Yafada cikin tamtama,mirmishi Mu”azzam ya sakarmai yana fadin”Nine Sani…Na dawo gida”Yafada kwalla tana ziraromai ai da wani gudu sani ya kwasa wajen su Ushe yana fadin”aradu kuzo kugani,ga yallabai chan yadawo aradun Allah kuzo ku gani..”yafada yana jan hannun Falalu ,banzan kallo suka bisa dashi kafin Falalu yace”wani yallaban,kai kawai gane ganenku na kauye kafara gani anan,to ta inama zaka ga yallabai..”Ganin sunki yarda ne yasa Sani kara cewa”Aradun Allah ba karya nakeyi ba kuzo ku gani,don su kuresa suka mike suka karisa wajen dasu Abbie ke tsatstsaye cikin mamaki suna kallon yadda mu”azzam ke kallon ma”aikatan gidansa yana hawaye.

    Suna zuwa sani ya dinga nuna musu mu”azzam yana fadin”Ku kallesa,kunga ni ko aradun Allah yallabai ne”Da kallo Ushe da falalu suka bi Mu”azzam kafin su isa kusa dashi Ushe ne yace”Oga…Na u..? yafada cikin mamaki,dariya Mu”azzam ya saki lokaci daya da kuka kawai ya rumgume Ushe yana fadin”oga na u.? yafada yana kwaikwayonsa.

  Cikin wani murna Ushe ya rumgume yallabai yana fadin”yes na our oga,i Swear na yallabai..”yafada yana dariya lokaci daya da kuka,ai da hanzari sani da falalu suka rufama Ushe baya suka rumgume yallabai suna kukan Farinciki,Abbie ya kalli mooh shima ya kalleshi kafin su saki mirmishi lokaci daya itako lubna gefe taja ta harde hannu akirji,tana kallon mu”azzam wani sonshi yana kara shiganta,ashe haka yake da kyakyawan mu”amala da ma”aikatan dasuke karkashinsa lalle dole suyi kewa kuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button