UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Itako Ummi ko aranta bata kawo wai in taga yarinyar da hijabi ta zargi wani abu ba,illa da sun hadu tayi tsaki tace”Munafuka irin uwarta..”In ba”ayi sa”a ba tasha rankwashi,ammh bata taba lura da yadda zahiran ta dawo ba hidimar gabanta kawai takeyi.

kwantashi tashi babu wuya awajen Allah gashi har cikin zahirah ya shiga wata na bakwai ajikinta babu wanda yasan dashi sai wa”inda suka san dashi dama,a mkranta kuwa ta dinga muku muku dashi kenan ko Asma”u bata taba lura ba saboda bazama takawo Tunanin hakan ba.

Ranar Friday suna cikin class bayan an tashi break Asma”u ne rike da wani littafi na Text messgs data gani ajakar zahirah tana dubawa zahirah na gefe tana rokonta tabata abunta rugawa Asma”u tayi tana fadin”report zan kai ki kina yarinyar ki dake kin san Siyan littafin text din soyayyah ko” tafada tana mata dariya ganin da gaske take zuwan zatayi sai Zahirah ta mike ta biyota da dan gudunta sai Asma”u tafara zagaya ajin,tana dariya,dan gudun da zahirah tayi sai taji ta gaji sai ta duka tana Numfashi dagowan nan da zatayi sai hijabinta ya daga cikinta ya bayyana awaje wanda gayanan har ya girma,Asma”u dake tsaye gabanta ta zaro ido lokaci daya ta dafe kirji tana nuna cikin Zahirah take fadi cikin Rawar murya”Me…ye…Wa.Nan..Besty..”Tafada tana matsowa ganin haka yasa zahirah tabi inda Asma”u ke nunawa taga cikinta waje sai tayi saurin jan hijabinta ta rufe jikinta na dan rawa.

Asma”u zata sake mgana zahirah ta rufe mata baki saboda an dawo break an ajinsu sun soma dawowa hannunta kawai takama suka fice daga ajin batare data mata mgana ba.

wayyo Allahna mura plz manage dis one oooo…Bani jindadin jikina ur pryers iz nedeed

1luv janaf fans,iya wuya muna tare????

Intelligent writer”s
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

      *Alkalamin:JANAF*
      *wattpad:Janafnancy*

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

Dedicated to Zumunta Novella,Taskar littafan Hausa,Janaf Novella,Uwar mijina Fans1,2 and 3,Beneficial Writers,Auren Fari fans,Aisha Alto Novel meeragee Fans club..Kuna da yawa gaskiya wanda baki bazai iya Furtawa,ba Ngd sosai da kaunarku gareni Allah yasaka da alheri

     *NO 22*

Tafiya sukayi har zuwa bayan wasu empty clasess,wanda sabbi ne ba”a fara karatu aciki ba.

Wani dan Dutse dake kafe ta bayan wajen Zahirah ta zauna kafin taja hannun Asma”u tazaauna kusa da ita,wacce tazama mutum mutum.

Kallonta tayi kafin ta sanya hannu ta dage hijabinta cikinta ya bayyana tasaka hannu tana shafawa,kafin tadago tana kallon Asma”u wacce ta sandare tana bin katon cikin Zahirah da kallo mamaki ya sandarar da ita.

“Wannan kike tambaya besty..”?Zahirah tafada tana kallonta kai tsaye Gyada kai Asma”u tayi don bakinta babu alamar zai bude balle tayi mgana,mirmishin Zahirah tayi mata kafin ta dauki Hannunta ta dora bisa cikin tana fadin”Ciki ne besty ciki na haihuwa..”Tafada tana saka idonta anata.

Zabura Asma’u tayi hannunta dafe da kirji tace”Ciki zahirah,wannan wani irin bala”i ne besty waya yi miki ciki besty wayeshi,?”Tafada ranta na kuna lokaci daya hawaye ya wanke mata ido.

Dariya zahirah tayi kan tace”Mijina ya mu”azzam shi yayi min ciki,besty cikina ba dan shege bane,dan Sunna ne wanda shedu suka taru suka daura shi..”Zuru Asma”u tamata da ido kafin tace ‘bangane mekike Nufi ba,wani ya mu”azzam,din? “Tafada cikin mamaki da al”ajabi,Riko hannunta Zahirah tayi ta sake zaunar da ita,kafin ta shiga bata lbrin tarihin rayuwarta daga farko har karshe harta gaban dake tsakaninmu Ummi da iyayyanta tafadamata,kafin ta gangaro zuwa rayuwarta da Ummi da yadda yanzu take boyon wannan cikin ta kareshe da cewa”Na damu besty Wlh inajin tsoron Ranar da Ummi zata ganni da cikin nan kila sai ta kusa kasheni..”Tafada hawaye na zuraro mata.

Asma”u dake kallon zahirah tana kuka ta sanya hannu ta sharemata hawaye,itama zahirah sai ta sanya hannu tana sharemata atare suka sakarma juna mirmishi,Kafin Asma”u tace”lalle besty Rayuwarku tana cikin hadari a lbrin nan ,na lura kaf Ummi bata da imani aranta,ina matukar tsausaya miki kin taso cikin maraici,gashi kinyi dacen miji ammh Uwar miji ita zata dakushe kwanciyar hankali..”tafada cikin damuwa Rausayar dakai Zahirah tayi kafin tace”Nima fargabana kenan besty wlh dashi nake kwana nake,tashi,in bata gani yanzu ba,zata gani agaba,don zan haihu kuma dole taji..”tagumi Asma”u ta xuba tana fadin”wannan matar anyi yar kutumar uba,yo ba”a yafiya takema Allah laifi ya yafemata,sai ita tadauki wani mummunar akidar riko,kai wlh Allah waddai halinta “tafada kafin ta cigaba da cewa”Ke karki wani daga hankalinki,mijinki na sonki,duk ranar data gani sai kimata bayanin danta ne yayi cikin,sai tayi abunda zatayi,shegiyar tsohuwa mara imani..”rije baki zahirah tayi tana fadin”kirufamin Asiri bani da kowa agarinan,In ummi takamani da duka sai na daina Numfashi xata rabu dani..”Tamke Fuska Asma”u tayi tana fadin’Kina da ni,Besty ko duk duniya zasu juya miki baya ni ina tare dake,so kicire duk wani tsoro aranki Abunda take gudun ya rigaya da yafaru,kuma hakan yayimin daidai,hakan ne kadai zaisa tagane ba”a ma Allah dabara.

Jinjina kai kawai zahirah keyi Asma”u na bata shawaran cire tsoron Ummi aranta,takuma yarda ta gamsu,sun dade awajen kafin su tashi sukoma class har an Fita period daya basu nan,kowannensu wajen zamansa yaje ya zauna suka maida hankali wajen Chemistry teacher nasu domin shi suka tarar cikin ajin.

Da Zahirah takoma gida tafadama Mu”azzam yadda sukayi da Asma”u ammh bata gayamai shawaran da ita Asma”un ta bata ba,shuru kawai yayi,shikanshi kan ya kulle yama rasa mafita,harga Allah baida kuzari da karfin gwiwan taran Ummi da wannan zencen gwara ya bari in ta haihu sai taga mai gabadayan lokacin bata da yarda zata yi dole ta rumgume kaddara.

Asma’u ma datakoma gida take lbartama Ummi abunda ke faruwa Mami ta rike baki cike da mamaki tana fadin”ba shakka sanda mukaje gaisheta naga kamar alamar ciki tare da ita,to ganin ba aure tayi ba,shiyasa na kauda wannan Tunanin Araina,ikon Rabbi dama haryanzu akwai masu mugum riko kamar na kafuran farko”Mami tafada tana mamakin hallayar Ummi kamar wacce bata da sani akan addininta.

Zahirah tabi shawaran Asma”u tadan rage tsoro aranta,ammh duk da haka tana taka tsan tsan da rayuwarta gudun Faruwan komai,Ummi kuwa ita ko aranta bata kawo hakan zai iya faruwa ba,shiyasa bata sanya ido ba balle tagano wani abu,hankalinta kwance jira kawai take lokaci yayi ya saketa takama gabanta don har abada batajin zata iya hada zuru”a da diyar Fadi ba.

Lokaci nata tafiya,ta hakan ne muke cinye lokacinmu bamu sani ba,Gashi,har cikin zahirah ya shiga watanshi tara yana gabda Da Fitowa duniya,cikin saida ya girma yayi kato dashi gashi ta kumbura sutum kafafunta batama iya tafiya,Allah yasa sungama qualifaying exams dinsu sunyi hutu sai shiga SS3 kenan suna gida bata zuwa ko”ina,kullum tana daki tana addu”ar Allah ya sauketa lafiya don taji ance ana mutuwa wajen haihuwa,gashi ya mu”azzam yahana Dr Abduljabar yayi mata scanning waishi baya so,dole aka dakata,sai dai yayi mata awo yabata magani.

Zahirah taso takira gida tafada halin datake ciki,koda Ta Allah ta kasance ammh mu”azzam yaki,yakuma gargadeta koda wasa kada takirasu tafada musu tana da ciki bayanzu bane lokacin jin nasu ba,Mu”azzam banda Shureim bai fadama kowa ba,shima din ko hajiya bai fadamawa gudun karta fasama Ummi zencen Abu ya kwabe ammh shikanshi yaga gangancin mu”azzam sanin wacece Ummi bazata taba yarda dashi ba,yanajin masa tsoron Ranar da Ummi zata fahimci ya yaudareta ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button