UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Dagowa tayi tana kallonsa ganin yadda yahade Fuska yasa ta tsorata sai ta fara kurban shayin tana cusa buredin ammh idanunta fa sunkawo kwallah,lura da hakan da yayi ne yace”Ki maida hawayenki,wlh kika bari suka zuba zan saba miiki”Jin haka yasa tayi saurin maidawa tana tura buredin abaki,shima fefersun kaza taci kadan bada yawa ba,kallonsa take tama marairaice Fuska,lura da hakan dayayi ne yasa yace”Kin koshi ne…”Saurin daga kai tayi mikewa yayi yana Fadin”ok..Daga haka ya wuce shashensa ko kara kallonta baiyi ba.

Da kallo ta bisa Aranta tana mamakinsa yadda lokaci yake rikidemata,ajiyar zuciya ta sauke tana kallon inda yatashi kamshin Turarensa take shaka tana jin wani sanyi Aranta,dakyar ta iya tashi ta karisa shashensu karime suka gaisa,tana zaune suna ta hiransu har bayan azahar kafin takoma dakinta itama tayi sallar,tana idarwa tabi lafiyan gado bata tashi ba sai bayan la”asar,wanka tayi da sallah kafin tafito zuwa falon,da Mu’azzam taci karo wanda ke kwance kawai bisa kujera idanunsa suna lumshe kamar mai barci,ganin haka yasa ta lallaba zata koma daki,kawai taji muryansa cikin sanyi yace”Come back..”Cak ta tsaya tana maida Numfashi ,tafiya tafarayi kafin ta kariso kusa dashi..,”Sit..”Kawai yacemata bai ko bude idanunsa ba,jikinta Asanyaye tazauna akasa tana sunkuyar da kanta,ta dade zaune kanzil bai cemata ba,tun tana kunya kunya harta saki jiki tana kallon wani idian film da Zee World ke nunawa,shiko duk motsinta yana kallonta haka kurum take bashi tsausayi,haka suka zauna babu mai ma wani mgana ita tana kallo shiko yana kwance abunshi,har sai da aka kira mangarib kafin ya fice zuwa massllaci,itama zahirah tashi tayi taje tayi sallah,tana idarwa ta dawo falon saboda taga yadda zata kaya afilm din,shiyasa tama manta da kashedin Ummi ta haye kujera tana kallo abunta tana mirmishi,sai da akayi Issha’i kana ya shigo,haka yazo ya sameta,lalle kallo yayi ma zahirah dadi,shima nan ya zauna tare da ita,system dinshi ya dauko yahau bincike aciki,itakuma tana kallonta,Sai da 9 tayi kana yace taje ta kwanta,dole ta mike ta mai sai da Safe ta wuce dakinta.

Ko a washagarima haka ta kasance Mu”azzam yana kula da Zahirah daidai gwargwado sai gashi cikin kwana biyu harta fara sakin jiki dashi,har suna dan Fira,duk da bamai Tsayi bace,Weekend din gabadaya bai Fita ko”ina ba,inba massllaci zashi ba,yana gida kuma suna tare Da Zahirah dan zaman dasuke tare,yasa ko bata Fito ba baijin dadi sai ya aika karime ta kiramai ita,tazo ta zauna koda bazai mata mgana ba,

       Yau din ta kasance lahadin karshen Sati,suna zaune Falo shi da zahirah wacce ke gefe kan kujera tana sanye da riga da sikat na wani material,shiko yana gefe kishingide kansa bisa cussion Ammh idanunsa alumshe,shi yabawa Zahirah daman kuramai ido tana wassafa kamaninsa Aranta,Ta shagala da kallonsa wanda har Ummi dake tsaye kanta bata Sani ba,sai da taji an zuba mata wani gigitattacen mari wanda Sai da ta Wutsinlo bisa kujera lokaci daya tana fashewa da kuka,Bata tsorata ba,sai da tadago ido ta zubasu kan Ummi wacce ke tsaye idanunta jawur tana huci,Mu’azzam yayi Saurin bude idanunsa yana kallon Ummi kafin ya mike yana fadin”Ummi yau…”Tas..Tas..Ta tsinkeshi da mari lafiyayyu har guda biyu,da hanzari ya dafe gun yana bin Ummi da kallo yadda take wani girgiza kamar wata mai aljanu sabon kamu.

Comment
Share
Vote

Janaf
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
   (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

          Alkalamin:JANAF
          wattpad:Janafnancy

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

NOT EDITED

                NO 12

        Cikin faduwan gaba da Firgici ya waigo yana fadin”Na”am Ummi na..”Yafada cikin nuna kulawa,kallonsa tayi fuskarta babu Annuri tace”Kazo ina son mgana dakai ne”jin haka  yasa,yafara takowa ya iso gareta Harda zai zauna bisa gefenta kan kujera sai wata zuciyar ta haneshi,kawai sai yanemi waje gefen zahirah dake sharban kuka ya zauna.

  Ummi tayi kasake tana kallonsu cikin takaichi tace”Kai miye haka? tafada tana hararansa dagowa Yayi yana fadin”Na”am me kika ce”Yafada kamar baiji metace ba

  Kallonsa tayi tana fadin”Taso daganan kafin na saba maka,yaushe ka chanza da har kafara zama kusa da wata bayan ni”Tafada da kakkausan murya Cikin mamaki Mu’azzam yakalli zahirah dake gefensa wacce Kanta ke sunkuye tana sharan hawaye duk da haka akwai tazara tsakaninsu.

Rausayar dakai yayi ya mike yana fadin”Am srry Ummi…”Yafada yana zama kusa da ita,kauda kai tayi tana wani cin mgani kafin tadago tana kallon Zahirah cikin wani dan lokaci tana nazarinta Aranta take fadin”Shegiya komai irin na uwarta ne,haka uwarta take Macijin sari ka noke”Tafada cikin ranta lokaci daya tana jan tsaki afili,mtsewww..wanda sai da Mu’azzam ya kalleta.

   Gyara zama tayi tace cikin kakkausan murya”Ke…”Tafada cikin tsawa Zahirah dake durkushe tadago da hanzari tana kallon Ummi lokaci daya kuma tayi hanzarin janye idonta saboda ganin yadda Ummi ke binta da kallon Tsana hawayen dake kokarin zubomata suka kwaranyo Ummi tace”Ke…Don Ubanki kinaji ina kiranki Shine don kin rainani kikayi banza dani”Tafada cikin bacin rai.

    Zahirah tadago cikin rawan murya tace”Na..”am..”Ckin tsoro da kuka harara Ummi ta sakarmata kan tace”So nake ki bude kunni dakyau kiji,nan gidan ba gidan Shettima bane balle na uwarki Fadi,nan gidan Suhaima ne wanda gudan jininta ya gina mata”Tafada cikin gadara,Mu’azz am dake gefe yana latsa wayar hannunsa saida zuciyarsa ta tsinke ta wutsiyar ido yake kallon yarinyar yarda take toshe bakinta ammh duk da hakan hawayenta sun kasa tsaya,lokaci daya yaji wani abu aransa koba komai bai dace ace jiya daga kawo yar mutane ba,Ummi ta tasata agaba.,bai gama tunani ba yaji Ummi na cewa.

“Abu nagaba kingan ni nan”Tafada tana nuna kanta gyada kai Zahirah tayi kafin Ummi tacigaba da cewa”Duk duniya banda makiyiya kamarki bar ganin kina mtsayin matar dana,don ni ban daukeshi aure ba”Tafada cikin halin ko inkula kafin tacigaba da cewa”Nasan an baki lbrina kuma kinsan Abunda Uwarki da Shettima suka hadu suka min,so no need na sake miki tuni,domin kinfi kowa sanin cewa sai kin girbi abunda suka Shuka,kafin nan dole namiki gargadi mai tsauri game da dana,ba ganin yana mijinki wlh billahil azim ko kallon arziki ban amince kimai ba,ke ko gaisuwa bance dole ba,bani bukatar ki rabi dana,bani bukatar kisan kammaninsa koda wasa na kamaki kina kallonsa ko kina mai mgana wlh sai na yanka ki”Tafada cikin tsawa lokaci daya tana zaro ido

  Ba Zahirah kadai ta tsorata ba, harda Mu’azzam wanda yadago da sauri yana kallon Ummi kan yace”Haba Ummi wann…!Kai..”Ummi ta katsesa da tsawa kan tace”Zan saba maka nayi magana dakai? tafada cikin Fushi rusunar dakai yayi yana fadin”Allah ya huci zuciyarki kiyi hakuri bazan kara ba”Wani kallo ta jefeshi dashi kafin ta juya takalli Zahirah wacce ke kuka harda shessheka tace.

  “Kinji ko baki ji ba”Tafada cikin mata tsawa da sauri Zahirah tagada kai wani tsawan Ummi ta dakamata kan tace”Don Uwarki baki da baki ne”Saurin bude baki Zahira tayi tana fadin”Na..J…..i..Cikin rawan murya da kuka Gyada kai Ummi tayi kafin tace”Na biyu ban lamunce kidinga giftamin afalo na ba,don na tsani naci karo da Fuskar munafukar uwarki ataki Fuskan,saboda haka kiyi nesa dani tunkafin wata zuciya ta debe ni na illataki”Tafada cikin nuna zata aikata,Abunda tace din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button