UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Jim Ummi tayi kafin tace”Ni nasan yadda za”ayi..”Tafada cikin karfin gwiwa,da Sauri Lubna ta waigo tana fadin”Tayaya Ummi? Hanyar ficewa Ummi tabi tana fadin”Gobe zamu maiduguri ni dake,kuma yazama Sirri ko mu”azzam kada kibari yaji,iya ni dake ne” gyadamata kai Lubna tayi ammh mamaki fal ranta mai yasa Ummi tace gobe zasu tafi maiduguri ko ta na hango wani nasara achan din ne..

  Bata da wannan amsan Sai dai tajira goben kawai taga koma menene Mafitar da Ummi ta neman musu.

Comment
Share
Vote

Jamilajanafty Aka Jamila mai kyau????????????
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

                  NO 40

    “”‘Da daddare Mu”azzam nadawowa Ummi ta rufeshi da fadan meyasa yana zaune ciwonsa ya tashi ammh yayi shuru yaki fada,yana jin hakan yasan dalili wani dirty look yayima Lubna domin yasan adalilinta Ummi tasan halin dayake ciki,Ummi tayi ta mai fada daga karshe ta fashamai da kuka ganin yadda take kukane yasa yayi Saurin isa kusa da ita ya rikota yana fadin

   “Plz Ummi nah Stop craying..In kina min kuka,tayaya kikeso na samu rahamar Ubangiji ranar gobe kiyama..”yafada yana sharemata hawaye lokaci daya yake fadin”Naji na yarda Lubna tazo ta dubani shikenan..'”Yafada yana matse hannunta.

  Dago kanta tayi idanunta na zubar da kwallah tasaka hannunsa dake rike danata tana sharewa hawyen idanunta na kallon idanunsa tace”Why son?meyasa zaka dauki wannan matakin,matakin kashe kanka,kana Tunanin in kamutu saboda zahirah zata jidadi aranta,ko kuwa ya”yanka in suka girma aka basu lbrin mahaifinsu ya kashe kansa saboda mahaifiyarsu kana tsammanin zasu yafemaka?kokuwa ni danake matsayin mahaifiyarka zan gafartama kaina in har ka mutu ta dalilin Tursasawata,kokuwa ita lubna zata dauwama cikin Farincikine indan, muka rasaka,to kagani ka taimakemu son katashi kada katafi ka barmu,ina bukatarka,ya”yanka na bukatar ita kanta Zahirah na bukatarka araye,matarkama tana bukatarka araye,akwai hakkoki dadama dasuke wuyanka suke bukatar ka saukesu..,Don Allah Son kadinga kula da kanka da lafiyanka ba don niba,kodon ya’yanka da matarka don Allah…”tafada tana hada hannuwanta alamar roko.

  Kawai Rumgume yayi yana fadin”Rasa zahirah ciwo ne yaki ci yaki cinyewa Ummi na,ammh wlh rasaki Numfashina ne zai dauke gabadaya..I love u so much Ammi na,”Yake fada yana kamkameta,itama kamkameshi take tana fadin”love u Too…My Son.”Lubna dake gefe sai da ta share kwallah Iya burgewa Mu”azzam da Ummi suna burgeta hartake ji aranta inama itama inta haihu ta samu da”n dazai mata so tare da tsananin biyayyah irin na Mu”azzam da Ummi.

  Dole Mu”azzam badan yaso ba ya kwanta Lubna ta dubasa ta rubuta magunguna da allurai Ummi tabawa Ushe yace wani babban phamarcy ya siyo,tayimai allurai har guda uku masu karfi,su suka taimakamai ya samu hutu sosai,tun da ya kama barci bai farka ba sai washegari da Safe koda ya tashi Ummi da lubna basu nan Karime ke fadamai Ummi tace Suntafi zaria su dawo,magungunar da zai sha da safe da rana duk lubna tabarmai Rubuce,yayi matukar mamaki yadda Tafiyan tatashi ba shiri kuma,ko albri Ummi batamai zencen ba,ganin bawani waje bane sabo,zaria ai gidane yasa ya share batun ya shiga tiolet yayi wanka yazo ya karya kana ya sha mgani Waya ya dauka yayi Taking Excuse wajen aiki,kafin mganin yafara mai aiki nan ya haye kan gado yaja blanket barci mai nauyi ya kwashesa mai cike da Natsuwa.


BAYAN SATI BIYU

   
    “”Zahirah ce zaune cikin dakinta ta zabga Tagumi tana jin Baruntun da little ita moodu suke mata adaki,domin yaran suna da karkaza da kama jiki har sunfara rarrafe,suna dafa abu su taka,kamar hadin baki,da little tayi abu sai moodu yayi,suna gasa da juna,yanzu haka sunacikin wata na takwas ne,sun ma kusa wata tara,daga gani zasuyi Saurin takawa saboda suna da karambani..

  Kallo daya zakamata ka fahimci ta rame,saboda yadda idanunta suka zurma sosai,Tunanin makomar rayuwarta take ammh haryanzu takasa samun mafita,Tuni ta fawwalama Allah dukan Lamarinta ta rumgumi Alhaji amtsayin miji,kamar yadda yagana ta raba musu kwana,hakan ta kasance yana kwana bibbiyu ako wani daki,duka duka ne,Sau biyu ne ranar girkinta ya zagayo Alhaji ya kwana adakinta,ammh yau tsawon kwana goma sha biyu baya shigowa dakinta ranar girkinta,baya cin abinta kuma baya mata mgana,boyewa ganinta ma yakeyi,ko sun hadu afalo sai yayi Saurin shigewa daki ya rufe kofa,ko Abinci tayimai inyadawo kafin ta fito daga daki ya saka Yagana takaimai daki,duk da ba son Alhaji takeyi ba Shariyarsa gareta tamata ciwo,ko Su moodo sai dai ya aiko a karbesu tun abu bai bata mamaki haryakoma yanzu yana bata,intace bata damu ba tayi karya domin har Damuwar ta bayyana afuskarta.

  Yau din ta kuduri niyyar mai mgana taji wani laifi ta aikatamai da zafi haka,kuma in Alissafinta daidai ne,yau din ita kedashi,bata wani tsaya bata lokaci ba,ta mike ta sungumi little Ummi dayan hannun ta riko moodu tana nishi saboda yaran ba laifi sunada girma,falo ta fita ta kwalama Zulai kira,bayan ta zo ta mikamata little tace ta goyamata ita zata goya moodu,zasu shiga kichen ne,amsa tayi ta goyamata ita kuma ta goya moodu suka fada kichen Tuwan Shinkafai tayimai miyar zogale,lokacin dasuka kammalla komai ake kiran sallar mangariba,Zulai tabarma Daukan Wammers din zuwa saman Diining,itakuma ta karbi Little ta shiga dasu daki zata yi musu wanka.

  Agurguje tayi musu wanka itama tayi,ko shirin nasu agurguje,tayi musu itama ta shirya cikin wata doguwar rigan da mu”azzam ya aikomata dashi,Sallah tayi kafin ta dauki little Ummi ta goya ta riko moodu ahannunta tafito daga dakin dukkansu suna baza kamshi cikin sha”awa..

   Abunda tagani ne afalon yasata jan burki ta tsaya,yagana ce Zaune gaban Alhaji sun baje abinci atsakiyar falon sunaci suna dariya Ranta yayi mummunar baci batasan sanda ta karisa cikin falon ba tana fadin”ammh Allah ya hana zalunci baiwar Allah,meye naki namin katsaladan ranar girki na,naga dai ni na girka abu na,ko ba”a jira ni nazo munci tare ba,ajira nazo nabawa mijina Tunda yau hakkina ne..”Tafada tana huci wanda nikaina bansan cewa haka Zahirah take Intayi Fushi ba.

    Dawani salon rainin wayau Yagana ta dago tana kallon zahirah kan tasaki wata siririyar dariya tace”Hmm su miji manya,yo ai mijin naki da kansa yakirani ya Umarceni dana zubamai abinci,kuma na tsaya kusa dashi harsai ya koshi,shiyakamata kima wannan tambayan bani ba hajiya..”Tafada da rainin wayau,tuni idanun zahirah suka kawo ruwa cikin bakin ciki ta juya kan Alhaji tana fadin”Alhaji menayi maka,baka cin abincina,kadaina kulani? baka shiga dakina?in wani laifi nayi maka bazaka iya samu na kafadamun na baka hakuri ba..”tafada hawaye suna kwaranyomata.

  Alhaji da jikinsa yayi Sanyi ya dago yana kallon zahirah yace”Ko daya Zahirah babu abunda kika tabamin na sabawa duk iya zama dake..”yafada yana kallonta cikin kuka zahirah tace”To menene,ban maka laifi ba,duk meya jawo wulakancin..?tafada tana ratseshi da ido,kallonta yayi kafin yace”Ki koma daki zan zo na sameki muyi  mgana..”yafada cikin kulawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button