UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Manage dis1 plz

            Jamilajanafty  
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

I DEDICATED DIS PAGE TO U..Aisha Idris,Aisha bello,Binta gombe,mrs Fahim,Asms”ul husna,Mrs zainah jega,Feenerh,Aysha Dkg,Rukayyah musa,khardeejerh,deejart,Baby mu”azu,mummy halil,Maman Useey,Oum Ahmed,Fatima garba,Fauziya S madaki,Umaima Aliyu,Rabi”atu Adamu,mommy Affan,maman islam,Bilqis,Andijat,Ameera,Amina musa,Hauwa”u S tudu,Wsllim Mu”azu,maman Sultan,Napeesa,Mmmn Emma,and preety..,Kuna da yawan da in nace zan ambaceku duka,to zan karar da page din nan ban kare ba,Ngd sosai da soyayyarku gareni,Ni janaf ina sonku santala santala????mazga mazga????ina mayen sonku lodi lodi????,kai dukkanku nace muku bhahoot bhahoot????????????✌

NOT EDITED????

              NO 38

       “”Zahirah kuwa taji matukar mamaki lokacin da Alhaji yazo yana fadamata,abunda yagana tace,ayadda taga bala”in matar ita azatonta ko lbri taji Alhaji ya kwana adakinta sai inda karfinta yakare,itadai Zahirah ta kasa yarda da Yagana kwata kwata,zuciyarta na fadamata ba alheri aran matar.

   Addu”a tayi ta watsar da batun aranta,shiko Alhaji ko ajikinsa sai ma kara”in diban gara dayaketayi ransa fes,yanzu Alhaji yazama jarababbe,ada baya saka kansa a jerin maza masu yawan bukata,ammh fara dandan zumar zahirah ya birkitashi sam,ko yanzu yagama saduwa da ita,to yanzu zaiji sabuwar sha”awarta shidai burinsa yajisa yana nutse cikin kogin nan mai yawan Ruwan Ni”ima acikinta,Abangaren zahirah kuwa abun na damunta ammh bata da yarda zatayi ko bata rai tayi Alhaji yadinga mata magiya kenan yana rokonta kamar zai mata kuka,abunda ke kashemata gwiwa kenan ta bashi kanta ko bataso ba,to abunda yake halas dinsa yatsaya yana rokonta,ai hakan bai kamata,amtsayinta ta mace wacce iyayanta suka bata tarbiya.

  Itako Yagana kawarta Zinatu ta bata shawaran kada ta saka Alhaji ya siyamata gida da fili,kudi kawai zata amsa ahannunsa suje wajen boka,akashe bakin kowa kawai basai ta biya wannan gidan da filin ba,Shawaran Zinatu yagana tabi ta,tambayi Alhaji kudi har dubu dari biyu,jikinsa na rawa ya dauko ya bata,domin baya isa musa ma yagana ko wuta tace yafada zai iya fadawa,Haka ko akayi suka famtsama malamai Suka sanya aka rufe bakin kowa,wanda tun daga ranar babu wanda ya kara tada wani mganar Fili da gida da mamarsu ta mutu ta barmusu an daure musu baki.


Yau din takama weeked ne,duk da Alhaji baicika fita ba,ammh yasamu kiran gaggawa dole yafice,duk da yanzu Zahirah tasamu saukinsa,domin Tunda yagana ta rufe bakin yan”uwanta hankalinta ya kwanta tana gida yanzu bakasafai take fita ba,inba wannan yar duniyar kawarta taba,in tazo suke fita tare,Alhaji kuma yau kwananta uku bai shigo dakinta ba,sai da su hadu daga nesa shima in yagana na wajen,ko motsi ba ya iyawa kamar wata uwarsa haka take tafiyar dashi,itako tskaninta da yagana gaisuwa,wanda bama kasafai suke haduba ba,indai Sun hadu to Zahirah zata gaisheta wani lokacin ta amsa wani lokaci tayimata banza,itako ajikinta an tsikari kakkausa,harkan gabanta take,sai kuma kula da ya”yanta.

    
   Tana daga cikin daki taji zulai na kwalamata kira tana fadin”Anty ki fito kinyi baki..”jin haka yasa ta fito da Sauri tana goye da moodu little na hannunta,Tana fitowa falon taci karo da Ummi da mahgana sai bakin Fuska wa”inda bata sani ba,cikin mamak ta rike baki tana fadin”La,Ummi..”Tafada tana isa gareta kafin Tamikamata little wanda Ummi ke mika hannu.

   
Cikin Fara”a take musu maraba bayan ta mikama Ummi,little takuma kwantoma mahgana Moodu dake bayanta,nan kan kujerun falon suka yada zango suna gaisawa,Zahirah ta umarci zulai data kawo musu ruwa,Ummi tsurama Jikokinta ido tayi tana ganin yadda suka kara girma da wayau,itako Lubna idonta nakan Zahirah tana karemata kallo,to ai wannan ta girmeta nesa ba kusa ba,kuma babu abunda zata nunamata domin tafita kyau da hasken Fata,Tafita moran jiki mai kyau,abu daya zahirah zata nunamata tsawo da cikar kirji dana kugu,itako zahirah tana kallon lubna taji gabanta yafadi kawai sai taji bata yarda da kallon datake mata ba,Basarwa zahirah tayi tana kallon Ummi wacce ke kusa da ita tana fadin”Ummi yaushe kuka zo..? Ummi ta dago tana kallonta da kulawa tana fadin”Dazu muka zo da safe,mun sameku lafiya..? lafiya kalau Ummi yasu hajiya naga banganta ba

  Ummi tace”Hajiya takoma zaria satin daya wuce,saboda aikwai baki agidan bani kadai bace kamar da..”yake zahirah tayi kafin ta sunkuyar dakai tace”Armm Ummi nace ya lbrin ya mu”azzam,anji lbrin inda yake? Kur Ummi tayimata da ido,kafin ta maida kallonta kan Lubna wacce take kallon duk motsin zahirah cikin wani yanayi wanda bazai wuce kishinta ba.

  mahgana ce ta yanke Shurun da cewa..”An samu lbrnsa yanzu ma haka tare dashi Ummi tazo..”Mahgana tafada tana kallon zahirah,dawani karfin Zahirah ta mike tana dafe kirji take fadin”da gaske mahgana yaya mu”azzam din yadawo? yana ina don Allah,tare kukazo nan gidan dashi? tafada lokaci daya hawaye na Wanke mata fuska,tashi Ummi tayi tamikama mom Moodu,little kuma ta mikama lubna kafin takoma gun zahirah tadafa kafadanta tana sharemata hawaye tace.

   ‘”Yadawo zahirah Sati biyu da suka wuce,ashe sudan ya tafi achan ya hadu da abokin abbansa kinga wannan ,ta nuna Mom tacigaba da fadin”Matar khamis ce,sai wachan ta nuna lubna tana fadin”yarsa ce,Suka tsincesa cikim mawuyacin hali,yazauna awajensu bayan ya samu lafiya suka dawo dashi gida,yanzu ma haka tare dashi muke,ammh yana chan gidan Abbanki,yanzu ma munzo tafiya dasu little Ummi ya gansu ne..”Ummi tafada tana kallon cikin kwayan idanunun zahirah.

   Kwallah suka kwaranyoma Zahirah tayima Ummi kuri tana kallonta kafin tace”Toh..Ummi,nima zan biku naje wajensa don Allah..”Tafada tana fadawa jikin Ummi tana hawaye,rumgumeta Ummi tayi tana buga bayanta,itama kwallah ta ziraromata,cikin dakewa mahgana tace”a”a bazai yuyu ba zahirah kina karkashin wani ne,ki yi zamanki,zan dawo miki da yaran bayan ya gansu”,Tafada cikin tsausayawa.

    Kuka Zahirah takara fashewa dashi tana fadin,”wayyo Ya mu”azzam dina,don Allah kubarni naje na gansa,wlh in ban gansa ba,zan iya mutuwa..”tsausayinta yakama Ummi takara rungumeta tana lallashinta itama tana kwallah,Lubna dake gefe taji Zuciyarta ta tsinke,ashe ba ya mu”azzam kadai ke dawainiya da soyayyar ba,hadda ita kanta zahirah tana gidan wani ammh bata daina begensa ba,lokaci daya taji tsausayinsu duka biyun yakamata,kwallah ta hau sharewa tana kallon yadda ta rumgume Ummi tana kuka mai taba ran mai sauraro.

mahgana ce tace”Hakuri zakiyi fa zahirah ki barma Allah komai,domin ke yanzu matar aure ce,shikanshi mu”azzam din yayi aure ga matarsa nan tare da ita muka zo..”Tafada tana nunamata lubna wacce ta dago tana kallon zahirah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button