UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   Tana fadawa tsakar gidan Ta hau kiran YAKURA da dan karfi wacce aka kira daya Yakura tayi hanzari Fitowa daga falon da gudu tana Fadin”Wani keji kamar yahna agidan nan”Bata gama rufe baki ba Zahiirah tafadamata aijiki cikin Tsananin Farinciki itama cikin murna takamata ta kamkame tana Fadin”Wayyo Yahna..Tundazu nake Tsimayanki naji Shuru”Tafada tana kara rumgumarta Ahaka Bahna yashi go ya samesu gyaran murya yayi musu yaga Abun nasu yaki karewa.

  Yakura tadago Da Zahiirah tana ma Bahna sannu da zuwa itako Zahiirah sai kara manne mata take tana kwabe fuskar gaisawa sukayi kafin Bahna yace”Yagana ina Baffa ne'”amsawa tayi da cewa”Yana ciki Bukar..”Da sallama yaashiga falon wanda yake zagaye da kujeru wani dan dattajo ne zaune kan daya daga cikin kujeran fuskarsa tacika da Farin gemu ammh kuma kallo daya zakamai ka fahimci cikakke barbareni babu sirki..Saurin Furfurane yayi ammh akallah bai wuce shekara 60 aduniya ba.

    Kusa dashi ya”isa Ya zauna akasa ya tankwashe kafa yana gaisheshi amsawa yayi cikin fara”a yana mika hannu alamar Su Alee su kariso karisawa sukayi ya daukesu yana shafa kawunansu..yakura da Zahiirah suka shigo zahiirah na makale da ita suna shigowa ta saketa ta isa ga Baffa tafada gefensa tana dariya karshen murnan Zahiirah kenan kaga Dariyanta Baffa shima cikin Murnan ya dafa kanta yana Fadin”Zahiiratah Allah ya Albarkaci Rayuwarki Duniya Da lahira”yakura ne Da Bahna ke amsawa Da Amin itakuwa mirmishi take saki kumatunta na lobawa alamar tana cikin Farinciki.

    Yakura tace”Maza tashi kije kichen kidau Abinci kici domin Nasan babu Abunda kikaci Tunbayan dawowarki daga mkaranta” Bahna yace”Ai kema kinsani bataci komai murnan ganinku yahanata cin Abinci”Mirmishi Baffa ya saki kafin yace yana Dafa kanta”Wannan kauna da Zahiirah take mana daga Allah ne…Maza hanzarta kije kici Abinci kizo nabaki lbari mai Dadi”dagowa tayi tana kallonsa kan tace”tsatsuniya  Baffa mai Dadi ko”Tafada da sigar Yarinta gyada mata kai yayi washe baki tayi ta mike da hanzari tashige ciki fuskarta na bayyana Tsantsan  Farincikin data cike.

  Gabadayansu Da kallo suka bita cikin so da kauna Da sha”awa kafin Baffa yakatsesu da gyaran murya gabadayansu suka maida Hankalinsu kanshi kallon Bahna yayi kafin yace”Kaji duk mganar da mukayi kwanaki da kai ko.?To yaron yazo jiya kuma na fadamai so nake ayi komai cikin lokaci”Yafada da son tabbatarwa gyada kawai bahna yayi kansa na kasa baffa yace”Bukar kaine mahaifin zahiirah na gaskiya..Kayi mgana matukar Abunda na yanke baimaka wlh zan janye dama kawai domin karfafan zumunci ne kuma don yaron yakara dawowa namu sosai”yafada fuskarsa tadanyi wani iri.

   Da sauri Bahna yace”Haba Baffa kaima mahaifin zahiirah ne Tunda wacce Tahaifeta kanwa take gareka..Har Abada komai ka yanke game da ita nidin mai bin Umarninkane…Allah ya sanya alheri”Cike Da murna Baffa ke amsawa Da Amin basu wani kara wani zance ba Bukar ya mike yayi musu sallama zai wuce Su Alee yadauka yafice Yakura nace mai yagaida mahgana.

.

   Yana Fita yakura tace”Haba shettima ashe baka bar batun ga ba..Zuwan da yaron nan yayi saida ta kafadamai”Tafada Ranta abace kallonta kawai yake baice komai ba kan tacigaba da cewa”Ashe Shettima baka Tsausayin marainiyar Allah zahiirah…Ka Manta yadda Hajiya Suhaima ta rikemu bata kaunar mu..Ko Danta ba”a son ranta yake rabarmu ba kuma sai kadauki zahiirah ka bashi.? ka ko san mezaka aikata.To wlh Gagarumin Tashin hankaline shettima kake shirin kullawa domin kafi kowa sanin komai sai dai kaba wani labari”Tafada wasu siraran Hawaye na zubomata tafice tana sharan kwallah tana Fadin”Kar kamanta Diyar FADI ne fa..Zahiirah jinin Kace Shettima..Kuma Na tabbata Suhaima tafi kowa tsanar ku”tafada tana ficewa.

  Baffa Shettima na zaune inda Yakura Ta barshi kansa na kasa na tsawon lokaci yana dagowa Abun mamaki hawaye ne ke zubowa bisa kuncinsa suna bin saman farin gemunsa…Kofa ya tsurama ido wasu lokuta achan baya suka hau dawomai Daki Daki kamar yanzu suke Faruwa.

    Topha..Meyake faruwa ne game Da wa”innan bayin Allah..Bukar,yakura.Hajiya suhaima,Barrister Mu”azzam,Baffa Shettima da zahiirah..Duk ku biyo yargidan Umar zan warware muku zare Da bawa..Lbarin UWAR MIJINA SALON SA DABAN NE..Janaf????

Don”t forget to
comment
Vote
Share

#Intelligent write’s#
#Uwar mijina..#
#HAFMEELART#
INTELLIGENT WRITERS ASSO

    ???? UWAR MIJINAH..????
          (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)

      ALKALAMIN:JANAF????
      WATTPAD:JANAFNANCY

Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF

NO.3

   WASU SHEKARU ACHAN BAYA

   “”” MUHAMMED MOODU Shine asalin sunan mahaifinsu,wanda Asalin iyayansu da kakaninsu yan Asalin haifaffun maidugurinne awani yanki da”ake cema USIFARI zama ne dakuma yaya da jikoki yasa suka koma cikin garin maiduguri da zama…cikakkun bare barine gaba da baya.

  
muhammed Moodu yakasance babban malami ne mai ilimi da addini wanda jama”a ke girmamawa,shiyasa kowa ke kiransa ZANNAH MOODU matar Aurensa Daya Ummu kursum wacce sukayi Auren Saurayi Da budurwa Ya”yansu uku aduniya kachal shettima ne babba sai Fadima( Fadi) kenan sai Auta Muhammed moodu wanda yaci sunan zannah.

     zannah moodu yakasance bayan malantansa yana kiwon Dabbobi kama daga shanu awakai farare da jajaye..,kaji zabbi kai komai fa yana kiwo,gidan Gona garesa na mussaman inda yake gudanar da kasuwancinsa,..Yakasance yanada almajirai daga garuruwa da dama yana karantarsu dasu..Cikin yayansa kaf babu wanda bai bawa ilimin addini ba daidai gwargwardo,Shettima baida Ra”ayin Karatun boko ko kadan shiyasa ya tsaya gana addinin Fadi kuma dama macece kuma zannah baida burin sanya diyansa mace makarantan boko..Moodu shine yafita zakka tun tasowarshi yaro ne mai kaifin basira komai aka koyamai yana daukeshi lokaci daya.,Yakasance mutum ne mai hakuri da kawaichi ko yana bukatar Abu bai iya fadi sai dai wanda ke tare dashi ya fahimta yayi sauka tun yana shekara bakwai Aduniya sauran littafai yake bita..Kullum safiya yana fitowa kofar gidansu inda wasu yara ke wucewa zuwa wata mkaranta boko ta gwannati.Abun na burgesa yana sha”awan Shima ya tsinci kansa cikin karatun na boko..Tun Zannah bai fahimta ba har ya Fahimta shikuma gashi Allah ya jarrbceshi da kaunar Dan nasa moodu shiyasa batare da shawara dakowa ba yasanya moodu mktantan prmary ta boko wanda hakan yakawo Rudani matuka ko Shettima bai so asanya shi ba ammh zannah moodu ya yi biris dasu yacikama Dansa burinsa..
   

  Cikin ikon Allah Moodu yakammallah Prmary sa cikin Nasara wanda kafin gamawarsa sai da yayi suna saboda kokarinsa da hazakarsa malamansu har gida suka zo gun zannah moodu suna fadamai irin baiwar Da Allah yayi ma yaronsa na kokari da hazaka hakan shiyakarama Zannah karfin gwiwan Sanya Moodu awata mkaranta maisuna IMMA MALIK mkarantace na ya”yan masu Dashi tana hade ne Arabi da boko..Cikin kudiran Allah Karatu yadinga Tafiya Da Nasara hazaka Moodu tawuce duk inda ake tunani, suma malaman makrantan da kansu sukazo gida suka ba Zannah Moodu shawaran kai moodu madina domin yahada degree sa na farko achan..Haka ko akayi da taimakon malaman mkarantan bayan kammallah jarabawan karshe dasu moodu Sukayi kuma Alhamdulillah yafito da sakamako maikyau..Zannah ya saida rabin Dabbobinsa yahada kudi akayi ma Moodu cuku cuku yasamu gurbin karatu ajami”ar Madina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button