UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Batawani ci dayawaba ta ture Lubna ta dauke bayan ta tsiyayamata ruwa okofi,tasha ta koshi,yanmatan ne kadai a bedroom din Su ashe da mahgana da Sauran suna falo suma Sun baje suna diban arziki,Lubna ce aciki da Zulaika sai zahirah da kawarta Asma”u,maminta tana falo wajen su hajiya Suna hira,Sai da suka kusa raba dare kana kowa ya kwanta saboda gajiyan hanya,zulaika da Lubna dakinta suka koma suka kwana,Su little ko wajen Ummi suka kwana Abunsu suma murna suke kamar sunsan sun dawo gida ne.
Washegari da hadahadar walimar dasu Ummi suka hada aka tashi ko kafin karfe goma tuni an kayata haraban gidan da kujeru farare da tanti,Karfe shadaya na safe aka fara gudanar da walima,Ummi ta gayyaci wata malama takanas daga zaria wato MALAMA SAFIYYA MUHD BA”ARE.,Ita tazo ta dagargaji wa”azin zama da miji da kwatanta adalci awajen maigida,dama ko awajen zama zahirah da Lubna suna sawun gaba hannunsu sarke da juna,hakikanin gaskiya wa”azin ya tsuma musu jiki matuka mussaman ma zahirah wacce taji duk kishin lubnar ya ficemata aka,in tayi duba da yadda bata kishi da ita,duk inda take tana tare da ita,tana nuna mata kauna mai tsanani,haka kurum taji ta burgeta,kuma itama tayi alkawarin taimakama mijinta wajen sauke nauyun dake wuyansa ko ya rabauta ranar gobe kiyama,Sai wajen uku na yammah aka tashi daga walimar bayan anci ansha,kuma anyi rabe raben su karamin alqur”ani da casbaha,da azakar da dabino,dauke cikin wata karamar jaka da”aka rubuta sunanye su Zahirah da mu”azzam din bayan ansaka Cut cee,Childreen SUHAIMA AND MUHMMED MOODU,abun sai wanda yagani,antashi cikin Farinciki da Annushuwa,bayan an cikama malama kayan arziki direbanta ya dauketa suka koma zaria.
Dare nayi aka fara shirin zuwa Dinner,wanda dukkansu matan ne Wato Lubna da zahirah wanda kowacce ta dau ado,kaya iri daya suka sa wani blue din material ne mai Stones fari suka sanya matukar kyau sunyi daya baka daya fara,ba”ayi african Time ba,Karfe 8:00pm aka fara dinner saboda ana so atashi da wuri,Guri ya cika da al”ummah Tundaga kan likitoci da lauyoyi domin kunsan yau ranar tasu ce,wannan karon hatta da Ummi da hajiya ba”a barsu abaya ba,sun hallarci wajen dinner din yan janaf novellah 1,2,hafnan novellah,Uwar mijina fans1,23 Zumunta novellah Taskar littafan hausa Aisha Alto Novels,Taskar marubuta da Sauransu suma sun sha anko sun hallarcin wajen dinner nan,sahibata kuwa barayin abinci ta nufa kowani kala sai taci dakuma ta fakaici indon mutane da diba ta zuba cikin wata burgamar jakarta,????????hakama Sisinah Aisha Alto ita tebura ta dinga bi duk wanda ya rage nama,sai tayi sauri ta dauke tana waige waige data ga ba”aganinta sai ta bude wani buhu da tazo dashi ta zuba aciiki…????????????, mu”azzam na tsakiyar matansa,wanda suka sha kyau Suka koshi,anci ansha anyi rawa,kuma anyi barin naira,koda za”a yanka cake,mu”azzam sai da yafara bama Zahirah kana ya juya yabama Lubna,ita kuma Lubna ta yanka tafara bawa zahirah kana ta juya tabama mu”azzam,haka itama Zahirah tayi Tako sha harara wajen Mu”azzam din wanda daga karshe suka bawa ya”yansu dukansu su ukun,Asma”u ko tana tare da Saurayinta wanda yagama sacemata zuciya mooh,suna chan suna zencensu na soyayyay,karfe 11:00pm aka tashi daga wajen dinner,kowa yakoma gidansa ya kwanta saboda gajiya yan maidugurima da Wuri Suka kwanta saboda gobe sammako zasuyi na tafiya gida.
Gari na wayewa Su Ashe suka fara shirin komawa gida karfe takwas na safe Ushe ya daukesu zuwa maiduguru cike da kayan alheri daga mu”azzam da Ummi,hajiya da zulaika da shureim ma sha biyu nayi suma suka dau hanya bayan Hajiya tatarasu tana musu nasiha,Su Asma”u ne karshen Tafiya domin maminta tabi zuwa gida,domin sai an kwana biyu kozata koma mkranta,bayan sun karbi nombar juna ita da mooh,wanda ya jaddadamata kafin yakoma sudan zaizo suyi mgana,to haka dai aka rabu cikin kewa Dr.Abduljabar ma aranar yakoma gida,gida ya rage daga Ummi sai mom,sai Lubna da zahirah da mu”azzam da ya”yansu little Ummi da moodu wadanda suka samu sabon waje sai guje guje suke,antafi da cikinsu an dawo dasu da kafarsu Allah kenan..
Kai yasin nagaji
janafty
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)
Mallakar:JANAF
Wattpad:Janafnancy12
Dedicated to my blood Sisters JANAF
GIFT TO:Hussain80k
Intelligent writer’s Asso✏
NOT EDITED????
NO 45
“””Sai da baki suka tafi kana Ummi tatarasu Zahirah da mu”azzam da lubna da mom da mooh tayi musu nasiha mai ratsa jiki nan take takira Abbie ta waya shima yayi ma mu”azzam nashi nasihan duk dai fadan na su zauna lafiya ne,kuma ya kwatanta adalci.
Ummi ta taso har inda take takama Hannun Zahirah tana fadin”Don Allah zahirah kiyiman alfarma taimakama mu”azzam wajen kwatantanta adalci a tsakaninki da lubna ki kuma yimin alfarmar zaki kalleta ne amtsayin yar”uwa ba kishiya ba don Allah kiyiman wannan alfarmar..”Rike hannunta zahirah tayi tana fadin”Nayi miki Ummi wlh bazan Rike Lubna dawani mgunta ba,mganar adalci kuma insha Allahu yaya mu”azzam zai kwatanta atsakaninmu domin in knga gida yana zaune lafiya to hadin kan Matansa,nikuma na tabbata yadda bani da mtsala haka itama kanwata bata dashi ko ba haka ba kanwata? tafada tana kallon Lubna.
Mirmishi tayi kafin tace”Hakane Ummi insha Allahu bazaki samu wata baraka daga barayina ba nayi miki alqawarin rike ki,amtsayin uwata zahirah kuma amatsayin yayata kana yaya mu”azzam amtsayin yayana,kuma adalin miji gareni bazan taba Fushi don ya nuna gazawarsa akaina ba,zanyi kokarin naga nayi mai biyayyah har zuwa karshen numfashina..”Tafada tana sunkuyar dakai gyada kai Ummi ta hauyi tana share kwallah kan tace”Naji dadi kuma na gode muku,indai kukamin haka kun gamamin komai,Allah ya zaunar daku lafiya ya kauda duk wata fitina Atsakaninku.”Dukkansu suka amsa da Amin.
Tashi ta isa ga mu”azzam wanda ke zaune kusa da mooh ta riko hannunsa ta Tana fadin”Son..”Dago kansa yayi yana fadin”Ummina..”yafada yana Tsareta da ido,Kansa ta dafa tana fadin”Kaji batun matanka don Allah ina rokonka kada kaba shedan daman Shigowa ya tarwatsa zamanku,kayi adalci atsakaninsu duka matankane,kuma dukkansu yan”uwanka ne najini,zahirah ya”take ga yar’mahaifinka Marigayi fadi,ayayin da Lubna diyatake wajen Abbanka khamis,kuma dukkansu kaunace yasa zaku zauna atare,To ina so kakiji kuma kaki gani,ka yi kokarin samu lahirarka ta hanyar kyautatama iyalanka in kayi haka,har in mutu ina sakama rayuwarka albarka..”mu”azzam da idonsa ya ciko da kwallah jin batun Ummi,wacce ta dauresa da maganganunta,Saurin Dafa hannunta yayi yana fadin”Naji kuma na dauka Ummi,insha Allahu zanyi kokarin yin yadda kikace,ammh ina bukatar addu”arki domin samun kwarin gwiwa kan dukkan al”amarina..”yafada yana kafeta da ido,ko bata tambaya ba,tasan meyasa yace haka Kansa tahau Shafawa tana fadin”kullum bakina baya gazawa da maka addu”a Son,Allah yabaka ikon yin adalci,yakuma albarkaci rayuwarka data iyalanka..”Kowa Afalon ya shiga amsawa da Amin bayan Ummi ta mike ne ta kalli mom tace”Rumana kema kiyi musu naki nasihan..”