UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Hannunta ya riko ya zaunar da ita kan Ciyarsa kafin yace yana kallon kwayan idonta yace”Mai jego..”yafada yana yar dariya,kallonsa tayi kafin tace”angon karni..”zahirah tace”angon karni karni zaki ce,..”harara ya zabgamata kafin yace”Kefa yanzu kin zama muguwa ko,To kisha kuraminki kuna haihuwa Aure zan kara tazo ta taimakamana.”Saurin waro ido sukayi tare,lokaci daya suka riko hannunsa atare,dariya ta kwacemai ammh ya kanne,kafin yace”eh Dukkan kunzama Jangwan lokaci babu maitaimakona ba gwanda nasamu wacce zata dinga debemin kewa ba”Filon dake jingine da zahirah Lubna taja tana fadin”Anty mu fara dashi,kafin mu ganta mai tsautsayin da zata aurarmana miji.”Gyada kai zahirah tayi kan su hada hannu a Filon suna makama Mu”azzam din Zahirah na fadin”Sai kayi Auren mu gani ai mu daga mu sai dai Amutu ahaka..”Shiko dariya yake yana kare kansa yake fadin”Wayyo Ummi,kizo wlh mugayene zasu kashe miki danki,wayyo Ummi..”yake fada kafin ya mulmula kan gadon ya danne Zahirah da hannu daya ya fizgo Lubna ta fada kanshi duka ya hadasu ya rumgume yana dariya yake fadin”Alhamdulillah Allah nagodemaka,Kune matana aduniya kuma ina fatan kuzamo matana har a aljannah Firdausi..”Da Amin Suka amsa duka suna Rumgumosa cikin Farinciki mara misaltuwa

A ranar da daddare aka sallami Zahirah suka koma gida bayan ya rubuta musu magungunar karin jini kuma,dukkansu yace babu aiki mai nauyi suna bukatar hutu na tsawon Sati biyu,shiyasa mu”azzam Yace Tun Wurima subawa Lubna hutu,don bazata dinga zuwa aiki tana wahalarmai da ciki ba,Agaban Ummi dr,namai dariya shiko ko ajikinsa,dole itama aka bata hutun sati biyu taje ta huta.

  Tabbas Lubna da Zahirah suna ganin gata na hakika da soyayyah tare da kulawa,mu”azzam kafin ya tafi aiki shi zai musu wanka dukkansu ya shiryasu,kafin ya fice zuwa office,in yatafi yashiga kiransu kenan yana Tambayansu me suke so,mezasu ci,babu bambamci atsakaninsu,ita Da Lubna yana kokarin nuna adalci da kulawa babu bambamci Atsakaninsu,haka Ummi ma tana iyabakin kokarinta akansu kamar ita ta haifesu haka takeji,su little Ummi kuwa Tuni Ummi tabada shawaran ayayesu abarsu awajenta,Tunda suna da wata goma sha takwas ne alokacin,Ada mu”azzam bai so ammh ganin Hujjojin da Ummi ta kawomai ya yarda zahirah ta ciresu anono,dayakema basu wani damu da nonon ba,shiyasa basuyi wani Rigima mai tsawo ba,Suka hakura suka cigaba da shan tea da kuma madara wacce take taimaka musu wajen yin girma,Labrin cikinsu zahirah ko ba inda bai zaga ba,hajiya harda juyi sanda Ummi ke fadamata ta waya,Kirari tayi ma Allah kan tace”Suhaima kin gani ko,ashe akwa raboi mai yawa tsakanin zahirah da mu”azzam,sannan ga Lubna itama rabon ne yakaishi sudan har suka hadu,sai ki godema Allah,Mu”azzam kadai kika haifa,yau gashi ta dalilinsa zai tara miki zuru”a na ban mamaki..”Ummi na hawaye take fadin’nagani hajiya,wanda bai godema Allah da da ni”imarsa ba to zai godema Azabansa wata rana..”

   Shureim kuwa dariya yake yana fadin”Yaron nan,narigasa shiga daga ciki,ammh yau gashi yana neman Wuceni..”Mu”azzam yace”Sa wasa,ai ni Mai gabadaya ne,bana wasa duk sadda na mika sai an amsa..”Baki shureim ya rike yana fadin”lalle ka zama dan iska mata sun budemaka ido ko”baki ya murgudamai kamar yana ganinsa yace”Eh din kai din fa..”yafada yana mai dariya,katse kiran Shureim yayi yana fadin”Dan”uwa ya lalace da mata..”yafada yana shafa kansa kan kuma yace”banga laifinsa ba,mata abun so ne,kune rayuwa.

Chan Sudan ma da lbrin ya iskesu Abun ba’a cewa komai,sun kira waya suna bayyana murnansu haka chan maiduguri suka ji lbri suma Farinciiki kamar mene,Bukar Saboda murna ya rasa ina zai saka kanshi kowa yaji sai yayi Farinciki tare da jinjinama Hikimar Allah da kudiransa,Satin Biyu da aka dibamasu Zahirah harya cika Tuni ta warware har Lubna takoma bakin aikinta.

Ranar wata jumma”a Da safe kwatsam Mu”azzam na wajen aiki yasamu kira daga maiduguri Bukar da kanshi ya kirasa yana fadamai yazo maiduguri da gaggawa jikin Baffa jiya da daddare yatashi a asibitima suka kwana,jiki kam babu dadi domin yakwana yana kiran sunansa dana mahaifinsa,jin haka yasa hankalin Mu”azzam ya tashi daga office yadau Excuss ko gida bai dawo ba,awaya yakira Ummi yake shaidamata ya wuce airport,yana zuwa ko yasamu jirgin da zai wuce maiduguri nan da nan suka lula,Bukar yazo Airport din maiduguri ya daukesa,zuwa asibitin da suka kai baffa babu laifi babban asibiti ne domin private ce,Lokacin da mu”azzam yaga baffa shettima bai san sadda ya fashe da kuka ba,baffa baya gane wanda ke kansa,kwata kwata,sai wasu surutai yake yi yana kiran sunan fadi da moodu yana fadin gayinan zuwa garesu zasu zauna tare,Mu”azzam kuka bukar kuka yagana kuka,mahgana kuka saboda tsausayin Baffa

Mu”azzam waje ya fita yakira Shureim awaya yana fadamai gobe yazo yana so kawai su fita Da Abbah zuwa kasar india suma su jaraba nasu su gani,shureim bayason yima mu”azzam gaddama ne saboda yadda ya gansa arude ammh a bayanin dayake mai na yadda baffa keyi anzo gangarane,bayan sun gama waya yakira Ummi yake fadamata halin da”ake ciki,yakuma ce gobe da sassafe duka su tararro suzo su duba baffan da jiki,Hakika Ummi jikinta yayi sanyi da yadda taji muryan mu”azzam,Tana tsoron shima awayi gari babu Shettima shima,tun adaren tafadama Su zahirah kan su shirya Ga Abunda mu”azzam yace,zahirah kuka ta fashe dashi Lubna ma sai hawaye to haka dai sukai kwanan jugum,Ummi ko runtsawa bata samu tayi ba,sallah tayi tayi tana neman ma shettima fatan sauki,karfe uku na dare wayan Ummi ta shiga neman Dauki,jikinta na rawa tajawo ta duba ganin Sunan Son ya fito baro baro shiya fadar mata da gaba.

  Hankalinta atashe tadaga kiran tana fadin”Son,ya jikin shettiman..? majina mu”azzam ya sharbe kan yace”Ummi Ciwon baffa ya kare..”dafe kirji Ummi tayi kan tace”ban..ga..ne ba..”Kuka ya kubcema Mu”azzam yace”Allah yayima baffa cikawa Ummi yanzu ba dadewa ba…”Mikewa Ummi tayi tana makyarkyata take fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju”un..Allah gareka muke kuma gareka zamu koma,Allah kajikan Sheettima kasa Aljannah ce makomarsa..”Ummi tafada tana fashewa da kuka,Mu”azzam yace”Ku taho da wuri Ummi hardsu,ki kulan da hirah kada kibari tayi kuka da yawa saboda halin datake ciki sai kun taho..”daga haka ya yanke kiran yana kara dafe bangon daya jingina yana share kwallah,daga gefe kuma yakura ne,keta kuka tana sharan majina,bukar ma gefe yana salati tare da sharan kwallah,dama sune suka tsaya dashi asibitin mahgana tatafi gida ita dasu Alee,adaren mu”azzam yakira shureim da Dr Abduljabar ya fadamusu rasuwar baffa,wanda Mutuwar tadakesu sosai sukace gobe suna tafe,sudan ne bai kirasu ba sai da Asuba ya kira Abbie yana fadamasa Abbie yaji mutuwar baffa sosai yayi ta kwararami addu”an samu dacewa wajen Allah,tare da bama mu”azzam hakurin Da kuma zama mai juriya adukkan jarabawan ubangiji.

Sai da safe Ummi kedama su zahirah Rasuwar baffa,Zahirah kadan yarage bata fadi ba,Lubna ta riketa,tayi kuka ita da Ummi har idanunsu suka kumbura karfe takwas na safe suka dau hanya Ushe ne tukasa,Ummi da zahirah da Lubna sai su little Ummi,ko karya basuyi ba,domin babu wanda zai iya sakama cikinshi wani abu,Ummi na rike da chasbawa tana ja,tana sharan kwallah,Itako zahirah zazzabi ne keneman Rufeta saboda kuka dadamuwa,suna hanya hajiya takira Ummi ta take tambayanta suna ina Ummi tace”Gasu bisa hanya..””Hajiya tace”ok Muma gamu bisa hanya..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button