UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Alhaji ya washe baki yana fadin”Masha Allah..”lokacin ne,kuma yaga zahirah wacce kanta ke duke,mu”azzam ne da kansa ya mike ya isa ga Alhaji ya mikamai hannu yana fadin”Sunana brr,mu”azzam nine mijin zahirah nada,da na yanzu..”mikasa yayi sukayi musabaha kan Mu”azzam ya cigaba da cewa”munji lbrin rasuwar maidakinka Shine kafin mu wuce mukace bari muzo muyi maka gaisuwa..”Cikin jin dadi Alhaji yace”Hakuri da godiya wlh ngd sosai,kuma yanaku hakurin? Allah yajikan Sheettima yasa ya huta..”Suka amsa da Amin kafin su Ummi Su shigamai gaisuwa yana amsawa zahirah ce ta karshe tafada asanyaye,Shima asanyayen ya amsamata yana kokarin danne wani Abu,matarsa hajara yakallah kan yace”Kinga zahirah dana baki lbrinta nan,ga yan biyu,suma kingansu wa”innan iyayyantane da mijinta suka zo min gaisuwa,dayake suma Wan mahaifinsu ya rasu,yau sati daya..”gyada kai tayi kafin tace”ayyah sannuku da zuwa,Allah yajikansu..”suka amsa da Amin.

Kafin ya cigaba da cewa”Matata kenan Sunanta hajara daga kano na Aurota..”Su Ummi suka amsa da masha Allah,suna musu fatan zama lafiya da zuru”a dayyiba.”ya amsa da Amin Amin Falon yadanyi Shuru kafin mu”azzam yayi gyaran murya yace”Dama na dade inajiran wannan Ranar,dazato nima narama maka Kwatankwacin Hallarcin dakamin..”yafada kan ya cigaba da fadin”kowa ya Shaida Alhaji yasaki zahirah ne saboda ya cece rayuwata daga mutuwa..”Kowa afalon ya bishi da ido banda Ummi da Lubna sai zahirah wacce kanta ke kasa.

  Bukar yace”bamu gane ba,kasamu aduhu mu”azzam..”Alhaji yayi saurin cewa”Don Allah karka tada mganarnan ni don Allah nayi,kuma harga Allah bantaba fadama wani nawa ba,mu binneta iya mu da muka sani..”Ummi ce ta mike tana fadin”Bazai yuyu ba Alhaji dole mu fadi kowa yaji..”Kan tajuya kan bukar tana fadin”Eh da gaske ne,ninazo dakai na rokeshi tare da fadamai halin da mu”azzam yake ciki alokacim,Nan ta shiga basu lbrin komai Tundaga farko har karshe,kafin ta karishe da cewa”kuma banyi hakan dawata manufa ba,sai don Ceto Mu”azzam daga Halin dayake ciki..”Sai falon ya dau Shuru kowa yana auna Abun yana jinjinakai Hajiya ce tayi karfin halin cewa”Baku kyauta ba Suhaima,gaskiya baku kyautaba,ai ba haka akeyi ba,mutum da matarsa kizo kice sai ya saketa saboda danki,to shi wani hali zai Shiga in ya rabu da ita..”Sunkuyar dakai Ummi tayi kafin tace”Nakasa juran ganin halin da Son yake ciki ne alokacin wlh banma san sadda nazo ba”Tafada tana kuka.

Bukar ne yace”Ya isa hajiya tunda aikin gama ya riga yagama,shima Alhajin baikamata ya biyemusu ba,ammh hakan babu laifi donko a addini akwai sadaukarwa, wani Abun indai Abun yafi muhimmanci garesa,kuma yafika bukatuwan Abun,hakan babu kuskure acikin saidai muyi fatan Allah yabamu da ladan Abun..”Dukkansu suka amsa da Amin.

  Mu”azzam baiyi mgana ba ya kama hannun Alhaji danasu Little Ummi yahada yana fadin”Ku shaida daga yau ni mu”azzam muhammed moodu na barma ko nace na mallakama Alhaji kabiru Little Ummi da moodu karami halak malak,ko bayan raina shine mahaifinsu ni sai dai na amsa sunan Ubansu asuna..”yafada yana kallon idanunwan zahirah da Ummi,wanda sukaji mganar abazata.

Zaro ido Alhaji yayi yana fadin”Ni..Ni..Ka..ba..Ma….”yafada yana rawar baki,gyadai mu”azzam yayi yana fadin”Eh na baku su halak malak kaine yanzu mahaifinsu matarka kuma mahaifiyarsu..”Ai sai Alhaji yayi luuu zai fadi mu”azzam yatarosa yana kiran sunanshi,fashewa da kuka kawai Alhaji kabiru yayi kafin ya hada Mu”azzam da yaran ya rumgume yana fadin”Ashe akwai ranar da wani zai sani Farincikin daka sani,duk duniya bani da kishirruwan komai sai nasamu zuru”a Ammh kuma Allah bai bani ba,sai gashi wanda banzata ba ya mallakamin Abunda ni bazan iya samarwa ba niko dawani baki zanyi godiya,Don Allah kutayani godiya”yafada yana hawaye,Sakinsa mu”azzam yayi kafin yace”Basai ka godemin ba,nima kabani abu mafi soyuwa da daraja atare dani,so ya”yan ne yanzu kafara tarawa,da an haifa an yaye zasu dawo hannunka,insha Allahu..”washe baki Alhaji yayi kamar yayima mu”azzam sujudda.

Hajara tazo ta amshi su little ta rumgume tana hawaye,ta duka harkasa tanama mu”azzam godiya,suka ko lafe ajikinta kamar sunsan yanzu itace makwafin uwarsu,Ummi da zahirah Zuciyarsu bata baci ba saboda hukuncin mu”azzzam duba da yadda Alhaji yayi musu hallarci yasake basu daman mallakan juna akarona biyu,Ummi kowa bata saka komai,domin nan da wata shekara ai wasu jikokin zasu zo bama daya ba biyu ba,kila Fiye da haka itama ta nuna murnanta haka hajiya da Shureim,Bukar ko yakasa mgana saboda Farincikin nan fa aka hadu anata godiya tare da jinjima Karamci da Zurfin Tunanin Mu”azzam,shiko damam Wannan kyautar tuni tadade aransa,tun Sadda zahirah ta bashi lbrin Alhaji da halin dayake ciki,shiko yayi alqawarin Shima sai yabashi wani Abu mai muhimmanci kamar yadda Shima yabashi.

  Sai gashi anan sukayi lonching dinsu anayi ana hira da dariya,anzama daya,koda Alhaji yaji zencen Bikin mooh da za”ayi nan da wata daya,nan yace insha Allahu zasu zo ayi dasu,suma domin yanzu duka anzama daya,basu sukabar gidan ba sai yammah,su little da farko da sukaga za”a tafi abarsu kuka suka saka,Sai da hajara tashige dasu jiki kana suka samu tafiya,Hajara ba yarinya bace akallah zata kai shekara talatin da biyar Aurenta daya da Ya”yanta biyu Allah yayima mijin nata rasuwa,macece mai hankali da kirki da kawaici macece datasan ciwon kanta da darajan Aurenta,ada Alhaji yaso karban ya”yanta ya rikesu ammh dangin baban yaran suka hanashi yaran dole yahakura,sai gashi budi daga Allah ya kawomai Yaran dayake tsananin kauna wanda baitaba zato ba,Asibitici kuwa tunda ga na kasarmu Nageria har zuwa kasashen ketare sai da yaje,ammh amsam dayane lafiyansa kalau,sudai in ma da mtsala sudai basu gani ba,saboda haka ya kwantar da hankalinsa lokacin haihuwansa ne baiyi ba,ammh inyanada rabo sai yaga ya haihuwa nan kusa,ko da nisa duk Allah yabarma kansa sani,saboda damuwa hakan tuni hawan jini yakamasa duk sati in aka auna bp sa sai likita yayitamai fada kan daina,saka damuwa ransa,saboda lafiyansa baya da yadda zaiyine Rashin haihuwan nan bakaramin tadaimai hankali yake ba,yanzu Tun inna na damuwa Harta cire Abun aranta saboda yadda taga da’n nata yafita damuwa,shiyasa tadaina nunamai damuwar haka takoma bashi baki.

Kwana daya suka kara,dukkansu suka tattara suka koma gidajensu tare da yakura su mu”azzam suka tafi bayan sun barma bukar cewa asamu wani magidanci yazauna shida iyalansa adayan barayin saboda kada abar gidan babu kowa,ko banza mutum agida ma Rahamane,Su hajiya suma daganan suka wuce su suka farama yin gaba kafin su Ummi,yakura tayi sallama da makota da abokan arzuka da yan”uwanta wanda basuso tafiyanta buh Sunyi duba da cewa sai tafi samun kwanciyar hankali achan fiye da tana wajensu shiyasa suka bita da fatan Alheri tare fatan Allah yasa sugana,ita kanta mahgana sai da tayi kwallah saboda shakuwarsu da yakura,ammh yau sanadin mutuwa sun rabu,sunaji suna gani motarsu ta daga daga gidan,Kayan cikin gidan ma suk sadaka mu”azzam yace ayi dasu nan da nan ko makota suka kwashe domin kayane masu kyau don bai dade da chanza musu komai na gidan ba,Ko kayan sawa bai bari yakura ta dauka ba,duk yace tabari sai taje chan zai siyamata komai,su bukar basu rufe gidan ba,sai da suka tabbatar sun bada sadakar komai kafin su tafi,mganar wanda zai zauna kuma yabari sai yasamu mai amana kafin yayarda yabashi amanar gidan Tunda dai gida dai mallakin yakura ne,domin baffa bai da wani dan”uwa sai ita,fadi bata rai,haka moodu ma,mu”azzam kuma yanada wadatarsa baya bukatar komai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button