UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Rike baki mu”azzam yayi yana fadin”yau naga yaran zamani,nima ido kukasamin ashe..”Dariya lubna tayi bata ankaraba mu”azzam ya sakarmata rankwashi akai yana fadin”ke kike daure musu gindi suke wannan Abun,to muma bamu bukatarku Ayashe ta gaida ayyah..”Dafe kai lubna tayi kafin tace ashagwabe'”Kai Daddy gaban ya”yana zaka rankwashe ni..”Dariya zahirah tayi kan tace”Wlh kau,ankusa yin Abun kunya..”Mu”azzam yace”bakijin mgana ne,dat why na miki dukan shari”a ko yan biyuna..”Kallon juna sukayi moodu da little kan su hada ido suce”Hmmm..Daddy kenan..”Suka fada harda hada kafada,Kallonsu yayi kan yace”Daddy mene Eye..”Dariya sukayi kan suce”Daddy da momy da mami..hmmm sai Allah..”Suka fada harda tafawa,Dariya iyayan suka kwashe kan mu”azzam yace”Kunga yan biyunan akwaisu da gulma.”Little ce tace”Bawani gulma Daddy kullum bakwa tsufa,Rayuwarku tana burgeni sosai Daddy Allah yabani miji wanda zai soni kamar yadda kakeson mommy da mami..”Baki zahirah ta rike kan tace”la’ila ha’illahi…”Mu”azzam yace”Eye Ummina To Amin”ya fada yana dariya sunne kai tayi tana dariya kan taruga zata shiga shashen Ummi sai gata da buyagin yara suka ci karo da little tace”Ke lafyan ki,kike Gudu haka?..”

Ummi na kallah sai da nayi Kabbara Allahu akabar Ummi ce da kaganta fuskarta bata chanzaba,ammh ta tsufa don akallah zatabama 70 baya gashin kanta yakoma fari,hartama dan duka,Furkarta yadan chanza,ammh hutu da jin dadi yasa hasken fatanta na nan,tafe take da yaran kai da kai,kowane yana rike da ita yana fadin”Ummi kaza,Ummi kaza..”Allah sarki Ummi dama Abunda takeso kenan,to yau ga mu”azzam yataramata ya”ya kiriniya da hayaniya kuwa sai wanda yagani.

  Zahirah ce tatarota tana fadin”Takwaranki keson Aure Ummi…”Ummi ta kalli little tace”Yo miye aciki,inace kema kina kamanta aka miki auren ko..”Sunne kai zahirah tayi akafadan mu”azzam suko sauran yaran suka saka dariya,Ummi ta riko hannu little tana fadin”Zo muje dakina kifadamin wakikeso takwara,ni dakaina zani gidansu na tambayan miki izini wajen iyayansa..”Dariya su zahirah suka saka ,zaro ido little tayi kan tace”kai Ummi..”eh mana..”Ummi ta katseta tana jan hannunta yaran sukayi duu zasu biyosu moodu ya daka musu tsawa mu”azzam ya harareshi kafin yace”Kai karka firgitamin ya”,yana kuzonan kunji ya”yan Daddy baisan darajan haihuwa bane sai ya haifa..”Bata rai yayi kafin zahirah tace”Bi bayansu daman Ummi ai ta iya biyema shirmenku kaida yar”uwantaka..”Bai ko kallesu ba ya wuce yana fadin”Ko muntafi Ummi kawai da mami za muyi missing sauran ko..Hmm..”yafada harda daga kafa,Zahirh tace”muma mun yafe wlh Allah raka taki gona..”yana kunkuni ya shige shashen Ummi,wanda daman chan suke wuni in hayaniyar ya”yan momy ya damesu,wani lokacin kuma dakin Ummi aketarewa duka yaran suna kiriniya,aiko yaya moodu yayi jam ido in anki yakai hannu,sakamakom su ita little Ummi babu ruwanta tana da sanyi sosai dayake gabadaya yaran Hutu suke.

  Muntaz ne tafito daga daki tana fadin”Mommy ina biccuit dina dana ijiye adaki ban gani ba..”hajiya karama tayi karan tace”Yaya muntaz nadauka na cinye..”Zaro ido muntaz tayi kafin tace”Kut nace ki daukane da zaki daukanmin Abu,bakuna da naku biccuit din ba..”da Sauri zahirah tace”a”a uwata ta kaina rabu da ita,muje daki na baki wani banason kina shiga shirgin yaran nan,kinsan ke uwace..”Dariya lubna tayi kantace”bawani Sonkai dai ake nunamana kiri kiri..”mu”azzam yace”Kema kya fada,dai..”zahirah taja hannu muntaz tana fadin”Eh din mutum da mamansa kuma sai abun yazama saka ido muje mama ki karba rabu da Daddy da mami yan adawane..”Washe baki tayi tana fadin”Dat my mommy..I love u..”Da haka suka shige cikin hannunsu sarke da juna,muntaz kenan,zahirah tana matukar kaunarta babu mai tabata ya zauna lafiya koda mu”azzam ne.

Bata jima ba,tafito daga ciki tana fadin”to bagashi ba har na bata wani tana ciki tana cin Abunta,na kashe rigiman..”Kyabe baki mu”azzam yayi kafin yace”next week zasu tafi zaria gabafayansu yaran,domin inason nima na sake da matana gaskiya..”Dukkansu dariya sukayi kafin yamike yana fadin”ku matanan zaku illatani da yunwa fa,almost pass 11 bamuyi breakfast ba..”Lubna tace’Kai ne kejin yunwa ammh Tuni yaran sun sha complex tun safe,oya kumuje kuyi breakfast kafin zo ayi wanka mufita mu buga basket ball..”Ihu suka saka suna fadin”ehyyyyee…Maminmu we love u so much..”Suke fada dukkansu dariya take tana fadin”I love u too my Childreen..”

Da kallo mu”azzam yabita har ta karisa dasu gaban makeken dining din tajama Kowa kujera tana kokarin Saving dinsu,Zahirah ce ta kwanto bisa jikinsa shiya dawo dashi cikin hankalinsa kafim tace”Kana kallon hidman mamin yarane..”Mirmishi yayi yana riketa yake fadin”Lubna ta kasance wata jigo ne na rayuwarmu ni dake zahirah,tabamu gudummuwa mai yawa,Duk tsawon zama da ita wlh batata batamin rai ko nuna wani damuwa da kishi kan irin son danake miki ba kuma koda rana daya batataba sabamin da gangan ba,kullim cikin min biyayya take,to in zuciyata bata girmama alherinta ta sakamata tabata waje acikin zuciya ta ba nakega kamar bata mata adalci ba.”

Dagowa zahirah tayi ta kallesa tana mirmishi tace”Sosaima Ai im baka so mamin yara ba,yaya kayi butulci Allah kuwa..”Ya runtse yana fadin”Ina sonta sosai my hirah,Tunda na fahimci tanason abayyana mata so,nikuma nayi alqawarin bayyanamata shi akoda yaushe..Ina sonku dukkanku matana na duniya dana Aljannah…”Yafada yana rumgume zahirah ji yayi an Rumgumesa tabaya ana dariya Lubna Ce,tun dazu take tsaye tana jinsu tazo cewa suzo suyi breakfasat sai ta iskesu suna mganar Zahirah tamata in kiya da ido da tayi Shuru kartayi mgana sai yakai aya..

  Dukkansu suka hada baki wajen fadin”MUMA MUNA MATUKAR SONKA MIJINMI,GWARZONMU,BANGONMU KUMA ABUN ALFAHARINMU…,”Suka fada suna dariya Juyo da lubna yayi yana kallonsu Kafin yace”Kai gaskiya Allah nasona,duka matana kyawawane..”Suma sukace”muma Allah na sonmu don mijinmu daya tamkar da dubune cikin maza”dariya ya saki kan Shafa kansa yana fadin”To dukkanmu mu godema Allah daya mallakama juna..”Fadawa Jikinsa sukayi suna fadi atare su duka ukun..” ALHAMDULILLAH… Tafi sukaji daga bayansu suna waigawa suka ga duka yayansu ne, little da moodu ne gaba Harda Ummi tana tsaye kwallah sun cika mata ido moodu yace”Oya all of us Say ALHAMDULILLAH..”Aikuwa suka dauka gabadayaALHAMDULILLAH..

NIMA ANAN NAKE CEWA ALHAMDULILLAHI GODIYATA TA TABBATA GA ALLAH (SWA) WANDA DA IKONSA KOMAI YAKE FARUWA,KANA TSIRA DA AMINCI ALLAH SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMED(SAW)TARE DA SAHABBANSA DA IYALANSA GABADAYA…KAMAR WASA NAFARA POSTING DIN UWAR MIJINA RANAR 7/7/2019 RANAR SUNDAY,MUKA FARA YAU NAYI GOBE BAZANYIBA,WATARANA MA HAR INA TSALLAKE KWANAKI,AMMH KUKAYITA HAKURI DA TSUMAYEN JIRANA GASHI AYAU 26/9/2019 RANAR THUESDAY MUN KAMMALLAH SHI,TO BADA KUDIRAN KOWA BANE SAI ALLAH DOMIN SHINE YABANI LAFIYAN YI MUKU TYPING GODIYATA GA ALLAH BAZATA TABA YANKEWA BA,INA ROKONSA YABANI LADAN ABUNDA NA RUBUTU DADAI,KUSKURE DANAYI ALLAH KA YAFEMIN DOMIN NOBODY ABOVE MISTAKE,KUMA DAN ADAM TARA YAKE BAI CIKA GOMA BA,KUKUMA ALLAH YABAKU IKON DAUKAN DARUSSAN DAKE CIKI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button