UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Koda sukaje sun iske Sani maigadi da Falalu durkushe sunatama yallabai sannu wanda ke kwance kan cinyar Ummi tana shafa kansa tana jeramai addu”o”i tana tofamai bisa kai,kamar zatai kuka kokuma ciwon yadawo jikinta nan su karime ma sukabi ayari suka zube suna jeramai sannu wanda ke amsamusu dakai kawai ammh a zahirin gaskiya jiyake dama shine su domin su basu da wata damuwar kamar yadda yake ciki,lafiyansa kalau kawai yarasa mezaicema Ummi ne, wanda hankalinta zai kwanta,to gashi bai tsiraba shiya manta yadda in yana ciwo Ummi haka zata sakashi gaba tana kuka bata sukuni sai ya samu lafiya..To yaudin ma hakane yafaru ita tadinga bashi abinci abaki Wanda yakeji kamar yana cin madaci ammh hakanan yaita Turawa yana gama ci dama tama Family doctor dinsu waya Dr Abduljabbar wanda yace yana hanya.

Koda Dr Abduljabar yazo yaduba mu’azzam kawai yace Rashin Samun hutu ne alluran barci yamai yace ya kwanta yasamu barci na good 5 hours yana tashi komai zai koma Normal,ai Ummi ta dakanta ta rikeshi har dakinta ta ciremai,takalmi da Socks taciremai caot din,ta kwantar dashi bisa gadonta tana Fadin”Oya sleep kaji dai Abunda Dr yace ko'”Yagyada mata kai yayi, sai tacigaba da cewa’Bani son katashi sai na tasheka da kaina so Rest kaji son”Tafada tana shafa kanshi.

Kallonta yakeyi kafin yariko hannunta yace”Nagode Ummi na Nagode”Yafada idanunsa sun kawo kwallah kafin yayima hannun kiss mirmishi tayi tamaidamai kiss din bisa goshi tana Fadin”Iz my duty son..Love u so much”Tafada tana kara kissing dinsa bisa goshinsa shikuma lokacin alluran tafara aiki idanunsa na lumshewa blanket tarufamai zuwa kwankwasonsa kafin ta fice bayan Ta rufomai kofa..Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar ya fashe da kuka..Yazaiyi Baffa shettima zai watsama kasa a ido ko Ummi wacce ta sadaukar da fatincikinta akansh,ta sadaukar da dukkan jin dadin Rayuwarta zuwa gareshi,yasan cewa Ummi bazatataba fahimtarsa ba kilama tayi Fushi dashi Fushi na har abada..Da wannan Tunanin barci yayi awon gaba dashi.

   “”””Saida yashafe wajen awa shidda yana barci kafin yatashi shima din kiran sallar mangarib ne yataadashi wanda daman haka yake komai Nauyin barci wlh ana fara kiran sallah Allah ke tayar dashi..daidai lokacin daya mike Ummi ta shigo dakin Ganinsa zaune yasa Takarisa tana Fadin” Nasan daman yanzu zaka tashi shiyasa na shigo”Tafada tana zama kusa dashi wuyansa tataba zuwa kansa tana Fadin”Ya jikin hop u feel better Now, son?”Tafada murya cikin Damuwa lumshe ido yayi kafin ya bude cikin sansanyar murya yace”Naji Sauki Ummi daman Ciwon kai ne,fa kawai”Yafada yana kallonta.

   Shiiiiiii..”Tace hannunta bisa bakinshi kafin tace”Ciwon kanka son Awurina ba kawai bane,bakasan tashin hankalin dana ke shiga bane duk sa”ilin dana ganka ba cikin walwalwarka ba”Tafada tana shafa fuskarsa riko hannuwanta yayi yana Fadin”Duk wanda yasamu Uwa kamar tawa Uwar hakika shi mai Sa”a ne kamar yadda nasan Nimai Sa”ane Nasamun ki Amtsayin mahaifiyata Ummi na”Yafada yana kwantar da kansa bisa kafadanta,Hannu tasanya tana shafa kanshi mirmishi take kawai ammh takasa furta komai sai shine keta maimata “ina sonki Ummi na”.

Har dare yayi haka Ummi keta hidima da mu”azzam ko abinci takasaci wayyo baiwar Allah gabadaya tsausayinta yacika Mu”azzam shiyasa yafaramata barcin karya donta kyalesa yaje dakinsa ya kwanta..Ammh ina Ummi bata yarda ba Dakinta takara maidashi ta, kwantar dashi kamar wani jariri bayan ta Tofeshi da addu”a Kallonta kawai Mu”azzam keyi baida tacewa gashikuma soyake ya kebe yakira Shureim yafadamai komai ke faruwa domin kanshi fa ya kulle ya Rasa mafita.

****   ****

   kwana Uku mu”azzam yayi Ummi bata barinsa Fita ko”ina wai sai yagama warwarewa Ranar na ukun da kuzarinsa yatashi shima din dakyar tabari yatafi aiki sai daya tabbatarmata da cewa ya warke kuma zai kula da kanshi..Suna Fita yacema Ushe kaduna zasu sai da Shureim ya gansa kwatsam kiransa kawai yayi yacemai yana ina ?yace yana cikin asibiti “

  Kallo Farko Shureim yayima Mu”azzam yasan ba lafiya yana tsakar duba patient ne ammh dole ya yanke ya turama wani Likitansu yadda kai kawai mu”azzam yayi bisa kafadansa yana fadin”Yazanyi dan”uwa ina cikin damuwa kirjina yamin Nauyi bansa yazanyi ba na shiga tsaka mai wuya”Yafada kamar zai fashe da kuka bubbuga bayansa Shureim yakeyi baiyi mgana ba sai zuwa chan yadago kujera yaja masa ya zauna karamin Fridge din dake office din yabude ya dauko Ruwa kofunan dake saman gun ajere ,yadau daya ya tsiyayamai Ruwa ya mikamai ba musu ya karba yasha Yakara mikamai alamar yakarama ba musu Dr Shureim ya zubamai sai dayakusa shanye rabi kana yadagamai hannu maida komai yayi ma”adanarsa kafin yakoma ya zauna yana Fuskartarsa kafin ma Dr Shureim yayi mgana Mu”azzam ya rigasa da cewa.

  “Sun saka Ranar Dauren Auren fa”Yafada cikin wani yanayi zaro ido Dr Shureim yayi kafin yace”Kai don Allah wasa ko gaske”Wani kallo Mu”azzam yamai kafin yace”Kaga alamar wasa atare dani wlh da gaske nake jiya baffa ke fadamun nan Da two week nazo adaura Aure”Dafe kai Dr Shureim yayi yana Fadin”Innalillahi Dan”uwa Abu fa ya rikice Yazamuyi Da Ummi shine babban problem din

“kallonsa kawai mu”azzam yayi idanunsa sunyi jawur yace”Shine nakasa nemo mafita.juz tell me ya zanyi.ni kamar ma na gudu daga kasar gabadaya wlh”yafada yana dafe kansa saurin girgixa kai Dr Shureim yayi kafin yace”No bashine solution ba,yanzu Abunda za”ayi kakoma gida gobe zanzo sai mutaru mu fadama Ummi ko ya kagani”zare ido mu”azzam yayi kafin yace”Wata Ummi kaga mallam nemo wata hanya dai…Kana tsammanin Ummi taji wannan lbrin bata Yanke jiki ta fadi ba kasan ko yadda Ummi tadauki gaba mai tsanani dasu Baffa”Yafada cikin Nuna Abun ya ishesa.

Dafe kai Dr Shureim yayi kafin yace”Hajiya fa bazatayi wani Abu akai ba”dagowa yayi kafin yace”Hajiyarmu..”gyada masa kai Dr shureim yayi Dan ihu Mu”azzam yayi kafin yace”Yes gud..Ka kawo shawara kafadama hajiyar tamu yadda kukayi sai naji..Ammh wlh fadama Ummi ba mafita bane dan”uwa kafi kowa sanin Ummi kai fi daya ce”

“insha Allah komai zai Tafi daidai karka damu” shureim yafada Mikewa Mu”azzam yayi ya mikasa hannu sukayi musabaha yana fadin”Ina da wata shari”a Zan koma sai munyi waya”Damke hannunsa Dr yayi kafin yace”Kadaina damuwa plz dan”uwa anytin will be alright kaji”Gyada kai kawai yayi kafin ya fice a office din Ransa a jagule…

Koda Dr Shureim yakoma gida bai fadama hajiya ba sai da safe itakanta ta shiga rudu tadinga juya Abin Aranta kafin tace”Shureim akwai mtsala Suhaima tanajin dukkan mganata ammh akan  Abunda yashafi zuru”ar moodu zuciyarta ta tsaure Abunda suka mata yasakarmata dafi mai zafi wanda mantashi sai anyi babban jihadi..Kai na ya kulle wlh Suhaima baza tataba yarda Mu”azzam ya auro diyar fadi ba bazata taba yarda ba”Tafada cikin tabbatarwa..Jikin Shureim yayi bala”in Sanyi rausayar dakai yayi kafin yace”Plz hajiya do Sometin ke kadai ce hop dinmu wlh”Kallonsa tayi kafin tace”baka son komai ba shiyasa ai shi mu”azzam din yasani shiyasa yakasa Fadamata,ammh kubar komai Ahannuna zuwa gobe in na yanke decision zan Nemeka”mirmishi yayi yace”yauwa barrister tink abount it nasan baki rasa mafita”Fulon kujera tamakamai Tana fadin”Ka maidani kakarka ko Shureim”Ficewa yayi yana fadin”Matsayinki na mutum uku ne uwa,uba,kaka kinga dole na dinga taba kowani barayi”Dahaka yafice yana dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button