UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ko takan Nurses din dake kokarin amsan Ummi su sanya bisa gadon jinya dake hannunsu baiyi ba,kai tsaye office din DR.Abduljabbar ya shiga yana Fadin”Dr. Save my life Ummi na “Yafada kamar zai fitar da kwallah.DR.Abduljabar dake zaune yana duba patient yayi Saurin mikewa yana Fadin” Brr.Mu”Azzam meyasamu Ummi kuma”Shima yafada cikin Tashin hankali kafin yayi mishi nunu da dan gadon dake office din yana Fadin”Drop her here”Yafada yana kokarin taimaka ma Mu”azzam din.
Patient din Dr.Abduljabar yabawa hakuri ta jirashi awaje cikin gaggawa yafara gwaje gwaje dakuma kokarin farfado da Numfashin Ummi wanda yadauke gabadaya shiko Mu”azzam yakasa zama fadi yake”plz Ummina don”t do dis To me,inkika mutu rayuwata tashiga lahaula plz wake up nayi miki alqawarin bin dukka umarninki”Yafada cikin wata irin karyayyan murya lura Da Dr.Yayi baya cikin hayyacinsa sai ya kallesa yana fadin”Brr.Cool down Karka damu Ummi zata tashi bawani abu bane seriuos kawai taji Abunda yadan Firgitatane.So Abunda nakeso dakai kabani wuri in gudanar da aiki na plz” yafada kamar yana lallashinshi kuramasa ido yayi kafin yakada kai ya juya ya fice.
Sai da DR.Abduljabar ya kwashe fin awa kana ya fito wanda Mu”azzam ke kofar office din yana safa da marwa cikin tashin hankali ya rike Dr.Yana Fadin”Dr karka cemin Ummi bata tashi ba don Allah”Mirmishi yayi kafin yadafa kafadarsa yana fadin”is ok Brr.Mu”azzam Ummi tafarfado Cikin Nasara alluran barci nayi mata..Karka damu kamar yadda nafadamaka wani abu ne taji kota gani, wanda ya matukar razanata har yayi sanadiyar sumarta ammh yanzu ta farfado komai Normal insha Allah”ajiyar zuciya ya sauke yana fadin”Alhamdulillah…”Dr.Yayi mirmishi yana fadin”Ummi baxata mutu tabar mu”azzam ba saboda dayansu bazai iya rayuwa babu daya ba..Bantaba cin karo da soyayyar uwa da ‘da irinku ba anyway kuna burgeni sosai”yafada yana bubbuga kafadansa
Gyada kai kawai Mu”azzam yayi kafin yayi mgana Dr. Yace”yanzu zamu maidata dakin dazata samu hutu insha allahu zuwa yamma ko tomorrow morning zaku koma gida” Hannu kawai Mu”azzam yabasa yana Fadin”Tanque Dr Allah ya saka maka da alheri’jijjiga hannun nasa yayi yana fadin”Haba babu komai Nima Ummi uwata,Allah yakara lafiya.
Cikin abunda baifi minti goma ba har ankai Ummi dakin Hutu cikin wani kayatattacen daki mai kyau da tsari wanda sai ka rantse ba acikin asibitin yake ba,saboda yadda ya tsaru komai na bukatar rayuwa akwai shi cikin dakin..Mu”azzam yakasa barin Asibiti waya yayi wajen aikinsu yana fadin bazai samu zuwa ba Brr.Barau ya wakilcesa wajen gabatar da sharia na yau din.
Brr.Mu”azzam yakasa jirkawa ko nan da chan saboda hankalinsa bazai iya kwanciyaba sai yaga farkawan Ummi yana zaune acikin dakin kan kujeran dake gefen gafon..Hannunsa sakale cikin na Ummi wacce ke barci Numfashinta na zuwa na dawowa ga karin Ruwan da”ake mata yana shiga dis dis..Fuskarta ya tsurama ido lokaci daya idonsa yakawo kwallah ganin yadda Umminsa ta rame lokaci daya,gabadaya kansa ya kulle ya rasa mafita..Bai gama zurfafa Tunani ba yaji hanunsa dake cikin Na Ummi yafara motsi da sauri ya mike yana fadin”Ummi na…Ummi na…”yafada yana damke hannunta itakuwa Ummi sama Sama,takejin Muryan Mu”azzam idanunta sunfara budewa dishi dishi..shiko ganin tana ta mutsu mutsu yasashi ficewa da sauri zuwa office din Dr.Abduljabar yakirasa da sauri da hanzari yabiyo bayansa suka rantamo dakin koda suka shigo Ummi tafarka tana kokarin mikewaa zaune da hanzari mu”azzam ya karisa yana fadin”Ummi karfa kiji ma kanki ciwo baki da lafiya”yasa ka hannu zai rikota da dakamai tsawavtayi lokaci daya dacewa”Karka kuskura katabani Ibrahim…”Tafada cikin kaukkausan murya wacce tadan shake.
Ba Mu”azzam ba kadai ba, hatta Dr.Abduljabar cak ya tsaya da kokarin karisa kusa da ita dayake dominn Dubata Mu”azzam kuwa suman tsaye yayi yana duban Ummi fuskarsa tana bayyana damuwa karara dakyar ya iya bude baki yace”Don Allah Ummi kiyi hakuri ki yafeman..Kinga baki da lafiya kibari mu koma gida mayi mganan a tsanake”Yafada yana hada hannuwa dago kanta tayi tana kallonsa lokaci daya hawaye suka zubomata tace cikin wata murya mai cike da tsausayi”yanzu dakai za”a hada baki aci amanata ko Mu”azzam? tafada tana kallonsa da jajayen idanunta ya bude baki zai yi mgana ta dakatar dashi bayan tadagamai hannu tacigaba da cewa”Ka kyauta..Kuma nagode bisa hallacinka ..Kaje na bar ma su shettima kai, nikuma zan barka dasu zankoma kasata inda aka reneni wato gidan marayu tunda yanzu maraicin nawa yakara bayyana”Tafada tana fashewa da kuka.
Mu”azzam yakasa mgana illa zuciyarsa dake bugawa fat..Fat..Inda ace zai samu sararin kuka wlh dayaji dadi..Dr.Abduljabar yakallesu cikin mamaki kafin yabude baki yace”Brr.Mu”azzam meyake faruwa ne..? wani laifi ka aikatama Ummi duk da irin son datake maka take furta wa”innan kalaman?”Yafada cikin tsantsan mamaki.
Mu”azzam yakallesa idanunsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sun taso Radau..Ummi ya kallah wacce keta sharban kuka kamar me yama kasa mgana sai durkushe wa yayi yana jan kafa zuwa bakin gadon Ummi yana ta so yayi mgana ammh zuciyarsa datayi Nauyi yakasa mgana hannu yasa zai riko hannu Ummi ta matsa baya tana fadin”Ka fice kabani Wuri Mu”azzam bana son ganinka”Tafada tana kuka kara matsowa yake shiyasa takara saka ihu hade da tswa tace”Ka ficeman nace IBRAHIM..Wlh indai baka fita nizan fita nabar maka dakin..KA FICE KABANI WURI NACE”Tafada cikin dakamai tsawa gani yaki motswaa yasa tafara kokarin tsinke karin Ruwan dake hanunta da Sauri mu”azzam ya mikewa yana fadi cikin rawan murya”No Ummi zan..Zan..Fita..Na fita shikenan ko”Yafada kamar wanda yarasa hankalinsa jin muryansa tafara rawa yasa Ummi kallonsa tsausayinsa na neman mata tasiri shiyasa tayi saurin kauda kai kuka na kara kwacemata.,cikin hanzari Mu”azzam ya mike yafice Dr.Abduljabar yana kokarin mai mgana ammh ina har ya fice..Dr yayi tsuru kawai domin yashiga comfuse jikin sanyin jiki ya karisa kusa da Ummi yana kallonta kafin yace”is ok Ummi..Kibar kuka hakanan kinga baki da lafiya kina bukatar Hutu”yafada cikin kulawa Kauda kai Ummi tayi batayi mgana ba komawa tayi ta kwanta kafin tace”Don Allah,Dr. biman Mu”azzam kada kabarshi yatafi cikin wannan halin don Allah”Tafada cikin kuka Mamaki ma yahana Dr.Abduljabar mgana yana tsaye Ummi tasake cewa”Don Allah Dr..”Tafada tana kallonsa saurin gyada kai yayi kafin yafice yana mamakin wannan al”amarin mai daure kai.
Koda yafito baiga Mu”azzam ba cikin zafin Nama yafice zuwa haraban asibitin yana zuwa daidai motarsa na ficewa daga asibitin dafe kai Dr.Abduljabar yayi yana fadin”oh my god..Wai meke faruwa ne'”Nifa kaina ya daure’ ganin ba wanda zai bashi amsa ne yasa yasaka kai yakoma cikin asibitin bai koma dakin Ummi ba, wata Nurse ya umarta dataje ta dubata tamata alluran barci ko tasamu Natsuwa.
Shiko Mu”azzam yana Fitowa cikin tashin hankali ya karisa wajen motarsa Ushe dake cikin motan yaga fitowar oga kamar zai fadi cikin hanzari ya fito ya budemai motar yafada ciki lokaci daya yana fadin”Uche back to house..”Yafada cikin wata murya mai nemam agaji jin haka yasa sai da Ushe ya waigo yana kallonsa kafin yace”Oga..Are u alright..”Yafada yana fatan kar ace hajiya ta mutu..Ko bude ido mu”azzam baiyi ba Kuma bai da niyyar mgana shiyasa Uche juyawa yayima motar key suka fice duka zuciyoyinsu babu dadi.