UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Abun mamaki su karime sunanan haraban gidan nan cikin jimami jin hon yasa sani zabura ya bude get..Gani  motar yallabai tasawo hancinta cikin gidan yasa suka kara tsurewa..Ushe baigama parking ba suka isa wurin da sauri Falalu shi yabudemai yallabai mota yana fadin”Yallabai ya hajiya take da jiki”ganinsu tsatsaye yasaka Mu”azzam dan sakin Fuska ammh ina ya makaro domin ma”aikatan nasa sunfi kowa lakantan Uban gidansu.

Cikin rashin kuzari yafito daga cikin motan yana kallon fuskokinsu lokaci daya yana kauda kai..Dakyar ya kakalo mgana yace”Ku kwantar d Hankalinku Ummi tana lafiya ta farfado an mata alluran barci ne kinji…”Yafada yana wucewa ,da kallo suka bisa duk da yayafada musu ammh kuma zuciyarsu ta kasa yarda da Abunda yafada musu ba.

  Har yakusa shiga falon ya waiwayo yana fadin”Baba ku yi hanzari kuyi abinci mai Ruwaruwa Ushe zai daukeko keda lami da Uwani kuje ku kaima Ummi ku dubata'”Yana gama Fadin Haka yashige falon.

  Karime takalli Lami tace”Wai anya yallabai lafiya kuwa” lami ta sauke ajiyar zuciya tana Fadin”gaskiya akwak mtsala”Sani maigadi yace”Koma miye Allah ya kiyaye gaba kuyi hanzari kuje kuyi abunda yace,kada ya fito kuma baku kammallah ba”Jin haka yasa suka Rumtuma cikin gidan zuciyarsu ba dadi.

  Fanten wake sukamata wanda yaji hanta..Sai suka hadamata lemon kanka..Kayan Fruit suka diba kama Daga kankana,abarba Apple,lemo etc basu wani tsaya neman yallabai ba domin Tunda ya shiga ciki bai Fito ba, suna kammallawa suka hada cikin kwando suka sako mayafai Ushe na waje na jiransu suka shige mota suka Fice su falalu nabasu sakon Suyima Ummi sannu kan Suzo.

    Ushe yayi musu jagora har zuwa dakin da Ummi take,tana kwance idanunta na kallon Saman dakin,Sukayi sallama suka shigo,Tana jin Sallamansu tafara kokarin mikewa Uwani ce takarisa Da sauri ta rikota tana fadin”Sannu hajiya,yi ahankali”Tafada tana sakamata Pillow abaya yadda zataji dadin zama.

  Karime ta ijiye kwandon Tana ma Ummi sannu lokaci daya da lami suna mata yajiki,ushe ma dake gefe sannu yake jeramata tana amsa cikin sanyin jiki kallon su takeyi kafin tace cikin dasasshiyan muryanta”Sannunku da zuwa,daga ina kuke”tafada kai tsaye karime tace”Yauwa hajiya,daga gida muke,yallabai ne ya umarcemu da mu yi abinci mukawo miki”Jin sun ambaci Mu”azzam yasa jikin Ummi na rawa tace”My son? yana ina yanzu,don Allah kufadamin wani hali yake ciki”Tafada lokaci daya hawaye na zubomata bisa kunci.

  Cikin mamaki su lami suka kalli juna kafin Uwani tayi karfin Halin cewa”Yallabai yana gida hajiya shi da kanshi yabamu Umarnin dafa miki abinci mukawo miki”Ajiyar zuciya Ummi ta saki kafin tace”Alhamdulillah..”Tafada tana lumshe ido lokaci daya tana share hawaye..Cike da mamaki su karime kebin Ummi da kallo yanzu suka samo bakin zaren,na damuwar yallabai.

  Lami ne tace”Hajiya azubo miki abinci ko kuwa Fruit zaki sha”Shuru Ummi tayi kafin tace”Bar abincin nan Lami kubani Fruit kuyi maza ku koma gida,ku tabbatar da Son yaci abinci kada kubarsa ya kwana da yunwa don Allah”Tafada tana tsaresu da ido gyadamata kai kawai sukayi domin Suma kansu ya daure.

**

 
  Koda Mu”azzam ya shiga ciki dakinsa ya wuce direct,yana shiga ya sulale yafada bisa gado ko takalmi bai cire ba,kansa ne yamasa Nauyi lokaci daya yaji kamar hawaye ya zubomai dazaya samu daman Yin kuka daya samu saukin halin dayake ciki,yanzu ya zaiyi?Bazai iya sabama Ummi ba kuma bazai iya Watsama Baffa Shettima kasa a ido ba,Gabadaya ya rasa inda zai sanya kansa.

     Idanunsa suna lumshe ammh ba barci yake ba,kawai tsabar Tunani wayarsa dake cikin aljihu tadau kuwa cikin kasala da mutuwar jiki ya zura hannu ya ciro saboda yadda kansa yama Nauyi ko duba sunan baiyi ba domin Idanunsa sun masa Nauyi yasa yadaga kawai yakara a kunne.

    “Dan”Uwa..”Shureim yafada Jin muryan Shureim yasa Mu”azzam mikewa jikinsa na rawa yace”Dan”uwa ina cikin wani hali ina bukatarka,kusa dani”Yafada cikin Tashi hankali jin yadda Mu”azzam ke mgana yasa ya mike daga zaunen dayake gaban Hajiya yace”Dan”uwa,meke faruwa ne? muryan ka tanuna kana cikin damuwa”Yafada shima cikin damuwa hajiya dake zaune gefe takalli Shureim tana fadin”Kai lafiya kuwa? meyafaru da mu”azzam din”Tafada tana kallonsa.

  Shureim najin Abunda hajiya tace sai ya budemata Speaker wayar..lokacin mu”azzam Yana takan  rabtafamai na abunda ke faruwa,cikin tashin hankali ya kareshe da cewa”Dan”uwa ya zanyi? Ummi tace bata son ganina,kuma tace ita kasarsu zata koma bata bukatata yanzu batason ko kallon Fuskata”Yafada kamar zai fashe da kuka cikin tashin hankali Shureim yace”Innalillahi..Ashh Abu baiyi dadi ba”Yafada yana dafe kansa.

  Hajiya dake gefe wanda tagama jin komai tace”Shureim bani Mu”azzam din in yi mgana dashi”Tafada cikin kakkausan murya alaman Ranta yabaci kai tsaye ya mikata ta karba takara akunni tana Fadin”Mu”azzam Saurareni”Tafada ranta babu dadi,jin muryan Hajiya yasa mu”azzam sakin ajiyar zuciya yana fadin”Hajiyarmu UMMI ta tsaneni tace natafi na bata wuri bata bukatata, kan Abunda bani da yadda zanyi na hana Faruwansa”Tsaki Hajiya tasaki kan tace”mtsweee..Wai wata irin zuciya Suhaima take dashi ne? Ta girma ammh haryanzu bata bar sakarci ba,in ta koreka tana da wani dan ne bayan kai”Hajiya tafada ranta bace kafin tace”Ka kwantar da hankali ka yanzu Shureim zai daukoni mu taho zan ganta sai naji dalilin wannan Sakarcin”Tafada cikin dattako Mu”azzam yashiga jerama hajiya godiya bata kulasa ba ta mikama Shureim wayar tana fadin”ka shirya muje Abujan yanzu”Tafada tana kokarin mikewa,saurin yanke wayar yayi lokaci daya yana taimakamata.

   Kaya kawai ta chanza,sai mayafi data sanyo,Duk da haryanzu da Sauran ciwon kafan ammh dayake motace shima Shureim yasan zuwan Hajiyan shine masalaha,shiyasa agurguje ya shirya Sukama Zulaika sallama Suka dau hanya Shureim da kanshi yake jan motan.

Comment
Share
Vote

#Intelligent writer”s#
#Uwar mijina..!#
#HAFMEELART#
[18/08, 14:17] 80k: INTELLIGENT WRITERS ASSO????

???? UWAR MIJINAH..!????
        (Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)

       ALKALAMIN:JANAF????
        WATTPAD:JANAFNANCY

DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF

NOT EDITED

                       NO9

    “”””Basu isa ba sai gabda la”asar Shureim, Mu”azzam kawai yakira yafada musu lambar dakin da Sunan Asibitin,kai tsaye chan Suka Nufa,Sai da Ummi tagansu kwatsam lokacin tana zaune bisa gadon ancireta mata karin Ruwa tayi nisa cikin Tunani sai jin Muryan Hajiya taji tana fadin.

   “Suhaima wannan wani irin sakarci ne naji kin aikata”Cikin Firgita Ummi tadawo daga tunanin Tilon danta ganin Hajiya tsaye bisa kanta Shureim na gefe yasa tace cikin mamaki”Yaya..” yaushe agari kuma”tafada tana kakaro mirmishi Balla mata harara Hajiya tayi kafin tace”Kul karki kara cemin yaya Tunda baki daukeni da daraja ba,sau nawa zan Fadamiki Suhaima kidinga barin yaron nan, ya shiga cikin Danginshi,ke baki mantuwa kuma baki yafiya wani irin zuciyane dake da bazaki gane yanzu kinfi karfinsu ba ehe'”Tafada ranta bace Ummi ta kalli Hajiya kafin tayi mirmishin Takaichi tace”To yaya ki zauna kiji mana,kinsan mezasu min kuwa Mu”azzam fa suke neman Rabani dashi”tafada cikin zubar hawaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button