UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dagamata hannu hajiya tayi kan tace”Bazan zauna ba,domin bashi nazo yi ba,nazo ne namiki fada ki chanza Tunani saboda Abunda kika aikata ko a addininki bashi da kyau,Wayace zai Rabaki da Mu”azzam danki ne fa,wanda kika dauki cikinsa wata tara kikazo kika sha wahalan Nakuda,bayan kin Haifesa kika sha wahalan Renonsa har ya kawo iyanzu,kina tsammanin ko butulu ne shi zai manta dake? balle Yaron iya biyayyah yana miki sujuda ne kawai baya miki shin bazaki godema Allah ba..,Karki manta akwai iyayan da ko mutuwa zasu yi wlh basu isa su hana ya”yan su abunda sukayi niyyah ba,shinke baki bambamta dasu ba,saboda sonki da yake yasa baya son bacin ranki, yakasa fadamiki sai dai shi yayi ta zama da damuwa bisa ransa,so kike watara zuciyarshi ta buga saboda zafafan kalamanki akanshi..”Hajiya tafada tana dakatawa saboda tagaji da tsayuwa( da dai kicii gaba da tsayuwan waya gayamaki borno gabas take????)
Wuri ta nema ta zauna tana kallon Ummi dake kuka Shureim kuwa hajiya nafara fadanta yafice..Riko hannunta hajiya tayi tana fadin”Don Allah don Annabi Suhaima kibar Mu”azzam yayi Auren karfa ki manta ba mugun abu bane,Sunnar ma”aiki ne fa zasu dambaka,kuma in baki manta ba yanzu shettima yaga ishara da halin Rayuwa ke din dai da suka tsana, kece sanyin idanuwansu saboda keki ka haifanmusu dan” daya zama garkuwa garesu'”takareshe fada tana kallonta.
Ummi dai kuka take bilqqi da gaskiya Kafin tadago tana kallon hajiya ta furta cikin kuka”yaya diyar FADI ce fa,Kin manta yadda Fadi tayi sanadiyar wargaza farincikina duk da burina na zama da moodu har karshen Rayuwata”Takareshe fada cike da gunjin kuka,Mirmishi hajiya tayi kafin takara rike hannunta Tace”To Saime,Ita Fadin tana raye ne? ehe..Ai Allah kenan wanda ka raina shi zai maka rana wata rana”Tafada tana kallonta shuru Ummi Tayi tana kukan ta Hajiya sai bata kara mata mgana ta kyaleta tayi kukan nata.
Mikewa tayi tana gyara mayafinta kan tace”Kinga in har baki ji mganata ba wlh tallahi Shi kanshi dan “Dakike Tutiya dashi watarana ke da hannunki zaki kasheshi”Da sauri Ummi Tadago tana kallon, hajiya idanunta jajur ta furta murya adashe”Ni Hajiya..Zan..Zan kashe mu”azzam”Gyada mata kai tayi kan tace’Kwarai indai baki janye kalamanki na bakison ganinsa ba,kuma baki sama auren albarka ba, Shi zai jawo ki Sakamai damuwa aranshi har yayi sanadiyar mutuwarsa kamar yadda Fadi da shettima suka kashe moodu da Zaluncinsu”Kallonta Ummi keyi cikin nazari kafin tayi mgana Hajiya ta rigata da cewa”Karki ce komai kawai kiyi Fatan alheri..Kifara shiri Sati mai zuwa za”a daura aure kuma yataho da matarsa,ki Natsu kuma kiyi aiki da hankalinki kuma ko bakomai yar”uwansa ne”Hajiya tafada tana tafiya kafin takara cewa”Indai na isa dake..Kada naji wata mgana kuma,ki fadama Mu”azzam amincewarki ko hankalinsa ya kwanta,Ni na wuce daman Abunda ya kawoni kenan”Hajiya tafada tana kokarin Ficewa.
Ummi tace”Yaya yamma tayi ku bari sai gobe” A”a Hajiya tace kafin tacigaba da cewa”Gwara mu koma muda zamu dawo sati mai zuwa biki,Allah bamu alheri Yakuma kara lafiya”Daga haka ta fice daga dakin.
Ajiyar zuciya Ummi ta Sauke duk kalaman Hajiya basu shigeta ba, domin Tana ji aranta duk wanda yace ta zauna da Jinin Fadi ba masoyinta bane..Wlh bazata iya ganin mu”azzam ya Auri diyar Fadi har yayi mata ciki sun Haihuwa ba har abada zata tsani yaran ,wanda kuma ba fatan ta kenan ba akullum fatanta Mu”azzam yayi aure ya haifamata jikoki wanda zasu debemata kewanshi tunda shikadai gareta,ammh yanzu yaya tasaka baki wanda bazata ta taba juya baya ga bukatarta ba don Kamar mahaifiyarta take kallonta ammah har abada BAZATA TA TABA SON JININ FADI DA SHETTIMA BA.Kawai tabarma Ranta ayi Auren ammh har abada wanan yarinya sun kawota ne domin Itama ta dandana abunda suka dandanamata..”Da wannan Tunanin Ummi ta tsaya ammh duk da haka sai da ta koka saboda yadda zuciyanta ke harbawa in tama Tuna wai Mu”azzam dinta zai auri Diyar FADI.
Wata Nurse ce tazo dubata,kawai sai tace mata takira mata Dr Abduljabar, yana office sanda Nurse din take fadamai,Bai bata lokaci ba,ya isa ga dakin Abun mamaki,Ummi cemai tayi yakira mata Mu”azzam yazo yadauketa su koma gida ita ta warke”Hakika ko Dr Abduljabar yaji dadi kai tsaye yakira Brr.Mu”azzam yana fadamai sakon Ummi.
Mu”azzam dake kwance wani abu mai kama da zazzabi yarufesa kiran Dr.Abduljabar ya shigo wayansa jikinsa na rawa yadauka yana fadin” Dr hop dai ba jikin ummi bane yatashi?” yafada cikin Nuna damuwarsa dariya Dr Abduljabar yayi kan yace”No..Ummi ce tace kazo ku koma gida,wai ita ta warke” yafada yana kallon Ummin yana yar dariya.
Da wani hanzari mu”azzam ya mike yana fadin”Plz doc,stop dis joking kasan fa zuciyata zata iya bugawa”Dariya Dr.Abduljabar yayi kan yace”Wlh billahil azim da gaske nake,au baka yarda ba,to ga Ummi tafadamaka da kanta”
yafada yana mikama Ummi wayar karba tayi tana mirmishi tace”my son..”Cikin farinciki ai mu”azzam mikewa yayi yana rawan baki ya Furta”Alhamdulillah my Ummi is back..Ummi am on my way yanzu kinji i love u”Yafada bakinsa yakasa rufuwa, gyada kai tayi tana jin kwallah na taruwan mata tace”
“”Love u too..Son drive safely kaji”Tafada muryanta yafara chanzawa sai tayi Saurin mikama Dr.Abduljabar wayar itakuma tayi saurin fadawa tiolet din dakin tana danne kukanta..Bataso likita yagani,Shiko baima lura da ita ba, ya kashe wayarsa ya maidata aljihu bayan ya kashe wayan,lokaci daya yana fita daga dakin.
Shiko Dan Marayan Allah mu”azzam jikinsa na rawa ya fito daga daki cikin Murna da farinciki lokaci daya yana latso kiran Dan”uwa bisa wayan yana picking lokacin Suna hanya Yaji mu”azzam yace”Allah Ya iyamaka abunda ka gaza Dan”uwa”
“Amin Amin..”Dr,Shureim yake amsawa yana fadin”meyafaru dan”uwa irin wannam addu’a haka”? cikin Farinciki Mu”azzam yafadamasa sa cewa Ummi yanzu ta kira yazo yadawo da ita gida.
Cikin jin dadi Dr.Shureim yace”To Alhamdulillah Dan”uwa ga duk alamu tafiya tayi kyau,hajiyarmu tayi nasaran Tankwara Mana Umminmu”Yafada yana dariya lokaci daya yana kallon hajiya wacce ke kallonsa itama tana mirmishin jin dadin Suhaima taji mganarta.
Cikin Jin dadi mu”azzam yace”Bari kawai dan”uwa ganinan zuwa mu hadu kawai”Dariya Shureim yayi kafin yace”To sai dai in zamu wuce Maiduguri dauro maka aure Dan’uwa”Yafada yana yar dariya
Cikin Rashin Fahimta Mu”azzam yace”Banga ne ba”Shureim yace”Muna hanyar komawa Abuja hajiya tace mu juya kawai”Rike baki Mu”azzam yayi kafin yace”Abuja kuma i think sai gobe”Dariya Shureim yayi yana fadin”To miye ai babu komai Tunda kwalliya tabiya kudin Sabulu angon Wani sati”Yafada yana sheka dariya Bata rai Mu”azzam yayi yana fadin”kaidai dan iska ne wlh,nidai bama Hajiyata waya namata godiya.
Shureim na dariya ya mikama hajiya wacce itama ke dariya tana fadin”Wlh nan da ko wani satin mtsayinshi zai kamo naka,yaro”Mu”azzam dake jinsu yayi dariya yace”yauwa hajiyata Proud of u Barrister mu”Yafada yana dariya,Dakuwa tamai kamar yana ganinta tace” kaniyarka nan,dan nema kawai wato karfi da yaji kaida Shureim kun maidani kakanku ko”? tafada tana dariya.