UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL


    Ranar alhamis Hajiya Baraka ta iso ita da matar Shureim Zulaika tare shi Shureim din,wanda agobe zasu bi jirgi zuwa Maiduguri daura Aure..Ummi babu wanda tafadamawa to dawa ma take hurda zuwan hajiya yasa tama su karime mgana kan Suyi shirye shiryen abinci gobe nasu dana bakin maiduguri..

Sunji mamaki da Hajiya baraka ke fada musu gobene yallabai zaiyi aure”Abunda basu taba ji ba Ummi kuwa kauda kai tayi ranta na mata kuna,hakuri hajiya ta basu tare da cewa abun yazo agurgujene,shiyasa basu ji ba.

Abangaren mu”azzam ko baida wani shiri Brr.Barau kawai yafadamawa,sai Dr.Abduljabar,Shureim kuwa yazo da abokin aikinsa Dr.Haruna kurfi,Su kadai ne zasu tafi maidugurin gobe in Allah ya kaimu.

   Ummi kuwa tayi bakan ko mganar bikin ake bata sanya baki,shima mu”azzam din koda wasa bai taba kwatanta hirar da ita ba,yana kiyayewa ammh duk wani motsinshi Tafin Hannunta yake kar take kallonsa aransa tana ayyana abubuwa dadama wanda nikaina ban sani ba.

RANAR DAURIN AURE

  Rana bata karya saida Uwar diya taji kunya takowani bangare shirye shirye,ne ke gudana tun ma bangaren su Zahirah su abun da gaske suke don kuwa gida tuni ya cika da yan”uwa da abokan arziki..Mahgana itama tana chan danata gayyah ga kuma yakura wacce itace gayyah komai.

    Zahirah tafara fahimtan wani abu domin Duk inda ta gifta amarya ake cema gashi Yakura ta shiryata cikin wani ubansu less bayan tanadeta da lifaya,.Ita kadai adaki tana tunani domin ita tunda take bata taba yin kawa arayuwarta ba ita kadai take rayuwarts..Duk wani shagali da sauri suka farashi domin Shettima yace Yakura su zama cikin shiri ana daura aure mu”azzam zai wuce da matarsa.

  Abangaren Su mu”azzam kuwa jirgin karfe goma zasu shiga zuwa maid,shiyasa da wuri suka kammallah shirunsu suma anasu barayin sun safe su karime suka tsabtace gida suka fada kichen  domin hada hadan abinci Hajiya kuwa na lura da ummi ko jiya batayi barci ba tarasa wannan bakar zuciya irin na suhaima,yanzu ma tana kwance ko tashi batayi ba gashi ita hartayi wanka zulaika ma ta cakare abunta tashige cikinsu su lami suna aiki dayake sun santa babu ruwanta.

  goma Saura kadan Mu”azzam da Shureim suka shigo dakin Ummi wacce ke kwance cikin bargo hajiya na gefenta tana mata fada kamshin daya bugi hancin tane yasata dagowa luuu..Tayi da ido na ganin yadda mu”azzam yaci ado wata ubansu gezner brown ammh light riga da wando yar ciki,harda malummalum kansa dauke da wular zannah bukar,kafafunsa kuma cikin booth suke bayan hannunsa daure,da agogon azurfa mai kyau da kyalkyali yana daukan ido.

  Fuskarsa tana Fitar da wani Annuri na dabam,anko sukayi domin shima Shureim irin shigan dake jikinsa kenan, domin shiya yimusu Ankon., Ummi na ganin suna takowa gareta tayi maza,ta maida kanta cikin blanket saboda kukan daya taho mata..Tanaji aranta shettima yagama da ita duk abunda zatayi daga baya ne..Tana ji tana gani mu”azzam yadau kwalliya zashi daurin aure..kawai sai tafashe da kuka harda shessheka wanda har ya fito sunajin sautin kukan nata.

Da mamaki suka bita da kallo kan suyi mgana Hajiya ta musu nuni da kofa da  suFita kawai,mu”azzam baida zabi illa juyawa yana fadin”Ummi na ina bukatar addu”anki zamu dau hanya’Banza tayi dashi dole jiki asanyaye yabi Shureim wanda yaja hannunsa suka Fice.

Babu yarda ya iya..Yanaji yana gani ushe yakaisu Airport suna zuwa sanarwan Sunaye yafara gudana lokaci kadan aka kirasu suka shiga jirgin kafin a kammallah komai yahau sararin Samaniya ya fara lulawa MAIDUGURI.

Comment
Share
vote

#Intelligent writer’s#
#Uwar mijina…!#
#Janafnancy#
INTELLIGENT WRITERS ASSO????

???? UWAR MIJINAH..!????
        (Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)

       ALKALAMIN:JANAF????
        WATTPAD:JANAFNANCY

DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF

NOT EDITED

                  NO 10

     “””Awa uku suka shafe a sama,kafin jirgin ya saukesu a babban Filin jirgin dake birnin na maiduguri,Mu”azzam da kansa yakira Bukar yafada masa isowarsu wanda dama tun suna gida yafada masa zasu biyo jirgi In sun kariso azo a daukesu.

  Bukar da kansa yazo filin jirgin ya daukesu zuwa chan gidan nashi, daya kachame da al”umma mata da maza wa”inda suka zo daurin aure,babban Falon Na gidan Bukar nan aka saukesu wanda sukansu yan”uwan Bukar din da sukayi tozali Da mu”azzam din sai da suka raina kansu domin sunga tsantsan  kyau,ilimi da kamala tareda tsantsan kwarjini da dattako.,Ba shakka zahirah ta dace da samun gwarzon Namiji haka suke fadi duk wanda ya fito daga falon bayan sun gaisa,Bukar daganshi ya shiga cikin gida inda mata ke gudanar da sha”aninsu yayi ma mahgana mgana kan akawo masu Mu”azzam abinci kafin su wuce daurin auren,Jin isowar ango yasa gidan yadau guda lokaci daya.

    Kafin kace kwabo an cika gaban su mu”azzam da abinci Nau”i na dabam dabam sai wanda suka zaba,Shureim ya kalli Mu”azzam yace”Ango fa kasha kamshi,to ya ne zaka taba ne kafin mu wuce”yafada yana dagamai gira.

  Tsaki Mu”azzam yayi kafin yace”Sai dai kai,domin naga kamar kafini bukata”Yafada yana Cigaba da dannan wayansa,Dariya su brr barau suka sheke dashi suna Fadin”Shima yana kukan aure so ba cin abinci”Kara darawa sukayi kafin Shureim yacire babban Rigansa yana fadin”To Ango ayi kuka lafiya,yan”uwa ku sauko muyi mu harraka kafin kuma na anjuma”Yafada yana zama lokaci daya da bubbude kulolin gabansa,Sinasir ce sai na biyu Tuwon shinkafa sai Farar shinkafa.

  Sinasir suka zuzzuba da miyar Alaiyyahu wacce taji nama da manshanu suna ci suna zolayansa suna dariya,Shiko yama gefe ko kallonsu bayayi yana ta latsa waya abinsa Shureim ya kallesa yana tura sinasir abaki”Wai nace ba”Yafada yana kallon Mu”azzam wanda ya dago yana kallonsu.

  Ganin haka yasa Shureim yace”Amaryan ba nan ne gidansu ba”eh sai akayi ya”mu”azzam yafada cikin dage kai,Dariya shureim yayi kafin yace”yo ko gilmawarta banji ba,balle kamshinta kasan ance yan maiduguri badai kamshi ba”Yafada yana tauna kashi Dariya Dr Abduljabar yace”Kwarai su daman, da kamshi aka sansu”Kauda kai Mu”azzam yayi kafin yace”Sai ku shiga ciki duk wacce kuka gani tana kamshi itace amaryar”Yafada yana wani hararansu dariyan shakiyanci suka shekemai dashi sunayi suna dibam garan abinci shiko yayi musu banza.

  Ahaka suka kammallah kafin duk su share hannayensu da bakinsu da Tissue,babu dadewa sai ga bukar yazo yace su fito su shiga ciki su gaisa da goggonin Zahirah kafin su rankaya ,zuwa gun daura auren lokaci ya kusa,Cikin jin dadi suka mike mu”azzam na baya baya,suka iza keyarsa gaba koda suka shiga nan suka ga dangi kowacce taci adonta ammh fa sun dane jikinsu cikin,lifaya wanda ya burgesu shureim sun gaisa da kowa da kowa don kowani daki sai da suka shiga,kanwar bukar itace autansu Aisha sunanta suna cemata, Ashe ta fito da gudu da wani kasko ahannunta wanda yake cike da Rushin wuta ga turare yana fitar da hayakin kamshi tafara zagaye Mu”azzam dashi tana sakin guda,nan da nan guri ya kaure da guda da wake wakensu na chan sai abun yakoma burgesu shureim tuni suka fitar da wayoyinsu suna daukan bidiyon yadda mata suka zagaye mu”azzam kowanne rike da kaskon Turare suna mai Feshi da hayaki,tare da guda,dakyar dai suka barsa ya isa gaban mahgana wacce keta faman saka mishi albarka bayan tasaka hannunta bisa kanshi”Allah ya albarkaci Aurenku moodu da zahirah,Allah yayi ma rayuwarku albarka,Allah ya baku zuru”a tagari,Allah ya zaunar daku lafiya,ya kauda dukkan Fitina akanku..Yaasaka ace gwara da akayi”Tagama fada hawaye suna zubomata gabadayan jama”an gun suna amsa mata da Amin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button