UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Shikanshi mu”azzam jikinsa yayi sanyi, shima din da Amin din yake amsawa su shureim na tayasa,To dakyar da mu”azzam yasamu ya fice daga gidan saboda yadda akamai cha mata suna ta kirarin Zahirah tagama dace da sun gwarzon mazaje.
Suna Fitowa suka shisshiga motoci sai Famfari gidan Baffa Shettima inda za”a daura Auren,koda suka isa guri ya cika da al”ummah sai wanda yagani lokacin Da Mu”azzam ya fito daga mota wasu sun ma dauka Moodu ne saboda kamar da suke,sai daga baya suka fahimci shine angon,Baffa shettima yaci fararen kaya da Babban riga harda rawani bakinsa kuwa yaki rufuwa,wani masallaci dake kusa dasu anan aka shiga domin daura auren wani yaya ga bukar shiya, amshi auren zahirah a inda mai gayyah mai aiki baffa Shettima ya nema ma Dansa Mu’azzam,auren zahirah kan sadaki Naira dubu dari,shaidu sun hallara kuma an nema sun bada cikin lokaci Alkwarin Allah ya tabbata Tuni yan,sheda suka hau sanarwa.
*ALKWARIN ALLAH YA CIKA AYAU MU”AZZAM MOODU YAZAMA MIJI GA ZAHIRATU LAKADAN BA AJALAN…”
Saboda Farinciki Baffa shettima Rumgume Mu”azzam yayi yana kuka kamar karamin yaro,kowa yadauka kukan murna ne ammh shi anashi barayin ba haka bane tunawa yayi da dan”uwansa Moodu uwa uba,Fadi wanda duk sun kwanta dama,rashinsu babban illa ne agareshi maraici ya lullubesa,haka yakoma ya Rumgume Bukar yana kuka yana mai godiya,shikuma yana mirmishi kawai domin yanajin sa wani iri duk da yacika ma Shettima Umarninsa,.
Jama”a kuwa dadama zunde sukayi tayi suna cewa”Dole shettima ya makale yahada Aure,yaga yaro yazama mutum ga kudi,ga dukiya ga uwa uba kyau,bayan ya manta dimbin Muzgunawa da takuran Da Suhaima ta fuskanta sanda tazauna tare dasu,dayawan su sunso suji ya Suhaima zatayi in taji wannan al”amarin(Kusan mutane baka gadonsu ammh sana da gadon bakinka).
Achan cikin gida kuwa,Lokacin da masu sheda suka sanar da an daura Aure,kannen yakura dake daki tare da Zahirrah wacce ke zaune kamar mutum mutum,tafara fahimtar meke faruwa da ita ammh abunda ya daure mata kai,in Aure za”ayi mata waza”a daura mata, ita da ko tadi da saurayi bata taba yi ba,bata gama mamaki taji sun rufeta da guda lokaci daya suna mata ambaliyan Turare mikar da ita sukayi suka Fito da ita Falo suna Fadin “Takawarki lafiya Yarinya mai babban mtsayi”Suke fada suna mata tafi da ihu gefe daya suna busa mata hayakin Turare.
Tuni zahirah taji tafara Rudewa kafafunta suna hardewa idanunta sun ciko da hawaye fahimtar haka da Yakura tayi ne ya sa ta isa garesu tana fadin”Don Allah ku dakata da wannan gudan kunsan fa yata batason hayaniya” Tafada tana rikoTa ai zahirah naji yakura ta rikota kawai sai ta fada jikinta lokaci daya ta fashe da kuka tana fadi cikin Rawan murya”Da gaske..Ne…Ni..Ni aka ma Au…Re”Tafada hawaye suna karanyomata..kallonta yakura tayi lokaci daya itama taji ruwan hawaye kawai sai taja hannunta suka fada kuryan dakin harda Rufo kofa.
Zaunar da ita yakura tayi kafin tafara share mata hawaye tana fadin”Kibar kuka yata..Kinji!Farinnciki zakiyi da godiya Allah daya daga darajanki Ayau din kika zama matar aure mai Daraja”Tafada tana kallon kwanyan idonta,Naurau Naurau tayi da ido kafin tace””Taya za”a min Aure ban sani ba? kuma ma waye na aura? tafada kanta tsaye ammh cikin sigar yarinyata
Mirmishi yakura tayi tana zama kusa da ita tace”Karki damu yanzu badadewa ba zaki ga angon ki,kuma na tabbatar in kika gansa sai kin godemana saboda zaben da mukayi miki”Tafada tana,dariya Abun mamaki itama zahirah dariyar tayi tana Rumgumota take fadin”Ammh anan gidan zan zauna ko”Tafada bayan tadago tana kallonta,shafa kanta yakura tahau yi aranta tana ayyana yarinta har yanzu na damun Zahirah
Bata bata amsa ba sukaji gida ya rude da guda ana ma ango kirari gaban zahirah ya yanke yafadi takara makalkale yakura lokaci daya jikinta na rawa..Dan kallonta yakura tayi cikin tsausayawa kafin tace”Kinji ko ga angon chan ya kariso maza tashi ki kiga wanka bari na turo yagana takara shiryaminke nasan kila shettima ya bukaci ganinki”Tana fadar haka tazame jikinta,tafice tana share kwallan data biyo mata.
waje ta fito inda Su mu”azzam suke dangi sun yamaimai mayesa suna sakin guda dasa albarka duk inda ya gifta jinjina ne domin dai duk inda Mutum yake to mu”azzam yakai Cikin dakin yakura suka shiga suna gaisawa da baki,anata saka albarka da fatan zama lafiya yakura tayi tasaka albarka tana hawaye Lokaci daya tana kallon Mu”azzam batare da kowa yaji mai tace ba tadan sunkuyo tace”Suhaima ko ta amince”Kallonta mu”azzam yayi kafin yayi kayatattacen mirmishi yace”Ta amince domin da yarda ta nazo nan”Kallon ban yarda dakai ba yakura ta mai kamar zatayi mgana sai kuma tafasa.
Har suka gama gaisawa da jama”a basu ga ko keyar amarya ba sukuma basu tambaya ba,itakuwa tana cikin daki yagana tagama shiryata cikin wata shadda green doguwar riga wacce taji aiki bayan ta yaneta da lifaya fuskarta tana ta kyalkyali da haske ga kunshinta wanda ya haskata sai zallar yarintarta ta fito fili..Koda Yagana ta jawota zuwa falo har su mu”azzam sun Fice daga gida,fitowarsa yasa suka kara sakin wani guda na ganin yadda amarya tayi kyau kamar ba ita ba.
Suko su Mu”azzam suna Fitowa shureim ya kallesa yace”Kai nifa wlh nagaji wai dangin naku basu karewa ne”Yafada yana daure Fuska,shiko Dr Abduljabar cewa yayi”Wlh ni kafafuna sunfara zafi fa..Kuma gashi bikin naga kamar ba yan mata sai matan aure”mu”azzam dake jinsu yayi musu banza don shima yagaji gaskiya yana bukatar hutu,shiyasa ya nemo bukar ta waya,Kan zasu je su dawo.
Gidansu dake maiduguri suka nufa,suna zuwa daman akwai wa”inda suka saka suna kula da gidan,Komai yana nan a muhallinsa,shashenasu dai na da dasuna matasa,anan suka yada zango,kowa ya baje yana sauke Numfashi Brr,barau yace”ammh sai gobe zamu koma ko? don wlh ban iya tafiya ayanzu haka”Harara Mu”azzam ya wurgamai yana fadin”raggo kawai hala wani aiki kayi”Yafada sanda yake kokarin fadawa tiolet.Sukowa kowa yabaje bisa gado wai sun gaji mamakinsu kawai mu”azzam yayi kamar wasu mata.
Nan suka zauna har dare basu sake fita suna ta zencen bikin yan maiduguri har Dr.Abduljabar nace shima irin na brr,zaiyi nan fa zai makale dariya sukahau yimai suna mai shakiyancinsu na abokai.
Mu”azzam da kansa yakira bukar yafadamasa cewa ashirya da amarya da mutum biyu domin sun rigaya da sunyi buking jirgin karfe tara na safe zasu tashi,jin haka yasa bukar cemai babu damuwa insha Allahu,anan ne ma sukayi mganar kayan dakinta nan mu’azzam yace abarsu sai zuwa gaba,da haka sukayi sallama suna gama waya dashi ya kira Ummi almost 7misseds call ammh bata dauka ba dole ya hakura yakoma ya kira hajiya.
Hajiya tadauka suka gaisa tana tambayansu andaura aure lafiya”Ya amsa mata da Alhamdulillah kana ya zarce da tambayan Ummi nayakira wayarta taki dauka,Ajiyar zuciya hajiya ta sauke kan tace”Lamarin Suhaima sai addu”a mu”azzam wlh tunda kuka tafi bata fito daga daki ba,nayi nasihan nagaji nadawo fada,ammh duk abanza kuka kawai take tana ma Shettima Allah ya isa”Tafada cikin nuna damuwarta na abun ya isheta.