UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

   mahgana tafara fitowa kana yakura tafito rumgume da zahirah wacce ta sunne kanta tana digan hawaye Rikota hajiya tayi tana fadin”Allah sarki Zahirah Allah yasa a kulla alheri”Tafada tana rumgumeta,Dariya yakura tayi tana fadin”hajiya baraka ashe rai kan ga rai”Hajiya baraka tariko hannun yakura tana fadin”Uhum kedai bari yakura ya bayan Rabuwa kuma”yakura ta amsa da “Sai alheri hajiya ina Suhaima.

  “Hajiya tace”Tana daga ciki mu karisa “Tafada tana musu jagora ammh zahira na rumgome ajikinta su zulaika na gaba suna jera guda ta ko”ina,suko su Mu’azzam daganan, sukayi sallama da Dr.Abduljabar da Brr.Barrau suka tafi amotar Dr din Shi da Shureim da Dr.Haruna ne suka take ma su hajiya baya.

   Ummi dake kwance, kan gado kowani dakika na zuciyarta bugawa takeyi,tana ji sanda hajiya kefadama zulaika cewa amarya ta iso..Gabanta ya amsa lokaci daya jikinta ya dauki rawa hawayen takaichi da bakin ciki suka zubomata ta sanya hannu ta share mata,bata gama tunanin mafita ba ,taji bude get da karan diran motoci,bata kara tsinkewa da al”amarin ba sai da taji gida ya kaure da ihu,da gudan zuwan amarya Ummi dake zaune tayi saurin mikewa Jiri na neman kadata ammh ina zuciyarta suya take tana fadin”Yanzu ke suhaima Diyar fadi zaki bari tashigo miki gida.ehe..Kinmanta yadda suka taru suka ruguza miki burinki da rayuwarki gabadaya”Jin abunda zuciyarta ke sakamata ne yasa ta nufo kofa da niyyar fita jirin daya debeta ne yasa tayi saurin dafe bango lokaci daya dadafe kanta nan ta sulale tana kuka mai cin rai tana fadin”Allah ya isa tsakanina dakai Shettima kadade kana cutar da zuciyata *WLH NI SUHAIMA NAYI ALQAWARIN DAUKAN FANSA AKAN KA,TAKUMA HANYAR DAKA,BIYOMIN,ZAN RAMA”Tana fadi tana dukan kanta da hannuwanta tana kuka kamar wata zararra.

     Suna zuwa kofar shiga babban falon hajiya tayi ma zahirah rada akunni tana fadin”Ki shiga da kafar dama,zahirah bayan kinyi addu’an fatan zaman lafiya agareki”Jin haka yasa tafara karanto addu”a tana kuka kafin su shiga falon wanda daman babban falo ne mai girma da tsari wanda yake dauke da kujerun royal chair har seti biyu,golden colour wanda sukayi ma falon kwanya bayanshi sai wani kafet mai kama da auduga wanda da kasanya kafa zakaji kafarka Ta, lume aciki,sai wani tafkeken Tibin bango daya kusa cinye rabin falon daga yamma kuma wani babban dining area ne wanda yaji wani ubansu Dining table wanda akallah mutane fin goma zasu kammallu agun.

      Daga gefe kuma wani korido ne wanda da ka shiga zaka ci karo da wani babban daki ciki da falo wanda cikin nan store,duk wani nau”in abinci yana ciki,sai falon inda nan ne madafi ma’ana wajen dafa abinci wanda yaji kayan wuta na amfanin yau da kullum,inka fito kuma dakuna uku ne ajere,na su karime ne duka.

  in mutum yadaga kai sama kuma mattakalan bene zai ci karo dashi,kana hawa zaka tarar da dakuna biyu kachal wanda nan ne shashen Ummi mai gayyah mai aiki..Daki daya bedroom ne,kawai da tiolet daki dayan kuwa babban falo ne mai dauke bedroom da tiolet harda kichen,Ummi tana zaune ne cikin one bedroom ne mai babban falon tabarshi ne in tayi baki kamar hajiya wanda ko wannan zuwan nan ta sauka.

    In ka kara saukowa kuwa akwai wani korido dayake kallon saman Ummi,dakabi nan sai sashen mu’azzam dauke da babban falo da bedroom da tiolet,indan ka fito kuma daga gefe ne sai ga wani daki shima dauke yake da falo mai 2 bedroom aciki harda kichen.

  Shi Naga hajiya tanufa tasaka makulli tabude, tana fadin”To amarya ga dakinki ki shiga da kafar dama”Yakura ta rikota tana tayata addu”an kafin su sanya kai cikin dakin wanda ke tashin kamshi ko”ina agyare yake falo ne,dan madaidaici mai dauke da wasu arnan kujeru royal chairs purple ne masu kyau sai wani capert daya mamaye duka dakin wanda taushinsa ya wuce misali,wani mamaken talabijin ne ke ta aiki shi kadai sai center table wanda ke tsakiyar dakin,Yakura da mahgana sakin baki sukayi suna bin,ko”ina da kallo,basu gama kallo ba sai suka dangana da cikin bedroom din wanda shima komai na ciki purple ne, shima ya kawatu da Royal bed da wani makeken wardrope da  madubi wanda ke shake da kayan ado na mata  dama, kowani daki agidan agyare yake da kayan more rayuwa.

  Kan gadon dayaji lafiyayyan zanin gadon aka ijiye zahirah wanda kanta ke dunkule cikin lifayanta ammh kallo daya zakamata kasan yarinyace karama ,haka suka karime ke fada bayan sun Fito daga dakin,nan fa suka shiga jera musu abinci kala kala wanda sukayi musu hajiya keta rawan jiki dasu,sallah suka farayi kafin su zauna suna cin abinci bayan hajiya tabasu wuri,Yakura da mahgana suna ta fadi zahirah tagama sa”a ammh UWAR MIJINTA itace babban mtsalanta.

    mu’azzam kuwa,da Shureim bangarensa suka fada sukayi wanka gado suka hau suka kwanta domin sun gaji jiki na bukatar hutu,shima kafin kace me dukkansu barci ya kwashesu,shiko mu”azzam da ,zullumi yayi barci saboda rashin ganin giftawan Ummi,kuma baisamu kebewa da hajiya ba balle yayi mata mgana.

   Hajiya kuwa falo suka dawo ita da zulaika,suna hiransu ammh ranta abace yake saboda abunda suhaima tayi mata,tun jiya tafita batunta saboda tun tafiyar su Mu’azzam take bata baki ammh suhaima takiji wuni tayi adaki,bata fito ba shiyasa yau din hajiya ko mgana bata mata ko dakin ma bata shiga ba,aranta tana fadin”Sai dai ki kashe kanki don ko ga amarya nan tazo”

  Kamshin Turaren da sukaji ne yasa suka kalli saman Ummi ce ke saukowa cikin takun isa sanye take da wata shadda gezner, doguwar rigar golden colour,wacce taji aiki sama da kasa,ta daura dankwalin bisa kanta bayan ta tamke gashinta,wuyanta sanye da sarka zinare da kunnenta harda hannuwanta kafafunta kuwa sanye da wani Vine ne mai dan Tudu sai mayafi data yafo mai dan girma.

  Fuskarta babu fara’a ko kadan duk da ba wani kwalliya tayi ba ammh kyau xalla ya bayyana,saukowa take cikin takunta na isa,hajiya da zulaika suka bita da kallon burgewa don sun shaida Ummi fa macece ta nunawa ako”ina.

  Ta iso falon lokaci daya tadan saki Fuska tana fadin”Sannu da gida yaya” mirmishi Hajiya tayi kan tace”Hoho..Hajiya suhaimar shagali kin gama fushin naki kin fito'”Dariya kawai tayi tanazama Zulaika dake gefe tana gaisheta ta amsa tana fadin”Lafiya kalau zulaika ya hidima kuma,Allah ya saka da alheri”Zulaika ta amsa da Amin.

  Hajiya ta kalleta tace””yan maiduguri fa sun iso dazu, mun barsu suna cin abinci ne”Tafada tana kallon Fuskanta Yamutsa fuska Ummi tayi kafin tace”uhm..”Kawai kauda kai Hajiya tayi kafin tace”Zulaika dan bamu wuri don Allah”Tashi zulaika tayi tanufi barayin su lami dake chan kichen suna shirye shiryen dora dinner.

   Hajiya takalli Ummi tace”Karki sake ki fara ma Suhaima wannan ba girman ki bane, Rama cuta ga wanda baiji ba baigani ba'”Ummi takauda kai kafin ta kago mirmishin dole tace”Allah bakomai yaya..Kawai nakasa kauda abun araina ne balle har na manta” hajiya tace”Hakuri zakiyi ki kuma tuna Allah ma muna masa laifi ya yafemana to kema kiyi koyi da musulman kwarai ki yafe suhaima don Allah”
     

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button