UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Godiya yakura tayi mata,.mu”azzam ne yayi gyaran murya yana fadin”Direba fa ya iso,tundazu yana jiranku”Jin haka yasa karime daukan musu kayan zuwa farfajiyan gidan,ai zahirah data ga da gaske ne tafiya zasuyi ai sai ta kwakumesu tana kukan zata bisu tun yakura na lallashinta hartagaji,Ummi dake gefe takaichi ya cikata batason sadda tace”Ke…”Cikin tsawa ai da hanzari tadago jajayen idanunta tana kallonta harara ta sakarmata kan tace”Dawo ki zauna makira,ai zama yazama dole tunda kika yarda aka daura auren”Tafada tana nuna mata hannu.

  Jikin zahira na rawa ta saki yakura hawaye na bin Fuskanta takoma ta zauna,suma cikin hawayen idon suka bita da kallo lokaci daya suka daga mata hannu suna fadin”sai wani lokacin yahna”da sauri suka juya barinma yakura da kuka yazomata,har suka fice daga falon ba wanda yakara waigowa,suna fitowa ansaka kayansu amota sallama kawai sukayi da mu”azzam bayan yabasu dubu hamsin gakuma kudin mota dayabama,ushe wanda yace ya tabbatar ya sakasu a mota tukun,cike da kewa da tsausayi mai girma azuciyarsu Motarsu ta fice daga gidan.

  Shima yadade tsaye jikinsa amatukar sanyaye kafin yaja jiki yakoma falon,yana shiga yaga zahirah durkushe gaban Ummi ko kwakwaran motsi takasa itakuma tana ta kada kafa ita kadai tana huci,ganin haka yasa ya sulale zai shige barayinsa sai ji yayi Ummi ta kira sa”  IBRAHIM.. tafada cikin kakkausan murya.

Comment
Share
Vote

         Jamcy bby
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
   (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

      Alkalamin:JANAF
      Wattpad:Janafnancy

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

              NO 13

       Karisowa tayi lokaci daya tana kafesa da ido,Saurin basarwa yayi da razanar da yayi yana fadin”Wlh Ummi wani fayel na manta shi ya dawo dani”Yafada yana daukan fayel din, kallonsa tayi kamar zata tanka sai kuma ta fasa kan kujera ta zauna batare da tayi mgana ba,shima ficewa yayi yana fadin”Sai na dawo Ummi na,da lebe ta amsa tana rakashi da ido.

    Zahirah ko tana shiga daki tasaki ajiyar zuciya lokaci daya kuma tana sakin mirmishi data tuna sanda tayi mai Wurgi da fayel saboda tsoron Ummi kan kujera tafada tana lumshe ido tana tuno Fuskar Mu”azzam lokacin daya sakarmata idanunsu lokaci daya taji wani yanayi yana shiganta batason kallon idanunsa saboda suna rikitata ainun,kara gyara kwanciya tana lumshe ido har barci ya kwasheta bata sani ba.

Sai wajen azahar ta farka gabanta na faduwa,kada yazo Ummi ta nemeta sallah kawai tayi tafito falon,Ilai kuwa da Ummi taci karo da ita zaune afalon,cikin rawan jiki ta zube tana gaisheta Ummi ta bita da kallon mai kama da harara,kafin tace”Ke dama kina ciki tun dazu,uban wa kika barwa sauran aikin”Zahirah tayi saurin cewa”A”a sallar na shiga nayi Ummi..”Tafada zuciyarta na tsinkewa,tsaki Ummi tayi kan ta kauda kanta ganin haka yasa zahirah mikewa tawuce kichen Ummi ta bita da kallon wani takaichi na kulleta kamar tatashi ta shakota takeji  gyara zama tayi tana,fadin”Allah ya isa Shettima cuta kam angma cutata.

  Ranar matare dasu karime ta wuni,sai da mangriba tayi kana,ta tafi dakinta ta daura alwala tayi sallah dayake taci abinci dasu karime,kallo ta danyi kan akira issha”i tana idarwa,tabi lafiyan gado saboda tagaji sosai.

Washegari

   washegari takama Friday ce,tun jiya Ummi tafadamai yau Zaria zata ta duba Hajiya dakuma yimata bangajiyan biki,Tun safe ta kammallah shirinta Ushe yayi ma waya kan yazo yakai Ummi dayake yau bazai Fita Office ba,har Ummi ta tafi zahirah na daki bata sani ba,domin tunda tatashi tayi sallar Asuba,takoma wani barci mai Nauyi ya dauketa wanda ta kasa tashi sai wajen 9 tafarka tana salati gabanta ko yafadi saboda Tsoron Ummi agurguje tayi wanka ta saka riga da sikat na wani less ja da baki,hijabinta ta saka ta fito falon ganin bakowa ya sakata sum sum ta wuce dakin su karime,suna ganinta suka hau gaisheta,ta amsa tana fadin”Yau na makara,Allah sa Ummi bata nemeni ba”Kallonta karime tayi kan tace”sha kuruminki Yata Yau Ummi tafiya tayi,Zaria taje tun safe”Wani siririn ajiyar zuciya Zahirah tasauke ranta yayimata sanyi sai ta ji tasamu Natsuwa,nan ta shige cikinsu suna hira.

   Tashi tayi ta hau sama ta gyarama, Ummi daki kafin ta sauko tafara kokarin gyara falon tana cikin goge Tibin dake jikin bango Falon ne taji gyaran muryansa,wanda ita tuni tabada amanna ga aikin datakeyi,Saurin juyowa tayi sai taci karo dashi cikin riga da wando kaftan Deep blue kansa babu hula kafafunsa ma wani takalmi ne budadde,hannunsa sanye da agogon na kamfanin Rado,duka idanunsa ya sakarmata ayayinda duka hannuwansa ke cikin aljihun wandonsa.

  Ganin ya tsaya yana kallonta yasa tayu Saurin dukawa tana fadin”Ina kwana ya Mu’azzam”Kallonta yayi cike da mamaki kan yace”Waya saka ki wannan aikin? yafada muryansa na nuna alamun baiji dadi ba,dukar dakai tayi kafin tace”Ni nasaka kaina..”,tafada cikin dakewa kuramata ido yayi,tayi Saurin dukar dakai saboda yadda takejin idanunsa akanta.

  Bata rai yayi kafin yatako zuwa kan kujera zama yayi yana kwalama karime kira”Baba..”Yafada cikin muryansa mai amo da burgewa,Karime dake daki ta amsa ta fito jikinta na rawa,ganin zahirah Durkushe agaban yallabai yasa jikinta yafara rawa,itama durkushewan tayi tana Fadin”Gani Ranka ya dade,Allah yasa ba laifi nayi ba”Kallonta yayi fuskarsa babu wasa yace”Baba waya saka yarinyarnan goge goge,”Yafada yana kallonta.

Daburcewa tayi tadago tana kallon zahirah wacce tayi mata wiki wiki da ido,dukar dakai Tayi kafin tace”Um….”A”a ni fa na saka kaina ko Mama”Ta katse Karime lokaci daya tana kayfamata ido,Karime tace”Eh..Eh hakane ita tasaka kanta wai tagaji da zama haka”Tafada tana dukar dakai saboda batason kallon Fuskar yallabai balle yagane tayi karya.

Shiko tuni ya ganosu,har kayftamata idon datayi yana lura dasu,mirmishin gefen baki yayi kafin yace”Ok yanzu nace ki karba aikin,ki karisa kuma daga yau kada ku sake bata wani aiki mai Nauyi,saboda batayi girman dazata dauka ba”Yafada yana basarwa Da toh karime ta amsa kafin ta karbi aikin Tafara karisawa,shiko wayansa ya fiddo yahau latsawa itako Tana gefe kanta duke tana wasa da adon leshin dake jikinta ta wutsiyar ido yake kallonta aranshi yana mamakin wayo da kuma hankalin yarinyar yasani sarai Ummi ce tabada Umrnin ta dunga yin wannan aikin ammh har ta san Tarufe bata so yaji,lokaci daya yaji Yarinyar ta burgesa matuka kuma ya yaba da hankalinta.

Sunan zaune jugum har karime tagama abunda zatayi ta fice,ganin Fitan karime yasa itama ta mike sum sum zata koma daki azatonta baya kallonta hankalinsa na bisa waya,kawai taji yace”Ina zaki? ai ban sallameki ba,dawo nan ki zauna”Yafada still idonshi na bisa wayar jikinta asanyaye ta dawo ta zauna ammh kan nan na duke,kallonta yaketa Wutsiyar ido tsaf lokaci daya ya karemata kallo doguwace siririyace bata da kiba,fuskarta doguwace mai dauke da idanunta ma tsaikaita,sai dan bakinta daidai misali babu abunda yafi burgeshi da ita sai zanenta na bare bare dake gefe da gefe kumatunta,sun mai kyau sosai har baisan ya shagala da kallonta ba,har sai da taji daga jikinta ana kallonta ta dago kanta karaf,suka hada ido,dashi,Kuramata ido yayi itama sai taji Takasa dauke idanunta akansa tanaji kamar wani abu ke zagaye duk ilahirin jikinta idanunta Tuni sukafara tara kwallah,lokaci daya taji kamar ana mata waiwayi, Saurin kauda kanta tayi zuciyarta na tsinkewa aranta tana fadin”Yana da kyau…”Mirmishi yayi still yana kallonta kan yace”Ya kewar gida,nasan kina kewan su ko” cikin sanyin murya ya furta hakan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button