UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jin haka yasa tadago tana kallonsa kan tadan murmusa kawai batayi mgana ba,kallonta ya sakeyi yaga tana ta mirmishi ita kadai,shima murmusawa ya sakeyi kan yace”Hop yanzu kindaina kuka ko? tunda nan din ma gida ne,ga Ummi gani kuma komai kike bukata ki tambayemu zamu yi miki kinji”Yafada idanunsa na kanta dagowa tayi ganin yana kallonta yasa ta gyadamai kai kawai tadan mirmishi.

  Mamaki ya kamasa baisan sadda yace”Baki mgana ne? ko nine ake ma rowan muryan”Jin haka yasa ta girgiza kai kafin ta bude baki tace”Ina yi mana..”Tafada kamar ansata dole,Jinginar da kansa yayi bisa Cussion yana fadin”To kidaina mun mgana dakai Juz open ur mouth and Talk to me..”yafada yana lumshe ido,itakuwa bakinsa ta kurama ido tana kallon yadda yake magana,jin batayi mgana ba yasa ya bude ido karaf ko yakamata tana kallonsa,kunya yakamata ta dukar dakai tana rufe fuska da hannuwanta.

   Shi dariyama take bashi,kallonta yayi yana Fadin”Kina son mkranta..”Jin abunda yafada yasata saurin dagowa lokaci daya tana washe baki,har hakoranta suka bayyana tare da dimple dinta mai karamata kyau,shagala mu”azzam yayi da kallon tsabar da kuma inda mirmishi hade da dariya yakema mace kyau,Masha Allahu kawai yake Furtama shima baisan yaushe yake kallonta ba,haka kurum yakejin dadin kallonta tana dariya.

“Makaranta..Ina so yaya,zaka sani ne”Tafada cikin nuna abun na ranta,rausayar dakai yayi kafin yace”eh mana zan sakaki indai zaki maida hankali,agida ajinawa kike? yafada yana kallonta gyara zama tayi kan tace”SS1 nake kafin acireni..”Tafada cikin Rauni,kallonta yayi kafin yace”Meyasa aka cire ki..? kallonsa tayi kafin idanunta su ciko da hawaye tace”Ba..Ba baffa bane yace nan garin xa”a kawo ni ba,kuma wai zaka sakani kowacce makranta nake so,wai haka”tafada da sigar yarinyata lokaci daya ta goge hawaye da dayan hannunta.

  Gyada kai yayi yana fadin”Eh mana zan sakaki mkranta insha Allahu zakiyi karatu har ki gaji da kudina,kuma da aljihuna nayi miki alqawarin rayuwa mai inganci matukar kika kasance mai hakuri ga dukkan al”amuran da zasu gabato mana tsakanin ni dake'”Galala tamai da ido alamar bata gane ina ya dosa ba,jinjina mata kai yayi kafin yace'”Kan Ummi na,nasan kinsan komai basai nayi dogon zence ba,don Allah kiyi hakuri da dukkan abunda zata miki,na lokaci ne,kuma banison kowani yazo kinunamai abunda ke faruwa plz and plz keep d screet mu kadai kawai,duk da abunda kikayi, dazu ya tabbatarmin bazaki bani kunya ba”Yafada yana kallonta,ga mamakinsa kayatattacen mirmishi ta sakarmai kafin tace”Indai wannan ne kada kaji komai,Ummi kamar Uwa take aguri,duk abunda zatamin bana ganin laifinta,fata Allah yasa ta canza ta gane gaskiya..”Tafada muryanta tafara rawa kawai sai ga hawaye sun zubomata,Kallonta Mu”azzam yayi yana mamakin kaifin basiran yarinya at her age haka,bata Fuska yayi kafin yace”to miye na kuka kuma? ke wai don Allah na tambayeki kuka bai miki wuya ne,koda yaushe kina cikin kuka”Yafada yana tsuramata idanunsa.

  Girgiza kai tahau yi,hankicif dinsa dake aljihunsa ya dauko ya mikamata yana fadin”Kinga Wipe ur Tears..Bani son kuka nan,daga yau'”Karba tayi tana share hawayen dashi kallonta yake yana ayyana abubuwa dadama,bai samu zarafin mgana ba,wayar dake hannusa ta dau kuwwa..Sunan Ummi ya bayyana kan Screen din bai tsaya,ba ya mike bayan ya dauki wayan yana Fadin”Ummi na badai kun isa ba”Zahirah jin an ambaci Ummi tayi hanzarin mikewa bata gama Fahimtar waya bace tafada daki da Sauri dauke da hanki din daya bata jikinta na rawa,itafa ko mala”ikan Mutuwa bata tsoro kamar yadda take tsoron Ummi.

  Da ido ya bita yana mamaki yadda take tsorata in taga Ummi,ko taji sunanta,bai wani tsaya tsananta Tunani ba yawuce barayinsa suna cigaba da waya da Ummi,koda suka gama waya yana duba agogo yaga lokacin jumma”a har ya kusa,baki ya rike yana mamakin yadda ya biyema yarinyarnam har yana neman makara zuwa masallaci,alwala ya daura kan yasaka hulansa ya Fito,su Sani da Falalu suna ta kwasan gaisuwa,amsawa yayi cikin Fara”a kafin yafada mota,yau mazajen da kansu sukayi Driving Sani ya budemai get ya fice.

  Itako Zahirah adaki murna ta cikata Ya mu”azzam yace zai sakata mkranta duk sanda ta tuna da haka sai tayi dariya ita kadai,haka kurum ta nanike ma Hanki din nan,Ta shinshinashi yafi akirga kamshin Turarensa Na Azzaro Visit,shi yakemata dadin shaka,takasa ijiyesa,saboda kada kamshi yayi nesa da”ita tana idar da sallah ta haye gado hanki din,na kan kirjinta tana shakar kamshin barcin yayi awon gaba da ita,cike da mafarkin Dan Ummi, MU’AZZAM

    Mu”azzam bai dawo ba sai dare,koda ya dawo Tuni zahirah tadade da yin barci,yau tasamu sake,batayi aikin komai ba,su karime kota matsa basa bata,sunce ta huta tunda Ummin bata nan,abinci kadai taci tabi lafiyan gado,ammh just imaging tana rumgume da hanki din Mu”azzam???? Zahirah kar ki saka kanki cikin wahala,wlh Ummi zata iya kasheki ni ba ruwana????
   

      Shima din a koshe yake Coffea kawai yasha yabi lafiyan gado,dayake sunyi waya Da Ummi tace hajiya ta riketa sai ta mata Weeked kana zata dawo,sai lokacin tafado mai Arai,mirmishi yayi shi kadai daya Tuna shirmenta,Fuskarta na dawomai lokacin datake dariya,da Tunaninta shima ya kwanta wanda ya rasa dalilin haka,ammh sai ya barshi a tsausayinta ne ke dawainiya dashi,da kuma yadda zai cikama yarinyar Burinta don ya lura tana matukar son karatu aranta.

  ***

  Da garin Allah ya waye,Zahirah an samu sake barcinta tasha ta hantse,don Tunjiya su karime suka sanar da ita,tunda Ummi takai dare to, bazata dawo ba,shiyasa bata damu ba sai 9 ta tashi,wanka kawai tayi ta gyara shashenta,wata doguwar riganta ta saka ta Atamfa,wacce cikin kayan da Bahna dinta yamata ne,ta daura dankwalinta ta zubo da gashinta baya,Falo ta Fito tana tafiyanta cikin sanyi,mu”azzam dake kan,Dinning yana breakfasat Tun fitowarta kamshin Humranta ya daki hancinsa,ya lumshe ido yayi, kafin ya dago yana kallonta itabatama Lura dashi ba,direct ta wuce zata shashen su Karime,muryanshi taji asama yana kiranta.

  ZAHIIRAH.. cikin husky voice dinta Tsam tayi da Ranta saboda yadda Sunan yadaketa,sai taji duk duniya babu wanda ya iya kiran Sunanta irinshi,waigowa tayi Asanyaye Tadora idanunta bisa kanshi wanda yake zaune yana karyawa,yana sanye da bakin wando da wata farar Riga na kamfani Armani,gashin kansa ya kwanta yayi kuf,Fuskarsa tana Fitar da wani Annuri.

Kwarjini yayi mata shiyasa takasa karisawa,sai shine yace”Ki kariso mana..”Yafada baya kallonta cikin sanyin jiki ta kariso kusa dashi,ammh kafafunta suna hardewa kamar zata fadi,basarwa yayi yana jamata kujera yana fadin’Be carefull,Set here…”Yafada yana nunamata gun zama a dofane ta zauna tana wani sunne kai,ta gefen ido yake kallonta,kafin yace”Ba gaisuwa..”jin haka yasa tayi saurin zamowa tana fadin”Ina kwana..”Amsawa yayi da “Lafiya,ya kika kwana”Da lebe ta amsa,ganin yadda bata natsu ba shiyasa ya mike yana fadin”Ki karya..”Daga haka yatashi ya karisa Falon ya fada kan daya daga cikin kujerun falon,yana dora kafafunsa kan center table  Din ,dake kusa dashi,ammh hankalinsa yana gun zahirah,yana kallon yadda take komai kamar mara lafiya,tea kawai tahada sai buredin wanda aka soya da kwai,shima din cikin sanyi takeci,kamar batason ci,yana lura da ita,Aransa yace dole ma ki zama wata lazy baki cin abinci,tashi yayi batayi Aune ba,sai ganinsa tayi akanta ya dauki Filet ya zubomata Ferfesun kaza,ya ijiyemata agabanta Filet din Buredin da kwan,ya dauka bayan ya sake lodamata,bai kalleta ba yace”Oya Eat..’Yafada ba alamar wasa bayan yaja kujera ya zauna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button