UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  Atare sukayi mirmishi lokaci daya karime tace”Ai ni yadace na duka miki ranki yadade ni mai hidinta miki ne saboda haka ina kasa dake”Kallonta Zahirah tayi kan ta sakin mata mirmishi tace”A”a kowani bawa daya yake da bawa dan Uwansa Ko awajen Allah sai wanda yafi tsoronsa..”Tafada ckin sanyin Muryanta.  

  Cikin Jin dadi karime tace”Hakane Ranki ya dade”Tafada tana kara kallonta aranta tana mamakin hankali da Natsuwar yarinyar,kallonta Zahirah tayi kafin tace'”Ki zauna mana mama”Girgiza kai Karime tayi tana fadin”A”a bazama nashigo yi bafa,Hajiya ce tace nayi kiranki”Jin an ambaci hajiya,yasa Zahirah ta kalleta da Sauri tace”Um..mmi..”Bakinta na rawa cikin mamaki Karime ta gyada kai.

  Ai da sauri Zahirah ta shige bedroom Jikinta na rawa ta dauko Hijabi ta sanya tana Fadin”Muje mama kada Ummi taga Mun bata lokaci”Tafada ckin Rudewa lokaci daya kuma jikinta narawa,batama jira cewar karimen ba ta rigata gaba,jikinta da zuciyarta suna rawa lokaci daya,don ko Sunan Ummi taji an ambata sai gabanta ya fadi.

  Zahirah na gaba,karime na bayanta,suna zuwa gabda Ummi Zahirah ta noke Karime ta rigata isa ga Ummi ta zube tana fadin”Gata nan Hajiya..”banza dasu Ummi tayi sai zuwa chan tadago kanta ta kalli karime a sakarce kan ta waiga tana kallon Zahirah wacce ta rakube jikin kujera tana rawan Jiki,tsaki Ummi taja kan tace”Lalle yarinyar nan,wato kina kwance acikin daki kina jira,ubanki ya girki yabaki kici ko” jin haka yasa karime ta rude ta dago ta kalli Ummi sai taga tana hararan Zahirah wacce harta fara Ruwan hawaye.

  Ummi tayi kwafa tace”To saurareni da kyau babu bawanki acikin gidan nan,Daga yau sai yau,gari na wayewa ke karime ki nunamata komai,daga yau ita nake bukatar ta tsaftace falon nan da dakina,kuma ki tafi da ita kichen ku nuna mata komai,su wanke wanke da yanke yanke,duk ku bata kan ku gama nuna mata kan girkin gidan,Nan gidan ba gidan da zaki zo ki kwanta bane don nima uwarki bata barni na kwanta ba”Ta kareshe cikin Tsawa..

   Jikin Zahirah na rawa ta mike,karime ma ta mike tana fadin”muje ran…”Sauran mganar ta makale ne da suka hada ido da Ummi Sum Sum ta wuce zahirah tabi bayanta kafafunta na hardewa,Ummi tabita wulakantattacen kallon Aranta tana ma Tunanin anya yarinyarnan Lafiyayyane,kuwa domin koda yaushe in tana Tafiya kamar ta lauye ta fadi.

    Suna shiga kichen din Su lami da Uwani dake aiki suna ganin zahirah suka zube suna gaisheta,tare da mata barka da Fitowa,cikin mamaki Zahirah ke kallonsu ganinsu manya dasu ammh suna duka mata,hawayen daya zubomata tasaka gefen hannu ta share lokaci daya tana musu mirmishu,kallon junansu sukayi kafin karime tace”Hajiya tace nazo da ita mu nuna mata komai,gyaran Falon ma tace wai na barmata”hada baki sukayi lokaci daya sukace”Ki barma wa…”Suka fada suna gwalalo ido

  Karime ta kalli Zahirah tace”Eh haka hajiya tace,nifa wlh kaina ya daure,matar yallabai guda ammh Hajiya tana wani abu wanda hankali ya gaza ya dauka”Tafada ckin nuna damuwa,lami tace”Iko sai Allah Ke karime wai kinji da kyau kuwa? tafada tana nuna mamakinta,mirmishi karime tayi kafin tace”Wlh lami nima Abun yabani mamaki,kuma fa hajiyar zaria tafadama cewa yar”uwansa ce fa.

Uwani dake gefe tayi tagumi tace’Oh nifa duk kunsani ackin Rudi,wai ita hajiyan da kanta tace,haka kada fa yallabai yazo ya ganta Muyima kanmu sanadiyar Hanyar cin abincin mu fa'”Karime tace”To ya zamuyi Umarnin hajiya ne fa,ko yallabai bai isa ya tsallake Umarninta ba.

kallonta Sukayi dukkansu tana tsaye tana kallonsu ammh hankalinta bashi agunta ta lula tunanin gida da kewar yan”uwanta,Karime tace”Nifa gaskiya bazan iya sakata wani aiki ba,mu kyaleta dai ta zauna tana kallonmu gudun karta koma ciki hajiya ta ganta ko ya kuka ce'”Uwani batayi mgana ba tajawo wata kujeran Roba ta sakama zahirah tana fadin”Don Allah matar yallabai Zauna kina tsaye Tun dazu”kallonta zahirah tayi kawai sai ta sakarmata mirmishi batace komai ba.

Kallonta karime tayi tace”ki zauna Ranki ya dade…”Girgiza kai tayi kan tace”Ina aikin da zan muku, nafara..”Tafada cikin Nuna Sanyinta kallonta sukayi lokaci daya sukaji kaunarta ta mamayesu atare suka hada baki suka ce’a’a babu wani aiki ranki ya dade ki zauna ki huta abinki”

  Duk da haka taki zama sai da sukayi da gaske kana ta zauna a tsorace tana kallon Kofa,karime ta gyada kai kan tace”Ki zauna da kyau hajiya bata shigowa kichen din nan”Jin haka yasa hankalinta kwanciya,haka ta zauna tana kallonsu suna aiki,suna hiransu wani waje ta murmusa wani waje tadanyi dariya ganin haka yasa suke dan Tsomota cikin hiran nasu,duk bata tsoma musu baki ammh takanyi musu mirmishi basu damu ba,domin Sun Fahimce halitarta ce rashin son mgana,tare da ita suka karishe girkin Tuwon Semo ne sukayi musu da miyar danyen kubewa,sai Farfesun kan sa,da alalan hanta da sukayi ma yallabai,lemon abarba Uwani tahada shima duk na yallabai ne,gudun Fadan hajiya yasa,suka bawa zahirah wasu kololin ta dauko suka zo Dinning suna jerawa Ummi dake zaune Ranta fes Aranta tana fadin”Kadan kika gani yar banza,sai kin barmin gidan dana da kafarki”

  Sai da suka kamallah komai suka goge kichen din Kana suka Nufi dakinsu koda suka Fito falon Ummi ta hau sama,abun mamaki zahirah dakinsu karime ta bisu basu hanata ba,abincima cewa tayi tare dasu zata ci,tuwon sukaci daman shi ne yafi, burgeta taji tana sha”awanci,kafin dare Tuni Zahirah taji ta saba dasu karime saboda yadda suke girmamata gasu babu Ruwansu,duk da,bata mgana sosai ammh sun lura ta saki jikinta dasu,suko fahimtar haka yasa suka kara janta ajiki suna mata hira tana dariya Uwani na bada lbrin Yanmatancinsu akauyensu Haka xahirah ke dariya harda kyakyatawa,suko murna ta cikasu don sosai Yarinyar ke basu Tsausayi mussamman Karime wacce take kallonta kamar yarta Asma”u data haifa da cikinta,Sai da aka kira mangariba,kana suka rakata dakinta,basu wani jima ba suka mata sallama suka fito,sanin Yanzu yallabai zai Shigo.

Aiko Illai bayan mangariban ya shigo da yake yana Tsaya masallaci yin sallah,barayinsa ya zarce direct bayan yayi wanka ya sauya kayan cikin riga da wando na jc,Fitowa yayi ya haura Saman,Ummi domin harga Allah ya ma manta da zahirah ma arayuwarsa balle yayi Tunani Dubata,tare suka sauko Da Ummi sukaci abinci kafin su zauna Afalo suna hira,Issha”i aka kira ya mike ya fice ,yana dawowa sallama yayi Ummi ya wuce sashensa domin yau din nan yagaji matuka shiyasa yana zuwa brush kawai yayi ya kwanta Sai barci.

  Yan Kawo amarya kuwa yakura da Maghana sun iso gida lafiya cikin koshin lafiya,ammh Kuma tun suna hanya Yakura ta roki alfarman Mahgana Ta boyo abunda yafaru Tsakaninsu da Ummi don Allah kada tafada ta tadama Bukar da hankali,suyi shuru da bakinsu sudai nasu addu’ane Allah ya yayyafama abun Ruwan sanyi.

  Mahgana ta ji mganar don da suka koma banda saka albarka basu ce komai ba,sun bada lbrin yahna ta shiga jin dadin rayuwa kam,tagama dacewa duniya sai dai kuma lahira ake mata fata,Jin wannan lbri ya sanyayama Bukar rai,wanda zullumin dake ransa sai da ya ragu,Mahgana kuwa kallonsa take tsausayinshi na ratsa Aranta tace”Bazan ko taba, fadamaka wani hali yahna ke ciiki ba,kodon kaima ka kasance cikin Farinciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button