UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

Afuwan,Afuwan,Afuwan..Kunjini shuru kwana biyu,wlh nayi busy ne sosai Shiyasa kukajini shuru,nagode sosai ga wa”inda suka kirani da wa”inda sukamin mgana ta chart am srry bansamu amsawa ba,ammh nagani kuma nagode sosai,da zarar komai yayi daidai zaku dinga ganin Update akai akai..Tancuu so much Janaf fans For d True luv????

Masu bina pc suna bukatar na sanyasu cikin groups dina am srry duka sun cika,Kuma bani da lokacin bude wani ammh in kuna ra”ayi sai ku bude,bani da mtsala,Nagode sosai da kulawanku akaina janaf tana girmamaku har cikin ranta

NOT EDITED

                   NO 14

  Dafe kuncinsa yayi cikin mamaki yanabin Ummi da kallo,ganin yadda take kallonsa idanunta sun jirkice lokaci daya kamar ba Umminsa ba,baigama mamaki ba yaga Ta nufi zahirah dake yashe akasa hannu dafe da kunci tana tsiyayar hawaye,da kafa ta shureta tana fadin.

   “Don Ubanki me na fada miki..? ko har kin manta kashedi na agareki? d’an Fadi ta haifamin ko Bukar don Uwarki da zaki tasashi kina kallo ko sallama baki ji ba,”Tafada lokaci daya takara kaimata duka,zafin dukan shiyasa Zahirah fashe da kuka tana ja da, baya tana girgiza kai,ammh Ummi Cigaba da binta tayi tana dukanta ko ta ina tana hadawa da Shurunta da kafa kamar wata yar Dambe????
  

     Mu”azzam dake gefe yayi Saurin karisawa ga Ummi yana Fadin”Haba Ummi meyasa kike hakane,baki duba yarinyace dakika ware kina mata wannan Dukan”Yafada yana riko hannunta,Fisgewa tayi tana kallonsa da jajayen idanunta kafin ta rikosa tana fadin”gayamin gaskiya ka kashiga dakinta ne? ko ka kwanta da ita,nace ka kwanta da ita ne..”? Ummi tafada cikin tswa lokaci daya tana jijjiga Mu”azzam,mutuwar Tsaye yayi yana bin Ummi da kallo don wata kwakwalwar tafara gayamasa Ummi tarasa hankalinta.

  Ihun Zahirah shiya Fito da su karime Tundazu,ganin dukan Da Ummi ke mata kuma da Maganganun datake jefama Mu”azzam shiya sasuka ja suka tsaya cike da mamakin Kalaman dake Fitowa daga bakin Ummi,gefe daya kuma ga Tsausayin zahira daya gama cikasu.

  Mu”azzam yadago ya kalli Su karime dasuka Tsura musu ido,lokaci daya yana maida kallonsa kan Ummi,wacce tatsuramai jajayen idanunta,rasa mezai cemata yayi shiyasa ya riko hannuwanta duka lokaci daya ya Rumgumeta yana ma su Karime inkiya da hannu dasu dauke Zahirah dake kwance tana kukan azaba,da hanzari karime da lami,suka kamata tana kuka mai tsuma zuciyar wanda yake Saurare,suka Nufi dakinta da ita,Mu”azzam yabisu da kallo in  ya kalli Fuskar zahirah sai yaji kamar yamata kwallah.

Rumgume yake da Ummi yana bubbuga bayanta yake fadin”Relex Ummi..Cool down don Allah zuciyarki Tayi sanyi bani son ganin wannan colour din naki”Yafada yana kara shafa mata baya,dagowa tayi tana kallonsa kafin tace”Juz ans me ka sadu da yarinyarnan ne? tafada cikin karyewan Murya”Cikin idanunta yakallah yaga yadda Firgici da tsoro suka dabaibayeta,girgiza mata kai yayi yana fadin”A”a Ummi,ni babu hakan har abada Araina,..”Yafada cikin son tabbatarwa “Are u sure..”Tafada tana kara rikesa gyadamata kai yayi yana fadin”Am very Sure Ummi na ki yarda dani…”ajiyar zuciya ta sauke kan tace”Kace wallahi Tallahi toh..”Tafada tana kyabe Fuska,mirmishi yayi yana fadin”Wallahi Tallahi Ummina..Ban saba Umarninki ba,kuma bani fatan na tsinci kaina cikin saba miki har abada..”rumgumesa kawai takarayi tana fadin”Allah yamaka albarka,aduk inda kake ya tsare minkai,yacigaba da Farantamaka kamar yadda kake farantamin”Da Amin yake ta amsawa zuciyar na saukowa da Tsoron data cika  game da Ummi yakara tabbatarma Ransa Ummi ba karamin Tsana tama Ahalin Mahaifinsa ba.


Su karime ko Suna kaita daki suka kwantar da ita bisa gado ta sulale tana kuka mai cin rai,Lami da Uwani suka kalleta cikin Tsausaya sukace”Sannu ranki ya dade,..”Karime ko gefe ta tsaya tama rasa ta cewa,gabadaya kansu yakulle tun da yarinyar tazo gidan nan ko da minti daya Hajiya bata barta ta huta ba,shin mene wai ke faruwa sufa sunshiga  cikin Duhu suna neman mai Fitar dasu haske.

  Suna tare da ita sukaga tafara rawan sanyi hakoranta na hadewa,kaf,kaf,blanket sukadauka suka rufamata suna ta jeramata sannu itako ta kanta take,domin wani zazzabi ne mai zafi ya bugeta hade dawani ciwon kai mai tafiya da barin kai,tanaji kamar andoramata dutsen dala bisa kanta dunkulewa tayi waje daya tana kuka,kuka mai kama da kukan nagaji da wannan Rayuwa,kuka ne na ban tsausayi ga wanda ke sauraranta,hawaye kawai ke ziraromata tagefen kunnenta domin kukan baya bukatar Fidda Amon Sauti.

Ganin haka gabadayansu Tsausayinta yahanasu Fita,kwata,kwata gefe suka samu Suka zauna kowacce ta buga Tagumin Tsausayin yar marainiyar Allah.


Mu’azzam kuwa daganan jan Ummi yayi yakaita dakinta daganshi ya hadamata ruwan wanka yalallabata tashiga tayi wankan ta fito,shi da kanshi yahadamata tea tasha,tana sha kuwa ta hau gado tacemai zata kwanta,don ya batadda Tunaninta sai ya samu gefenta ya kishigida yana tambayanta ya tabaro suhajiya,tana bashi amsa suna hira sama,sama wanda gabadaya hankalisa yanaga zahirah ne ya rasa sukuni wlh ji yake kamar akan kaya yake,cikin ikon Allah sai barcin gajiya ya sace Ummi ta bingire anan,ganin haka yasa Mu’azzam lallabawa ya Fice daga dakinta nata ya doshi na zahirah.

Su karime na zaune ya shigo har bedroom din wanda shine karo na farko daya shigo cikin dakinta tun bayan Tafiyansu yakura,Suna ganinsa suka mimmike Kallonsu yayi kafin yace’Ya jikinta..”? Karime ce ta amsa da cewa”Gata nan dai yallabai inaga masassarace ta kamata tana ta,rawan dari Tun dazu”Shuru yayi hannusa cikin aljuhu yana kallon yadda zahirah ke kara dunkulewa tana rawan sanyi,Numfashi ya Furzar kafin yace”Ok tom nagode kuje sai na nemeku..”Tashi sukayi suna Fadin”Afito lafiya yallabai,Allah kara Afuwa'”lokaci daya suka fice,karisawa yayi gaban gadon na zahirah kan ya saka hannu ya yaye blanket din,Saurin rikewa tayi hakoranta na dakan juna idanunta a lumshe ammh kuma hawaye suna gangarowa ta gefe gefen kumatunta.

  Wani baKon yanayi yaji atare dashi,sakin mata bargon yayi baisan sadda ya yi durkuso gaban gadon ba, yana Fadin”Sannu zahirah..Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawan..”yafada kamar yayi mata kwallah,jin muryansa yasata ta bude idanunta wa’inda suka rine suka koma jawur ta kallesa,shima kuramata ido yayi,yana kallonta,mirmishin karfin hali tamai kafin ta maida idanunta ta kulle,hawaye na cigaba da zirarowa,hannu ya cira ya dora bisa goshinta yaji zafi rau,dafe kai yayi yana fadin”Oh my god..kinji zafin jikinki kuwa? plz stop craying kina kara ma kanki wani zafin ne fa”yafada Wit Serious Tok,shuru tayi batayi mgana ba,kuma bata Bude ido Ba,daya rasa wani Taimako zai bata sai ya zaro wayarsa datake cikin aljihu ya fara laluban Dr.Abduljabar.

Bugu daya ana biyu,ya dauka yana fadin”Ango kasha kamshi,har da mai Abunka..”Yatsina Fuska Mu”azzam yayi yana fadin”Kai kaga wani mai,ni kaga mallam tambayarka zanyi wani irin Treatment din farko zan fara bawa mai fama da matsancin Fever kafin muzo muga likita? yafada muryansa ba wasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button