UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Koda yakoma dakin zahirah baiwar Allah hartayi barci,Assigment din yadauka yayimata awata takarda ya ijiyemata akan side drower dinta,wanda data tashi zata gani,Gyaramata kwanciya yayi bayan ya sumbaceta agoshi ya rufeta da blanket,ya fito zuwa nashi dakin,aransa yana kara mamakin yadda Ummi take mai wasu abubuwan,kamar ba danta ba wacce ta haifa da cikinta ba.
Washegari Tunda Zahirah tatashi taga sakon mu”azzam,akasan aikin dayayimata ya Rubuta SORRY MY HIRAH ALLAH YABAKI HAKURI KINJI salon Rubutun nasa shi ya tsumasata ainun,batasan sadda ta rumgume Takardan ba tana shakan kamshinshi,Aranta tana jin ko me Ummi zatayi sai dai tayi domin takamu da son ya mu”azzam so kuma mai tsanani,wanda tanajin bazata iya rayuwa babu shiba,koda kuwa kasheta za”ayi itakanta da ace zuciyarta tayi shawara da ita,kafin tafara sonshi da bata bari ba,saboda sanin Abunda ke gabanta,ammh sai dai kash,bata da yadda zatayi Allah ya rigaya da yarubuta haka zai faru,yana cikin kundun kaddaranta.
Sauri tayi Ta kwashe a Note Book dinta kafin ta shiga wanka,tana fitowa shiryawa kawai tayi Karime ta kawomata abun karinta agurguje ta karya ta fito rataye da jakanta Ushe na waje na jiranta,tana fitowa suka wuce,Sai da suka dauki Hanya kana Zahirah ke tambayan Ushe yakai yallabai wajen aiki ne? amsa mata yayi da cewa”A’a yau yanajin yallabai bazai Fita umartansa dai yayi daya kaita mkranta akan lokaci”gyada kai kawai tayi Cikin gamsuwa.
Amkranta sunyi kamar yadda suka saba Da Asma”u har aka tashi gida,tare suka fito har bakin get kowacce na tsimarin jiran mai daukanta,shuru shuru babu wanda yazo sai chan sai ga direban Asma”u yazo tafiya da ita,tayi tayi Zahirah tazo sufara kaita gida taki yarda tace tabari itama yanzu za”a zo daukan nata,saboda haka yasa Asma”u taki tafiya ta tsaya jiran Wanda zai dauki Zahirah ammh fiye da minti talatin babu omo babu labari,dole tasa Zahirah bin Asma”u duk da ranta baimata, dadi ba,ammh bataso Asma”u ta zargi wani abu ne,Suna mikawa Asma”u tacema zahirah”Tunda dai yau gaki besty Allah sai kin karisa gida kingaida Mami..”Jin haka yasa Zahirah ta rude taso tayi gaddama Ammh Asma”u ta bata Fuska dole tayarda,ammah akasan Ranta duk zuciyarta babu dadi,ga gabanta dake faduwa.
A asoko road Gidansu Asma”u yake,wanda Sai Da zahirah ta saki baki da hanci tana kallon aljannar duniya domin gidansu mu’azzam ba gida bane,akan tsaruwa da haduwa na gidansu Asma”u,Zahirah bataso zama ba ammh Asma”u ta matsa harsai sukaji abinci sukayi sallah,mami kuwa taji dadin zuwan zahirah ta rumgumota tana sakamata albarka,dazata tafi Mami ta cikamata leda da kayan kwalliya na kamfanin MAKARI harda Atamfanta Super wax,da farko Zahirah kin amsa tayi,Asma”u ce ta amshi kayan tana Hararan zahirah,wacce taketa zubama mami,godiya tana amsawa da Amin.
Tare da Asma”un suka koma zata rakata gida,wanda ko amotan Asma”u keta zencenta ammh ita zuciyanta na gida,illai suna zuwa Suka zuba hon Sani maigadi na wangale get sukafara cin karo da mu”azzam yana kai da kawo hannunsa goye abayansa,yana sanye da riga da wando na kamfanin Armani black and white,jin hon din mota yasa ya zurama get din ido azatonshima Ushe ne,sai yaga wata bakar accord tasawo kai cikin gida Abunda ya dauremai kai ganin zahirah ta fito daga motan ita da wata yarinya,daure fuska yayi yana jifanta dawani kallo wanda sai da zahirah taji kafafunta sun kasa daukanta,lura da yadda zahirah ta rude ne yasa Asma”u ta riko hannunta tana fadin”Shine broda dinki din nan..”?gyada mata kai kawai Zahirah tayi kanta nakasa.
karisawa,sukayi Dan dukawa Asma”u tayi tana fadin”Ina wuni..”Amsawa yayi idonshi na kan zahirah kafin yace”Wacece ke? kuma daga ina kuke..”Yafada cikin bacin rai,Cikin dakiya Asma”u tashiga koramai jawabin abunda yafaru ta kareshe da cewa”Kayi hakuri wlh ba da gangan nadauketa mukaje gidanmu ba,naga ba”azo daukanta bane.”Tafada tana mtse hannun zahirah wacce kanta ke duke taki ko dagowa.
Ajiyar zuciya ya sauke,kafin yace”it ok,ammh karku sake irin wannan,saboda kun tadamana da hankali,tunda ita ba ko”ina tasani ba”Yafada fushinsa na sauka ,Asma”u tace”Insha Allahu bazamu sake ba…”gyada kai yayi kafin yace”Madallah babu komai..”zahirah dai kanta na kasa duk kokarin mu”azzam nasu hada ido bai samu dama ba har suka shige ciki,Zahirah ta godema Allah da bata tarar da Ummi afalo ba,har suka shiga cikin dakinta,Asma”u bata wani zauna ba,illah zahirah tafita takiramata su karime tana nunamusu Asma”unta suka gaisa cikin sakin Fuska,da Asma”u ta tambayeta ina goggonta take,karya Zahirah tayimata da cewa bata nan,Asma”u bata kawo komai ba tace”In takara dawowa sa gaisa da ita..,Bata wani jima ba tayima Zahirah sallama wacce ta rakota har gun mota kafin takoma ciki,bata dai kara saka mu”azzam a ido ba har dare.
Shiko Mu”azzam sam ya manta da zahirah ma saboda ya aiki Ushe kuma bai dawo da wuri ba,sai da lokaci yaja,kana yatuna da ita,koda ushe yaje mkrantan babu kowa,kuma ya tambaya sukace gaskiya basu da masaniya sukam,dole ya dawo yafadama Mu”azzam wanda jin haka yasa hankalinshi yatashi matuka tunaninsa kada yar mutane tazo ta bace ya shiga uku,ina tasani agarin Abuja,Kara tura ushe yayi kan ya dudduba kan hanya ko Tafara takowa akasa,to yatafin ne baidawo ba suka shigo,Ummi kuwa duk wainar da”aka toya tana dakinta bata sani ba,wardrope dinta take gyarawa tun safe shiyasa ba wanda ma yaji Duriyanta ko lunch dinta ma sama,aka hauramata dashi domin yau sarautarta ta motsa ne,Mu”azzam ya godema Allah da haka yafaru,domin bayason Tijaran Ummi sam.
–
Yau kimamin kwana biyun da faruwan Haka,Ammah mu”azzam bai kara waiwayarta ba,taci karo dashi sau biyu tana gaisheshi yana amsawa adakile,kuma fuskarsa,babu Annuri ko kadan,Tuni zahirah tasha jinin jikinta,takuma fahimci Mu”azzam din Fushi yake da ita tun laifin Ranar nan,Tana so tabashi hakuri kuma bata samu dama ba,don akwanakin nan Ummi sai takai goma afalo bata haura ba sama,shiyasa babu halin zuwa bashi hakuri,tunda ba zuwa dakinta yakeyi ba yanzu yana Fushi da ita.
MAFARIN KOMAI
Soyayyah
Ranar jumma”a gidan suka tashi da haihuwar zulaika matar Shureim wacce akama aiki a asibitin Chika dake zaria,ga hajiya jikin sai a hankali,dole Ummi ta shirya Aranar Ushe ya wuce da ita bayan yakai zahirah mkranta,wacce batason wainar da”ake toyawaba sai da tadawo kana su karime ke fadamata,Tsalle tayi itakadai adaki tana murna domin karime tace mata,kila Ummi ma tafi sati don ta debi kaya da yawa,Ran Zahirah fes,Ranar Wuni tayi walwalarta wanda ko malaminta dayazo yaga alama domin Karatun nasu ma na yau na dabam ne,haka take sakin kira”anta cikin Annushuwa,kamar babu abunda ke damunta.
Karfe 8:00pm taji shigowar mota tasan kuma ya Mu”azzam ne,dama already tayi wanka cikin wasu riga da wando wanda cikin siyayyar da yayimata ne,red and black sai ta sanya mayafi R&S karami ta yane kanta dashi bayan tafeshe jikinta da Turare cikin wanda Mami ta bata ne,bayan kuma ta saka humranta wanda Su yakura suka zomata dashi,wani bakin flat shoe ta saka,ta fito tana Baza kamshi,abun mamaki shashen Mu”azzam kai tsaye ta nufa ranta babu ko fargaba.