UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

      Lokacin Da zai Tafi yayi kuka kamar me saboda baison Rabuwa da gida,alokacin yana Dan shekara ashirin da biyu aduniya..Shettima Dana da ashirin da bakwai fadi kuma tanada wajen ashirin da hudu don anyi mata Aure da almajirin Zannah moodu ABUBAKAR BAHGANA Wato Abubakar Babakarami kenan Shima dan asalin maidugurin ne yayi zama gidansu gun zannah Moodu to shi ya bawa Aurenta wajen shekaru biyar kenan ammh ko batan wata bata taba yi ba.


  shekara Biyar Moodu yayi Ya kammalah degree dinsa na farko,saboda hazakarsa dakuma basirarsa yasa jami”ar ta rikesu shida wani KHAMIS khamis yakasance haifafan sudan ne wanda shima karatu yakawoshi har suka hadu Da moodu to ganin yadda yakeda kokari ga fanni karatu shima khamis din badai kwanya ba yasa suka kulla abota tun Moodu bai saki jiki dashi ba hardai yasaki khamis dan manyan mutane don iyayansa suna da hali matuka…Sun amshi tayin mkarantan sunfara koyarwa da taimakon Khamis moodu ya amince saboda yaso komawa gida saboda ko wanda baffansa ke aikowa shekara biyu kenan babu lbarinsa..khamis ya matsamai ya amshi aikin,ganin sunfara koyarwa khamis yakara tursasama,moodu suka dora digirinsu na biyu,suna karatu suna koyarwa ammh duk da haka kewan gida da tunanin halin da ahalinsa ke ciki basu barsa ba,duk kuma albashinsa da Abunda ya samu ba ya iya ci..Yana tarawa ne domin iyayansa da yan”uwansa.

   Sai da sukayi shekaru biyar lokacin sun kammallah masters dinsu akan islamic .Kuma iya Abun duniya sun tarashi alokaci girma tareda hankali mai hade da jin dadi sun bayyana tare dasu.Kana ganinsu kaga wanda kwanciyar hankali da ilimi ya ratsasu lokacin moodu nada shekara talatin da biyu aduniya,hankalinsa yarigaya daya koma gida awannan gaban khamis yaso ya tankwarashi ammh ina moodu ya rigaya da garin ya fitar mai aka kasar haihuwa tayi kira,tuni ya ijiyemusu aikinsu sunyi matukar bakinciki da rashin haziki irin muhammed moodu ammh basu da yarda zasuyi ammh sun fadamai kowani lokaci yaji yana sha”awar dawowa to aikinsa na nan na jiransa..Karon Farko da moodu yayi ma khamis rakiya zuwa sudan wanda duk hutun dayake zuwa ko yamatsamai ya bishi baya zuwa..Ammh ganin zasu rabu shiyasa yabishi don yaga inda yake saboda halin Rayuwa

   Zuwan Moodu Sudan achan yaga tsantsan karramawa na larabawa haka sukaita Rawan jiki dashi kamar dansu khamis sai ga moodu ya shantake fin sati yana sudan yana tareda Khamis yana zagaye gari dashi cikin ziyarce ziyarcensu sune suka ziyarci babban gidan marayu na Kasar Sudan wanda achan ne mafarin komai yafara.

    SUHAIMA takasance Daya daga cikin ya”yan Dake Rayuwa awannan gidan…Suhaima tana yarinyarta macece kyakyawa tanunawa a mujallah..Takasance duk yan matan gidan bamai kyanta Da Natsuwarta marainiyace gabada da baya Tarasa iyayansa ne a wani ambaliyan Ruwa da yafaru akayi awani yanki na kasar Sudan tun Tana yar shekara 9 aduniya iyayanta larabawa ne akasar Sudan tarasasune, tareda dukiyansu dasuka mallaka..Shine dalilin daya saka tataso karkashin kulawan gwannatin kasar.

   Suna zagayen gidan marayun ne idon Moodu yafada kan Suhaima wanda tafito daga bakin compound dinsu tana dube dube kamar tana neman wani Abu dayake ita tana sama ne sukuma suna kasa yadda jikinta yayi mata ya tabbatar mata ana kallonta daga kan dazatayi tacikaro Da Muhammed Moodu bakin Babarbare yakafa mata ido..Lokaci daya zuciyansu ya buga kuma Allah ya sanya musu Son juna…Itace tayi Saurin janye idonta takoma ciki gabanta na tsananta faduwa..Tundaga lokacin Moodu yaji jikinsa ya mutu tun yana daukan Abun wasa har ya fahimci bana wasa bane..Ranar kasa barci yayi ashe khamis na lura dashi shi ya tsaresa kana yake fadamai Abunda ke faruwa ya kara da cewa”Khamis kabar mganar nan saboda wlh yarinyar tafi karfina”Khamis yamasa shuru ashe yasamu iyayansa da mgananan sunaji kuwa sai dai moodu yaga sun daukesa sai gidan marayu su awaje suka tsaya Sauran bayanan Duk iyayan khamis suka gudanar Rasa gane wacce yarinya aciki yasa aka fiddo musu duka yan matan gidan akace Moodu ya Nuna wacce yake so aciki.

Wayyo Dadi moodu yarasa awata Duniya yake alayi na biyu yacikaro Da Suhaima wacce tun zuwanta gun take kallonsa domin ita dakyar barci barawo ya saceta saboda tunani dan barebare sai ga shi sunkuma haduwa..Lokacin dayazo kusa da ita zuciyanta tafara harbawa tadago ta sakarmai ido shima ita yake kallo..Sundade suna kallon juna kafin Moodu ya juya ya Nuna Suhaima..Nan Da nan aka sallami Sauran..Sukuma suka Rankaya wani katon office Abunka ga masu DashI..Domin iyayan khamis wasu agarin.

   Koda aka fadama Suhaima muradin Su moodu batare da dogon Tunani ba ta amince Moodu yabada Tarihin Rayuwarsa kaf dakuma shi Dan asalin ina ne kuma yacike Atakarda cewa zai Tafi Da Suhaima kasarshi Ta haihu..ta amince dama amincewarta ake Nema nan da anan aka gudabar da wasu cike cike mahaifin Khamis Shi yayi ma Moodu walicci kuma ya biyamai Sadaki aka Daura masa Aure Da Suhaima.

   Babu Abunda tadauka illa sallama datayi da yan”uwanta wa”inda suka tashi tare…Gidansu khamis suka Nufa wanda Moodu yarasa bakin dazai mikama iyayan khamis godiya..Suhaima taga gata gun iyayan khamis taji dama sune iyayan Moodu wanda farat daya ya shiga ranta..Sati daya sukayi khamis ya shirya musu zuwa Nageria domin Moodu ya mtsa yana so yakoma gida.

Nageria

Agarin Maiduguri

     Lokacin Da dan Taxi din da suka dauko ya tsaya dasu daidai kofar gidansu Muhammed moodu,wanda dabadon yayi ma gidan mugun sani bazai taba ganesa ba saboda yadda komai ya chanza anguwan ta Famfamari tacika da al”ummah anyi gine gine ainun.

  Kofar gidansu kamar anshare babu kowa jikin moodu yayi sanyi shiyasa yakasa gaba ya kasa baya..Sai Da khamis yadafasa itakuwa Suhaima tana sanye cikin bakar doguwar Riga baka ta yane kanta da gyalensa baki kalle kalle kawai take tazo bakon waje..Cikin sanyi jiki moodu yafara yin gaba lokacin dayake rafka sallama acikin gidan UMMU SALMA CE YAKURA matar Shettima ta amsa sallama tana zaune atsakar gidan tana  wanke wanke.

     Moodu ne agaba sai khamis sai Suhaima dake bayansa basu da wani kaya sai Moodu dake rike da yar jaka..Cikin mamaki yakura take amsa sallamansu tana kallon fuskokinsu lokaci daya ta shaida moodu saboda kammaninsa Da shettima kuma tanajin labarinsa gun Shettima ammh bakin larabawan dake tare dashi ne bata gane ba…Maraba ta hau musu shiko moodu kallonta kawai yake alamun Rashin Sani ganin haka yasa tace mai’Sunana Ummu salma Ni matar dan”uwankane Shettima'”Fadar haka yasa Moodu washe baki ammh kuma abun mamaki babu motsin Innarsa da Baffansa…Suna haka sai ga Shettima yayi sallama cikin gidan lokacin Da Shettima ya kyallah ido yaga dan”uwansa mutuwan tsaye yayi saboda ganin yadda yadawo kamar bashi ba hutu da ilimi sun xauna na mai…Kafeshi da ido Shettima yayi yayinda Moodu yayi saurin isa garesa zai Rumgume ammh Abun mamaki sai shettima yadagamai Hannu alamar kada yakariso hawaye na zubowa bisa idanunsa ya furta”Ashe kana nan Da Ranka da lafiyanka kabarmu cikin zullumi da Tunanin Rashinka”Yafada yana tsiyayan hawaye kafin ya wuce ya shiga aininhin falon mahaifiyarsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Leave a Reply

Back to top button